Buba Galadima: Na Kusa da Kwankwaso Ya Fallasa Makarkashiyar Tinubu kan 'Yan Adawa

Buba Galadima: Na Kusa da Kwankwaso Ya Fallasa Makarkashiyar Tinubu kan 'Yan Adawa

  • Buba Galadima ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu tana da mugun shiri kan jam’iyyun adawa kafin zaben 2027
  • Ya yi gargadin cewa idan gwamnatin ba ta sauya salon mulki ba, za ta fadi kasa warwas a zabe
  • Hakazalika ya bayyana matsalar da 'yan adawa su ke fuskanta fitar da dan takarar da zai fafata da Shugaba Tinubu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Babban jigo a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi zargi kan gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu.

Buba Galadima ya zargi gwamnatin Shugaba Tinubu da rashin shirin kin gudanar da sahihin zabe a 2027.

Buba Galadima ya yi zargi kan gwamnatin Tinubu
Hoton shugaban kasa Bola Tinubu da Buba Galadima Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Buba Galadima
Source: Twitter

Jigon na NNPP ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Prime Time na tashar Arise Tv ranar Litinin, 15 ga watan Satumban 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane zargi Buba Galadima ya yi kan Tinubu?

Kara karanta wannan

Buba Galadima ya yi hasashe mai hadari kan nada sabon shugaban hukumar INEC

Buba Galadima ya yi ikirarin cewa dabarun gwamnati na rusa jam’iyyun adawa na nuni da cewa tana son kawar da kowane irin kalubale a zaben da ke tafe.

“Wannan gwamnati ba ta shirya gudanar da sahihin zabe ba. Salon da su ke dauka na rusa jam’iyyun adawa yana nuna cewa ba sa son kowace jam’iyya ta yi musu adawa a zabe na gaba."
"Ina tabbatar musu da cewa za a samu adawa. Idan ba su canza salon mulki ba, za su fadi a zabe.”

- Buba Galadima

Buba Galadima ya yabawa Rabiu Kwankwaso

Buba Galadima ya bayyana tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin babban jigon siyasa a Najeriya.

"Kwankwaso jagora ne a siyasar Najeriya, domin shi kadai ne, komai ruwa ko rana, idan aka gudanar da sahihin zabe, zai kawo Kano, jiha mafi yawan jama’a a Najeriya."

- Buba Galadima

Matsalar jam'iyyar ADC wajen Buba Galadima

Game da ADC, Buba Galadima ya ce jam’iyyar ta zama tarin ’yan siyasa kawai, amma son zuciya ya hana su hadewa domin fitar da dan takarar da zai kayar da gwamnati.

Kara karanta wannan

Atiku ya sake yi wa gwamnatin Tinubu saukale, ya fadi abin da ta gaza magancewa

“ADC tarin ’yan siyasa ce kawai. Ina so ace mun hada kai gaba daya don kawar da gwamnati, amma saboda son zuciya ba mu yi hakan ba."
"Dukkansu sun san wadanda za a hada don a ci zabe, amma shin mun shirya mu yi hakan?"

- Buba Galadima

Buba Galadima ya yi kalamai kan gwamnatin Tinubu
Hoton babban jigo a NNPP, Buba Galadima Hoto: Buba Galadima
Source: Facebook

Shawarar Buba ga Jonathan da Peter Obi

Buba Galadima ya kuma yi tsokaci kan ganawar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da dan takarar shugaban kasa na LP a 2023, Peter Obi.

Jigon na NNPP ya yi nuni da cewa ya kamata su fitar da dan takara wanda zai fafata da Shugaba Tinubu.

"Ina ganin idan Jonathan da Obi suka hadu suka fitar da mutum daya, za ku ga kasa baki daya za ta amince, domin hakan dabarar siyasa ce da za ta fitar mu daga wannan wahala."

- Buba Galadima

Atiku Abubakar ya soki gwamnatin Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ragargaji gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Atiku ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta kasa magance matsalar yunwa da talauci duk da kwashe fiye da shekara biyu a kan mulki.

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin Atiku ya raba gardama kan shirin ficewa daga PDP zuwa APC

Hakazalika ya bayyana cewa yunwa da talaucin da ake fama da su a kasar nan, ba abin da za a yarda da shi ba ne.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng