"Babu ADC": Jigon PDP Ya Hango Yadda Za Ta Kaya a Zaben 2027
- Jigo a jam'iyyar PDP, Segun Sowunmi, ya yi magana kan zaben shugaban kasa na shekarar 2027
- Tsohon dan takarar gwamnan na jihar Ogun ya bayyana cewa jam'iyyar ADC ba za ta kai labari ba a zaben
- Ya nuna cewa zaben zai kasance ne a tsakanin jam'iyyar APC mai mulki da babbar mai adawa a Najeriya watau PDP
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Babban kusa a jam'iyyar PDP, Segun Sowunmi, ya tabo batun zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Segun Sowunmi ya ce zaɓen shugaban kasa na shekarar 2027 zai kasance ne kawai tsakanin jam’iyyar APC mai mulki da PDP.

Source: Twitter
Jigon na PDP ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin 'Sunrise Daily' na tashar Channels TV a ranar Litinin, 15 ga watan Satumban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jigon PDP ya yi wa ADC shagube
Segun Sowunmi ya ce jam’iyyar ADC ba ta da karfin da zai ba ta damar yin katabus a zaben.
"Zaɓen shugaban kasa na 2027 zai kasance ne tsakanin APC mai mulki da PDP."
“Wannan haɗakar da ku ke gani suna ta faman yawo da ita mai suna ADC? To suna da ‘yancin yin hayaniya, amma idan ka kalli zabubbukan baya-bayan nan da aka yi, ba su cimma wani abu mai muhimmanci ba.”
- Segun Sowunmi
Sowunmi ya magantu kan karfin PDP
Tsohon dan takarar gwamnan ya kara da cewa har yanzu jam’iyyar PDP tana da karfi a wajen al’umma duk da ficewar wasu manyan mambobi.
“Mun ga mutane ɗaya ko biyu ko uku da PDP ta gina su, amma yanzu suna tunanin za su iya yin siyasa da kansu."
“Abin da nake gani zai fi zama kalubale ga ADC shi ne yadda za su zaɓi ɗan takara a tsakanin mutane masu son kai fiye da kima, waɗanda ke ganin komai dole sai yadda suke so.”

Kara karanta wannan
'Yan hadaka na shirin sauya jam'iyya daga ADC zuwa ADA,? An ji yadda lamarin yake
- Segun Sowunmi
Segun Sowunmi ya ce banda APC da PDP, sauran jam’iyyu ba su da tsarin dimokuraɗiyya na cikin gida.
"Akalla a wurinmu, kana jin muhawara kan NEC, kan shugabanni da dai sauransu."
- Segun Sowunmi
Jam'iyyar PDP ta fi karfin raini
Ya kuma bayyana PDP a matsayin jami'ar gudanar da dimokuradiyya a Najeriya.

Source: Facebook
“Kar a taɓa raina PDP. Ta yaya za a raina jam’iyyar da ta kasance tun daga 1998, ba ta taɓa canza suna ba, ba ta taɓa canza tambari ba, kowa ya san taken ta, kuma har yanzu tana da ƙarfi?”
"Idan kuka sake ba mu kuri’a, za mu ba ku rayuwa mai yalwa kamar yadda muka saba. Idan kuka zabi akasin haka, to za ku rayu da sakamakon wannan zaɓi.”
- Segun Sowunmi
Segun Sowunmi ya ce PDP ta tsira daga rikice-rikice daban-daban ne saboda jajircewarta da juriyarta.
Sowunmi ya magantu kan ficewa PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan takarar gwamnan jihar Ogun a karkashin inuwar PDP, Segun Sowunmi, ya yi magana kan ficewa daga jam'iyyar.
Segun Sowunmi ya bayyana cewa zai ci gaba da zama a PDP wadda ya kasance cikinta tun shekarar 1998.
Jigon na PDP ya bayyana cewa ganawar da ya yi da Shugaba Bola Tinubu, ba ta nufin cewa zai koma jam'iyyar APC.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

