Tsohon Hadimin Atiku Ya Raba Gardama kan Shirin Ficewa daga PDP zuwa APC

Tsohon Hadimin Atiku Ya Raba Gardama kan Shirin Ficewa daga PDP zuwa APC

  • Tsohon mai magana da yawun Atiku Abubakar ya tabo batun sauya sheka da aka ce ya yi daga jam'iyyar PDP zuwa APC
  • Segun Sowunmi ya bayyana cewa bai kamata a yi tunanin cewa saboda sun gana da Shugaba Bola Tinubu, zai bar jam'iyyar PDP ba
  • Ya nuna cewa 'yan Najeriya na da abin dariya kan yadda su ke fassara wasu abubuwan da ke faruwa a fagen siyasa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja – Tsohon mai magana da yawun tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, Segun Sowunmi, ya yi magana kan batun ficewa daga PDP.

Segun Sowunmi ya karyata rade-radin cewa yana shirin sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Segun Sowunmi ya ce yana nan a PDP
Hoton tsohon dan takarar gwamnan PDP a Ogun, Segun Sowunmi Hoto: @SegunSowunmi
Source: Facebook

Segun Sowunmi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin 'Sunrise Daily' na tashar Channels Tv a ranar Litinin, 15 ga watan Satumban 2025.

Kara karanta wannan

An samu bayanai daga majiyar Aso Rock kan takarar Tinubu da Shettima a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Sowunmi ya ce kan barin PDP?

Tsohon hadimin na Atiku ya ce ya ce duk da ganawar da ya yi da Shugaba Bola Tinubu a gidansa da ke Legas ranar 8 ga watan Yunin 2023, bai da nufin barin jam'iyyar PDP.

"Da ina son na sauya sheka zuwa APC, da tuni na yi hakan, amma ba yanzu ba. Har yanzu ni ɗan jam'iyyar PDP ne."

- Segun Sowunmi

Sowunmi ya ce gaisuwarsa da Shugaba Tinubu, wanda su ka san juna stun shekarar 1994, ta jawo fahimtar kuskure daga wasu ’yan Najeriya.

"Abin akwai daure kai saboda bayan wannan gaisuwar da shugaban kasa, mutane da dama sun yi tunanin na sauya jam'iyya. 'Yan Najeriya nada abin ban dariya. Na kasance a wannan jam'iyyar tun 1998."
"Gaisuwa daya ce, ziyara daya kawai ga shugaban kasan da na sani tun shekaru masu yawa a baya, sannan ake tunanin zan bar jam'iyya ta? A'a ko kadan ba haka ake yi ba."

Kara karanta wannan

APC ta kama tsohon gwamna dumu dumu kan zargin taimakon PDP, ta faɗi dalilai

- Segun Sowunmi

Me Sowunmi ya tattauna da Tinubu?

Segun Sowunmi, wanda ya tsaya takarar gwamna a zaben fitar da gwani na PDP a jihar Ogun a 2023, ya bayyana cewa tattaunawarsa da Tinubu ta mayar da hankali ne kan manyan batutuwa.

“Ina da damuwa kan lamarin Rivers, shugaban kasa ya yi min bayani wanda ya yi ma’ana. Haka nan na nuna damuwa kan tsaro a Arewa. Na ce na fahimci inda yake son zuwa kan manufofinsa, amma tasirin da su ke da shi kan talakawa ya dame ni."

- Segun Sowunmi

Segun Sowunmi ya ce zai ci gaba da zama a PDP
Hoton Segun Sowunmi tare da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: @SegunShowunmi
Source: Facebook

Ya kara da cewa bayan kusan shekaru 30 na tafiyar dimokuradiyya a Najeriya, lokaci ya yi da za a mayar da hankali kan hadin kai da ci gaban kasa fiye da rikicin jam’iyya.

Sowunmi ya ba jam'iyyar PDP shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban kusa a jam'iyyar PDP, Segun Sowunmi, ya bada shawara kan tunkarar zaben shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Rigima ta barke tsakanin Ministan Tinubu da gwamna a APC? An samu bayanai

Segun Sowunmi ya bayyana cewa lokaci ya yi da ya kamata jam'iyyar PDP ta duba yiwuwar dawo da tsohon dan takarar shugaban kasa na LP a zaben 2023, Peter Obi, zuwa cikinta.

Jigon na PDP ya bayyana cewa dole jam'iyyar ta koma ga Peter Obi, duba da irin tarin magoya baya, musamman matasa da yake samu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng