Maganar Kifar da Tinubu a 2027 Ta Dagawa APC Hankali, Ta Yi Martani ga ADC

Maganar Kifar da Tinubu a 2027 Ta Dagawa APC Hankali, Ta Yi Martani ga ADC

  • Jam’iyyar APC ta ce ikirarin sakataren ADC na cewa za su kwace mulkin Najeriya da Legas a 2027 magana ce maras tushe
  • Kakakin APC, Seye Oladejo ya zargi Rauf Aregbesola da cin moriyar APC kafin ya juya wa jam’iyyar baya a halin yanzu
  • A martanin da ta yi, APC ta ce ba da maganganu kawai ake zaɓe ba, aiki da cancanta ne ke jawo amincewar jama’ar kasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas - Jam’iyyar APC reshen jihar Legas ta mayar da martani mai zafi kan tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola.

Rahotanni sun nuna cewa ya Aregbesola ya bayyana cewa jam’iyyar sa ta yanzu, wato ADC, za ta karɓi mulki daga hannun APC a 2027.

Rauf Aregbesola tare da shugaba Bola Tinubu
Rauf Aregbesola tare da shugaba Bola Tinubu. Hoto: @raufaregbesola|@aonanuga1956
Source: Twitter

Legit Hausa ta tattaro martanin da APC ta yi ne a cikin wani sako da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a X.

Kara karanta wannan

APC ta kama tsohon gwamna dumu dumu kan zargin taimakon PDP, ta faɗi dalilai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai magana da yawun jam’iyyar APC a Legas, Seye Oladejo ya bayyana furucin Aregbesola a matsayin maras tushe da kuma yunƙurin neman suna bayan barin APC.

Maganar da Aregbesola ya fada kan APC

Aregbesola da ya rike mukamai daban-daban a karkashin APC tun daga kwamishina a Legas (lokacin jam'iyyar AD), gwamnan Osun (jam'iyyar AC), har zuwa ministan cikin gida, ya ce ADC na da shirin kafa gwamnati a 2027.

Tsohon gwamnan ya yi bayanin ne yayin da ya kaddamar da wani shirin ƙarfafa goyon bayan jama’a da ADC ta shirya domin tunkarar zaɓen 2027.

A cewarsa, ADC za ta iya ɗaukaka ta hanyar haɗin kai da kuma wayar da kan jama’a a matakin ƙasa da jihohi.

Ya kara da cewa jam’iyyar na da niyyar kafa gwamnati a Abuja da kuma Legas, lamarin da ya fusata APC mai-ci.

Sakataren ADC a wani taron 'yan adawa a kwanakin baya
Sakataren ADC a wani taron 'yan adawa a kwanakin baya. Hoto: Rauf Aregbesola
Source: Facebook

Martanin APC kan ikirarin Aregbe

Oladejo ya ce Aregbesola ya gama rayuwarsa ta siyasa gaba ɗaya a APC, daga matakin jiha zuwa na tarayya, amma yanzu yana ƙoƙarin rusa gidan da ya gina shi.

Kara karanta wannan

Gbenga Daniel: Yadda Sanata ya ci dunduniyar APC a zaben cike gurbi

Ya bayyana wannan hali a matsayin illa ga kansa, inda ya yi ikirarin cewa sukar APC daga bakin Aregbesola ba wai yana cutar da jam’iyyar ba ne, illa dai rage kimar shi a idon jama’a.

Punch ta wallafa cewa ya ce:

“Duk wata suka da Aregbesola ya yi kan APC tamkar ya share tarihin aikinsa ne da hannunsa.”

APC: 'ADC ba ta da tasiri a kasa'

APC ta bayyana ADC a matsayin jam’iyya mara karfi, tana nuna gazawarta a zaben kananan hukumomi da na baya-bayan nan a matsayin hujja.

Oladejo ya ce bai kamata jama’a su ɗauki ikirarin ADC da muhimmanci ba, domin jam’iyyar ba ta da sahihan ayyukan da za su ja hankalin masu zaɓe.

Ya yi hasashen cewa ko da Aregbesola ya kasance a gaba gaba wajen yaki da APC, ADC za ta sha kashi a zaɓen 2027.

APC: An yi wa Tinubu da Barau addu'a

A wani rahoton, kun ji cewa wasu malaman addini a jihar Kano sun yi taron addu'a ga shugaban kasa Bola Tinubu da Sanata Barau Jibrin.

An gudanar da addu'o'in ne domin neman cigaba da samun nasara da karfi ga jam'iyyar APC da shugabanninta a Najeriya.

Kara karanta wannan

'Za mu fitar da Tinubu daga Aso Rock Villa,' Aregbesola ya fadi shirin ADC a 2027

Hakan na zuwa ne yayin da APC da jam'iyyun adawa suka fara maganganu kan makomar siyasar Najeriya a zaben 2027 mai zuwa a gaba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng