Fara Kamfen da Wuri Zai Jawowa Tinubu Tasgaro, Zai Iya Fuskantar Matsala kan Zaɓe

Fara Kamfen da Wuri Zai Jawowa Tinubu Tasgaro, Zai Iya Fuskantar Matsala kan Zaɓe

  • Tsohon dan majalisa Dachung Bagos ya bukaci hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta hukunta Bola Tinubu a Najeriya
  • Bagos ya bukaci hakan ne daga hukumar INEC saboda fara tallan Tinubu da aka fara yi tun kafin zaben 2027 ya karato
  • Bagos ya ce Sashe na 94 na Dokar Zabe 2022 ya haramta haka kafin kwanaki 150 da zaben, yana bukatar INEC ta yi adalci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jos, Plateau - Tsohon dan majalisa na tarayya, Dachung Bagos, ya kalubalanci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) kan fara kamfe da wuri.

'Dan majalisar ya bukaci hukumar INEC ta hukunta shugaban kasa, Bola Tinubu game da fara tallata shi da ake yi.

An taso a gaba kan fara kamfe da wuri
Shugaban kasa, Bola Tinubu yayin taro a Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

An bukaci INEC ta hukunta Bola Tinubu

Bagos, wanda ya wakilci mazabar Jos Kudu/Jos Gabas ta Jihar Plateau, ya yi wannan magana ne a ranar Alhamis lokacin da yake magana a shirin AIT Focus.

Kara karanta wannan

Tsohon soja zai bada wuri, Simi Fubara zai koma kujerar gwamnan Rivers

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bukaci INEC ta nuna cikakken ikon ta, ta hukunta Shugaba Bola Tinubu da magoya bayansa kan tallan kamfen da ke dauke da rubutun “Vote Tinubu 2027”.

Tsohon dan majalisar ya bayyana cewa hakan saba ka'ida ne watanni kafin lokacin da doka ta amince da shi.

Me doka ta ce kan fara kamfe da wuri

'Dan majalisar ya yi nuni da cewa Sashe na 94 na Dokar Zabe ta 2022 ya haramta duk wani kamfe da ke neman kuri’a a fili kafin lokacin.

Sashe na 94 na Dokar Zabe ta 2022 ya bayyana cewa kamfe zai fara ne kwanaki 150 kafin ranar zabe, amma yakin neman zabe ya fara tun bayan kammala zaben 2023.

Bagos ya bayyana matsayin dokar da cewa ba ta hana taro ko shawarwari ba, amma abin da take hana shi ne duk wani tallan da aka rubuta “vote for.”

Ya ce:

“Doka ta haramta amfani da kalmar ‘vote for.’ Don haka duk wata magana da ta kunshi wannan a tallan da aka fara shi ne abin da doka ta hana.

Kara karanta wannan

Rigimar ADC ta ki karewa, 'dan takarar shugaban kasa ya ce za a wargaza lissafin 'yan hadaka

“Shi ya sa a Abuja yau wasu suka sa hoton shugaban kasa da mataimakinsa da rubutu 2027 kawai, sai mutum ya yi masa fassara.”
An taso INEC a gaba kan fara tallaen Tinubu da wuri
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmud Yakubu a Abuja. Hoto: INEC Nigeria.
Source: Twitter

Yadda tallar Tinubu ta jawo maganganu

A yayin taron, an nuna tallar kamfen da ke dauke da rubutun “Vote Tinubu 2027” tare da hoton shugaban kasa da matarsa, abin da ya jawo cece-kuce.

Bagos ya ce:

“Da zarar aka saka kalmar ‘vote,’ wannan ya sabawa doka, musamman Sashe na 94. INEC ya kamata ta hukunta duk wanda ya yi haka.
“Idan shugaban kasa ne, kuma babu tambarin jam’iyyar, amma kalmar ‘vote’ ta bayyana, INEC ya kamata ta hukunta shugaban kasa.”

Ya bukaci INEC ta rubuta wasika kai tsaye ga shugaban kasa, ta nuna cewa suna da ikon kansu, inda ya ce a tuntubi INEC ta fara da wannan mataki.

'Dan APC ya shawarci Tinubu kan kamfe da wuri

Kun ji cewa jagora a APC, Charles Udeogaranya ya bukaci Bola Tinubu ya dakatar da kamfen 2027 domin mai da hankali kan cika alkawuran mulki.

Ya bayyana haka ne a lokacin da INEC ta gargadi ‘yan siyasa su guji fara kamfen da wuri domin hukumar ba ta fitar da jadawalin zaɓe ba.

Kara karanta wannan

NNPCL: Mele Kyari ya yi magana bayan EFCC ta masa tambayoyi kan almundahana

Udeogaranya ya ce kamfen da wuri yana hana nagartaccen shugabanci kuma yana haddasa zafin siyasa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.