Rigima Ta Barke tsakanin Ministan Tinubu da Gwamna a APC? An Samu Bayanai
- Wasu rahotanni da ake yadawa sun yi ikirarin cewa rikici ya shiga tsakanin Ministan harkokin cikin gida da Gwamnan jihar Ondo
- Dr. Olubunmi Tunji-Ojo ya musanta wadannan rahotanni, yana mai bayyana su da shaci-fadin da aka saba a kafafen sada zumunta
- Ya bayyana cewa a yanzu ya maida hankali wajen tallafa wa duk wani yunkuri da zai kara nuna wa yan Najeriya alherin Shugaba Bola Tinubu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ondo -Ministan Harkokin Cikin Gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ya karyata rahotannin da ke cewa akwai sabani tsakaninsa da gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa
Ministan ya bayyana irin wannan jita-jita a matsayin “maganganun shafukan sada zumunta marasa tushe da hujja.”

Source: Facebook
Tunji-Ojo ya yi wannan jawabi ne a ranar Alhamis a Ikare-Akoko yayin wani shirin kiwon lafiya kyauta da ƙungiyar Grassroots Movement for Tinubu (GMT) ta shirya a mazabar Ondo ta Arewa, Tribune Nigeria ta rahoto.
Minista ya samu sabani da gwamnan Ondo?
Ministan, wanda tsohon hadimin Gwamna Aiyedatiwa, Hon. Bode Obanla, ya wakilta, ya ce babban abin da ya fi mayar da hankali a kai shi ne tallafa wa shirye-shiryen da za su ƙara nuna nasarorin Shugaba Bola Tinubu.
Ya ce:
"Aikina shi ne na tallafa wa kowace ƙungiya da ke kokarin yada ayyukan alherin Shugaba Tinubu.
Babu wani rikici ko sabani tsakanina da gwamna. Abin da ya fi muhimmanci shi ne mu haɗa kai mu bayyana nasarorin Asiwaju.”
Ministan Tinubu ya yabawa kungiyar GMT
Tunji-Ojo ya bayyana cewa GMT ƙungiya ce mai girma a faɗin ƙasar nan wadda ta shahara wajen shirye-shirye, musamman a fannoni na kiwon lafiya da tallafa wa al’umma.
Ya kara da cewa zai ci gaba da ba da goyon baya ga irin wannan ƙoƙari domin isar da saƙon Shugaba Tinubu ga jama’a, in ji Punch.

Kara karanta wannan
'Talauci ya yi muni a Najeriya,' El Rufa'i ya ce akwai mafita kan matsin tattalin arziki
A nasa jawabin, shugaban GMT, Hon. Saka Yusuf-Ogunleye, ya ce za su tallafawa mutane akalla 1,000 a kowace mazabar sanata karkashin shirin kiwon lafiya kyauta.
Ya ce sun dauki wannan aikin a matsayin wata hanya ta tallafa wa manufofin Shugaba Tinubu.

Source: Facebook
GMT ta kudiri aniyar tallata nasarorin Tinubu
Haka kuma, Shugabar Mata ta GMT, Mrs. Olamide Falana, ta sake jaddada aniyar ƙungiyar na nuna irin nasarorin da shugaban ƙasa ya samu.
Ɗaya daga cikin masu cin gajiyar shirin, Mista Sodiq Issau-Sanni, wanda ma’aikaci ne, ya yaba da ƙoƙarin kungiyar GMT.
Ya bayyana shirin a matsayin wanda ya zo a kan gaba kuma mai tasiri wajen kawo kiwon lafiya kusa da jama’a, musamman mazauna yankunan karkara.
An fara tallata Tinubu gida-gida a Ondo
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar AMG ta kaddamar da shirin tallata shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu gida-gida a fadin jihar Ondo.
Kungiyar AMG ta kudiri aniyar tallata Tinubu ne bisa goyon bayan da take samu daga Ministan Harkokin Cikin Gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo.
A cewar kungiyar, za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin Tinubu ya yi tazarce a kan mulkin Najeriya domin ya ci gaba da ayyukan alherin da ya fara.
Asali: Legit.ng
