2027: Lamura Sun Fara Juyawa, Kwankwaso Ya 'Gana' da Jonathan, an Tattauna Batutuwa
- Siyasar Najeriya musamman kan zaben 2027 ta sake ɗaukar sabon salo duba da yadda ake ta neman gina haɗaka domin nasara
- Wasu majiyoyi suka ce Goodluck Jonathan da magoya bayansa na kokarin jawo Sanata Rabiu Kwankwaso domin tafiya tare
- Hakan bai rasa nasaba da karfinsa a Kano domin hada kai da shi a zaben 2027 mai zuwa domin a iya kwace mulki daga Bola Tinubu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Lamuran siyasar zaben 2027 na sake sauya salo domin tabbatar da kwace madafun iko daga hannun yan APC.
An ce bangaren Goodluck Jonathan na kokarin jawo Sanata Rabiu Kwankwaso domin hada kai.

Source: Facebook
Ana rade-radin Kwankwaso ya gana da Jonathan
Rahoton Vanguard ya ce hadakar idan ta yiwu, za ta yi tasiri duba da nasarar Kwankwaso a Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata majiya kusa da Jonathan ta tabbatar da cewa tuni tawagar Kwankwaso ta gana da nasu domin samun mafita.
An ce kowane bangare ya gabatar da bukatunsa na farko domin cimma matsaya kan burin da ake da shi na siyasa.
Majiyar ta ce bangaren Rabiu Kwankwaso na bukatar kujerar mataimakin shugaban kasa, sai dai Jonathan da tawagarsa ba su yanke shawara kan bukatar ba tukuna.

Source: Facebook
Babbar matsalar Jonathan game da takara
Wani babban jami’i ya bayyana cewa bangaren Jonathan na iya duba wani bangaren, kamar daukar matashin dan siyasa daga Arewa, musamman gwamna mai ci, don jawo matasa.
Sai dai babbar matsalar Jonathan a yanzu, kamar yadda aka gano, ita ce rashin tabbas kan wace jam’iyya zai yi amfani da ita.
An gano cewa ko da PDP da ADC suna iya ba shi dama, rikicin rarrabuwar kawuna a jam’iyyu biyu na iya zama cikas.
Rudanin da ke tattare da takarar Jonathan
Duk da haka, wani daga bangaren Jonathan na ganin akwai rudani game da takararsa a PDP da kuma ADC a zaben da ke tafe nan gaba.
Majiyar ta ce:
“Jonathan yana cikin rudani kan damar sa a PDP da ADC saboda wasu daga cikin abokan hamayyarsa har yanzu suna da ikon sarrafa ɓangarorin biyu.
"Hakan ya sa lamarin ya ɗan zama mai wuya gare shi ya zaɓi ɗaya daga cikinsu a matsayin dandali na tsayawa takara a 2027.
“Gaskiya ne cewa a yanzu, ADC ta ƙunshi mafi yawancin ‘yan Jonathan waɗanda suke shirye su ba shi dandalin tsayawa takara, amma matsalar ita ce Atiku ma yana neman wannan dandali, ko da yake ba shi da ƙarfi a jam’iyyar kamar Jonathan.”
Da alamu Jonathan zai bijirewa matarsa kan takara
A baya, mun ba ku labarin cewa komai na iya faruwa game da takarar tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan a zaben shekarar 2027.
Majiyoyi sun ce Jonathan ya dage kan tsayawa takarar shugabancin kasa a 2027 duk da rashin goyon bayan matarsa Patience Jonathan a lokuta da dama.
An gano cewa magoya bayan tsohon shugaban na gudanar da taruka a kasashen waje domin karfafa tushensa a PDP da neman hadin kai kan zaben.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


