Hukumar INEC Ta Raba Gardama, Ta Saki Sunayen Shugabannin Jam'iyyar Hadaka, ADC

Hukumar INEC Ta Raba Gardama, Ta Saki Sunayen Shugabannin Jam'iyyar Hadaka, ADC

  • Hukumar INEC ta amince da shugabannin rikon kwarya na jam'iyyar ADC karkashin jagorancin Sanata David Mark
  • Hakan na zuwa bayan watanni da hadakar yan adawa ta rungumi ADC a matsayin jam'iyyar da za ta tunkari babban zaben 2027
  • INEC ta saki sunayen wasu daga cikin mambobin kwamitin gudanarwa na ADC ta kasa (NWC) da ta amince da su

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Bayan tsawon watanni, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC ta amince da sabon shugabancin jam'iyyar hadaka ta ADC karkashin David Mark.

Hukumar INEC ta amince da canjin shugabancin da aka samu a ADC bayan tawagar hadakar yan adawa ta hade da jam'iyyar domin tunkarar zaben 2027.

David Mark da Rauf.
Hoton tsohon shugaban Majalisar Dattawa, David Mark da tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola Hoto: @Davidmark
Source: Twitter

Hakan dai na kunshe a wani gyara da INEC ta yi a shafinta na yanar gizo dangane da shugabannin jam'iyyar ADC, wanda Legit ta gano ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Mele Kyari: Tsohon shugaban NNPCL ya fada komar EFCC, an ji dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

INEC ta amince da sabon shugabancin ADC

A sauye-sauyen da hukumar INEC din ta yi, an ga tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Mark a matsayin shugaban jam'iyyar ADC na kasa.

Haka zalika, INEC ta amince da tsohon Ministan harkokin cikin gida kuma tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola a matsayin sakataren ADC na kasa.

Idan ba ku manta ba an nada David Mark da Rauf Aregbesola a matsayin shugaban ADC da sakatare na rikon kwarya bayan hadakar adawa ta rungumi jam'iyyar.

Yadda manyan 'yan adawa suka shiga ADC

Jagororin adawa sun amince su dunkule wuri daya karkashin inuwar jam'iyyar ADC domin kalubalantar shugaban kasa, Bola Tinubu da APC a zaben 2027.

Manyan jagororin hadaka sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.

Tun bayan kulla wannan hadaka, aka fara rikici kan shugabancin ADC, lamarin da ya fara tada hankalin wasu daga cikin magoya bayan jam'iyyar.

Kara karanta wannan

'Sun fara kamfe a sakaye,' INEC ta fadi yadda 'yan siyasa su ke birkita mata lissafin 2027

Amma mai magana da yawunta, Mallam Bolaji Abdullahi, ya kwantar da hankulan yan Najeriya a lokuta da dama da cewa babu abin damuwa,

A makon da ya gabata, wasu mambobin kwamitin gudanarwa (NWC) na ADC sun ziyarci hukumar INEC kan wannan batu, in ji rahoton Daily Trust.

Hadakar yan adawa a ADC.
Hoton manyan jagororin adawa a Najeriya a wurin taron amince wa da ADC a Abuja Hoto: @atiku
Source: Twitter

Sunayen shugabannin ADC da INEC ta saki

Sai dai INEC ta amince da sabon shugabancin ADC karkashin jagorancin David Mark, inda ta wallafa sunayen wasu daga cikin shugahannin jam'iyyar a shafinta.

A cewar hukumar INEC, sabon kwamitin gudanarwa (NWC) na ADC ya haɗa da:

1. Sanata David Mark – Shugaban jam’iyyar ADC na kasa.

2. Ogbeni Rauf Aregbesola – Sakataren jam'iyya na kasa.

3. Dr Mani Ibrahim Ahmad – Ma’ajin ADC na kasa

5. Akibu Dalhatu – Sakataren harkokin kudi na ADC ta kasa.

6. Farfesa Oserheimen Aigberaodion Osunbor – Mai ba da shawara kan harkokin shari’a na jam’iyya.

ADC ta zargi APC da yiwa 'ya'yanta barazana

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta yi ikirarin cewa karbuwar da take yi a wurin yan Najeriya ya fara firgita jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

2027: Yadda Jonathan ya nuna layinsa kan takara duk da rashin goyon bayan matarsa

Bisa haka ADC ta zargi APC ta yiwa 'ya'yanta barazana saboda tana tsoron cewa yan Najeriya na iya juya mata baya.

Zargin na jam'iyyar ADC ya biyo bayan rikice-rikice da dama da suka faru a tarurrukanta, musamman a jihohin Kaduna da Legas.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262