'Sun Fara Kamfe a Sakaye,' INEC Ta Fadi Yadda 'Yan Siyasa Su ke Birkita Mata Lissafin 2027
- Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC ta bayyana damuwa a kan yadda 'yan siyasa su ka fara jirkita mata lissafin zaben 2027
- Kwamishinan INEC na kasa kuma Shugaban Hukumar TEI, Farfesa Abdullahi Zuru ne ya bayyana haka a wani taro da aka gudanar a Abuja
- Farfesa Abdullahi Zuru ya kara da cewa yanzu haka, wasu daga cikin 'yan siyasa a Najeriya sun fara kamfe a cikin dabara kafin lokaci ya yi
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta nuna damuwa matuka kan yadda 'yan siyasa da magoya bayansu ke kara tsunduma cikin kamfen tun yanzu.
INEC ta bayyana cewa wannan abu da 'yan siyasa ke yi ya saba da dokokin zaben Najeriya kamar yadda aka gindaya a hukumance.

Source: Twitter
Vanguard News ta wallafa cewa wannan bayani ya fito ne daga bakin Kwamishinan INEC na kasa kuma Shugaban Hukumar TEI, Farfesa Abdullahi Zuru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan siyasa suna fusata hukumar INEC
Jaridar Punch ta ruwaito cewa ayayin tattaunawa da masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ranar Laraba a birnin tarayya Abuja, INEC ta ce ba ta jin dadin yadda 'yan siyasa ke take dokar zabe.
Taron ya maida hankali ne kan “Kalubalen Kamfen da Wuri a Siyasar Najeriya” yayin da ake zargin tuni aka fara yakin neman zabe, amma da dabaru.

Source: Twitter
Farfesa Zuru ya bayyana cewa, yanzu haka ‘yan siyasa da jam’iyyun su sun fara amfani da dabaru wajen gudanar da kamfen tun kafin lokacin da doka ta amince ya yi.
Ya ce an fara ganin kamfen ta hanyar rubuce-rubuce a allunan talla, kafofin sada zumunta, da kuma taruka da ake yi a bainar jama'a – duk da sunan “godiyar goyon baya” ko “aikin alheri”.
Ya ce:
“Wannan dabi’a ce da ke ci gaba da yaduwa kuma tana barazana ga sahihancin tsarin zabe da dimokuradiyya."
INEC ta ce wadannan ayyuka na ‘yan siyasa na iya shafar zaman lafiya da adalci a lokacin zabe, tare da haddasa rudani a zukatan al’umma.
INEC ta yi kira ga jam'iyyu siyasa
Farfesa Zuru ya bukaci jam’iyyun siyasa da ‘yan takara su mutunta tsarin doka da ka’idojin da aka shimfida domin kare ingancin tsarin dimokuradiyya a Najeriya.
Ya kara da cewa akwai bukatar hadin gwiwa tsakanin gwamnati, kafafen yada labarai, kungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki wajen hana ci gaba da irin wannan halayya.
Wannan ba shi ne karon farko da hukumar INEC ke koka wa da yadda ta ce wasu daga cikin 'yan siyaar Najeriya sun fara kokarin kamfen a taruka da maganganunsu ba.
INEC: Jihohin Kudu sun yi zarrar yin rajista
A baya, mun wallafa cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) ta bayyana jihohin Najeriya da suka fi yawan mutane masu karbar katin zabe bayan zaben da ya gabata na 2023.

Kara karanta wannan
'Talauci ya yi muni a Najeriya,' El Rufa'i ya ce akwai mafita kan matsin tattalin arziki
Lagos ta fi kowace jiha yawan masu karbar PVC, inda mutane kusan miliyan 6.21 suka karbi nasu katin zaben, Kano ta zo na biyu da mutum kusan miliyan 5.59 da su ka karbi katinsu.
Baya ga haka, akwai sauran jihohin da suka samu karbar katin zabensu kamar Katsina (miliyan 3.46), Ribas (miliyan 3.29), Delta (miliyan 2.99), Oyo (miliyan 2.76) da sauransu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

