Ministan Abuja, Wike Ya Yi Martani ga Tambuwal kan Zargin Cin Amana

Ministan Abuja, Wike Ya Yi Martani ga Tambuwal kan Zargin Cin Amana

  • Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa ya saurari kalaman tsohon gwamnan Sakkwato, Aminu Tambuwal
  • A hirar Tambuwal da manema labarai, ya sanar da cewa bai ci amanar Wike a zabaen fitar da gwanin PDP na Shugaban Kasa ba
  • Wike yana daga cikin mutanen da su ka marawa tsohon gwamnan baya, shi kuma tsohon gwamnan ya goyi bayan Atiku Abubakar a 2023

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa zai yi martanin da ya dace ga Sanata Aminu Tambuwal.

Lere Olayinka, mai taimaka wa Wike a kan yada labarai ne ya bayyana haka bayan hirar tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato da manema labarai.

Kara karanta wannan

2027: APC ta ba 'yan adawa satar amsa, ta fadi kuskuren Atiku, Obi da El Rufa'i

Wike zai yi martani ga Tambuwal
Hoton Ministan Abuja, Nyesom Wike da Sanata Aminu Waziri Tambuwal Hoto: Aminu Tambuwal
Source: Facebook

The Cable ta wallafa cewa a cikin hirar, Tambuwal, wanda ke wakiltar Sokoto ta Kudu a majalisar dattijai, ya musanta zargin da ake masa kan Wike.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tambuwal: 'Ban ci amanar Wike ba'

The Nation ta ruwaito cewa tsohon gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya ce bai ci amanar Wike ba a lokacin zaben fitar da gwanin shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a shekarar 2022.

Tambuwal ya ce har yanzu dangantakarsa da Wike tana da kyau, kuma bai taɓa karya wata yarjejeniya da suka yi ba.

A cewarsa:

"Ba ni da wata matsala da Wike. Ban ci amanar kowa ba. Cin amana yana faruwa ne idan ka yi yarjejeniya da mutum, sai ka karya."

Tambuwal ya janye daga takarar shugaban ƙasa a wajen zaben fitar da gwani na PDP sannan ya nemi magoya bayansa su mara wa Atiku Abubakar baya.

Wannan mataki, a cewar masu sharhi, ya sauya yanayin zaben, yana bai wa Atiku damar samun nasara a kan Wike.

Kara karanta wannan

APC ta yi martani bayan Tambuwal ya zargi Tinubu da shirin ruguza 'yan adawa

Martanin Wike ga Tambuwal

Rahotanni sun Wike ya kasance ɗaya daga cikin masu goyon bayan Tambuwal a zaben fitar da gwanin PDP a baya.

Wannan ta sa ya dauki abin da Tambuwal ya yi a 2022 a matsayin cin amana da karya amintar da ke tsakanisu.

Ana zargin Tambuwal da cin amanar Wike
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike Hoto: Nyesom Ezenwo Wike
Source: Facebook

A cikin wata sanarwa da hadimin Wike, Lere Olayinka ya fitar a ranar Litinin, ya ce:

"Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, zai fitar da martani kan duk abubuwan da Sanata Aminu Tambuwal ya fada a ranar Juma’a da ta gabata."
"Baya ga kalaman da ya yi kan Ministan, Tambuwal ya yi wasu maganganu marasa dadi a kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kuma hakan ba zai wuce ba tare da amsa ba."

Olayinka ya ƙara da cewa:

"Saboda haka, abin da zan iya cewa yanzu shi ne, Ministan zai yi martani yadda ya kamata. Zai bayyana wa ’yan Najeriya menene cin amana, da kuma menene mutunci. Sai mu ci gaba da jira."

Kara karanta wannan

"Yaudara ce": Gwamna Uba Sani ya fallasa 'yan siyasa kan matsalar rashin tsaro

Tambuwal ya magantu kan zaben Shugaban Kasa

A baya, mun wallafa cewa tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana zabinsa a takarar Shugaban Kasa a zabe mai zuwa.

Tambuwal ya ce zai fi marawa tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar baya fiye da Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike.

Tsohon kakakin majalisar wakilan ya kuma yi bayanin tarihin siyasarsa, inda ya bayyana dalilin da ya sa ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC a baya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng