2027: Yadda Jonathan Ya Nuna Layinsa kan Takara duk da Rashin Goyon bayan Matarsa

2027: Yadda Jonathan Ya Nuna Layinsa kan Takara duk da Rashin Goyon bayan Matarsa

  • Ta na sama ta na dabo kan takarar tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan a zaben shekarar 2027 da ke tafe
  • Watakila Jonathan ya dage kan tsayawa takarar shugabancin kasa a 2027 duk da rashin goyon bayan matarsa Patience Jonathan a lokuta da dama
  • Rahotanni sun nuna cewa magoya bayan Jonathan na gudanar da taruka a kasashen waje domin karfafa tushensa a PDP

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon shugaban kasa a Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya dage kan shirin tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Goodluck Jonathan na duba yiwuwar tsayawa takara a zaben 2027 duk da rashin goyon bayan matarsa, Patience Jonathan.

Ana hasashen Jonathan na son takara duk da rashin goyon bayan matarsa
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan da matarsa, Patience Jonathan. Hoto: Goodluck Jonathan.
Source: Facebook

The Guardian ta ce a wani biki da aka yi a Abuja a Mayu 2025, Patience ta nuna damuwa kan matsin lambar da ke cikin mulki.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare, kotu ta yi hukunci kan halascin takarar Jonathan a zaben 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Patience ta ce a yanzu ba ta bukatar komawa 'Aso Rock' tana cewa ta fi bukatar kwanciyar hankali da zaman lafiya kawai.

Wani hasashen ake yi na takarar Jonathan?

Sai dai rahotanni daga gefen Jonathan sun tabbatar cewa tsohon shugaban bai damu da rashin amincewar matarsa ba, ya kara dagewa wajen yin shiri.

Domin gujewa tsoma bakin magoya bayan gwamnati, an ce mabiyansa sun gudanar da taruka da dama a kasashen waje don tsara dabaru.

Wani babban abu da tarukan suka mayar da hankali a kai shi ne yadda za su magance matsalar Nyesom Wike da ke adawa da takararsa.

Wike ya ce bai kamata Jonathan ya tsaya ba domin kiyaye mutuncinsa a matsayin dattijo, ya kuma zargi magoya bayansa da munafurci.

Sai dai wani daga cikin mabiyan Jonathan ya bayyana cewa:

“Adawar Wike barazana ce, shi yasa muke tsara yadda za mu magance shi.”
Akwai alamun Jonathan zai tsaya takara a zaben 2027
Tsohon shugaban kasa a Najeriya. Goodluck Ebele Jonathan. Hoto: Goodluck Jonathan.
Source: Facebook

Abin da Jonathan ke bukata daga 'yan PDP

Kara karanta wannan

Yadda shugaba Tinubu ke yawan nadin mukamai ya warware daga baya

Jonathan ya umarci magoya bayansa karkashin Gwamna Bala Mohammed na Bauchi su tabbatar da cewa PDP ba ta rasa nagartattun mutane ba.

Rahotanni sun ce Jonathan ya shawo kan Gwamna Duoye Diri na Bayelsa ka da ya sauya sheka zuwa APC, domin kare PDP a Kudu maso Kudu.

Game da rashin goyon bayan matarsa, wani ya ce:

“Wannan ba matsala ba ce, lokacin Yar’Adua ma ta yi hakan amma bai hana shi fitowa ba.”

The Sun ta ce wasu kuma sun soki shirin Jonathan da cewa bai da hurumin sake tsayawa takara, kasancewar an taba rantsar da shi sau biyu.

Sai dai magoya bayansa sun wallafa hukuncin kotu da ya tabbatar cewa yana da hurumin tsayawa takara, wanda ya kawo karshen wannan jita-jita

2027: Kotu ta yi hukunci kan takarar Jonathan

Mun ba ku labarin cewa an samu sabon hukunci kan cancantar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan na shiga takarar zaben shugaban kasa a 2027.

Wata kotu a Yenagoa ta yanke hukuncin bayan da wasu 'yan jam'iyyar APC suka shigar da kara kan hana Jonathan yin takara.

Mai shari'a Isa H. Dashen ya bayyana cewa Jonathan na da 'yancin takara, kuma ya yi bayani kan sashe 137(3).

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.