Harin Kaduna: El Rufa'i, Jagororin ADC Sun Yi Fatali da Gayyatar Ƴan Sanda
- Rundunar ƴan sanda ta gayyaci tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, da jagororin ADC su gurfana a gabanta
- Gayyatar ta biyo bayan zargin karya doka tare da haɗa taron siyasa ba tare da sahalewar hukuma ba da ta da fitina
- Amma Nasir El-Rufai ya zargi ƴan sanda da take dokar ƙasa bayan rufe ofishin ADC a Kaduna tare da kai su kara
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta gayyaci tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, tare da wasu manyan jam’iyyar ADC guda shida.
Rundunar ta gayyace su bisa zargin haɗin baki, tayar da fitina da kuma kawo cikas ga zaman lafiya.

Source: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa wannan na kunshe a cikin wasiƙar da Mataimakin Kwamishinan ƴan sanda mai kula da sashen CID, DCP Uzairu Abdullahi, ya sanya wa hannu a ranar 4 ga Satumba, 2025.

Kara karanta wannan
Tirkashi: El Rufai ya kai ƙarar kwamishinan ƴan sanda da wasu jami'ai ga hukumar PSC
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan ADC da 'yan sanda suka gayyata
Ƴan siyasar da rundunar ta gayyata a cikin wasiƙar sun haɗa da: Malam Nasir El-Rufai; Bashir Sa’idu da Jafaru Sani.
Sauran sun hada da Ubaidullah Mohammed da Nasiru Maikano da Aminu Abita da Ahmed Rufa’i Hussaini.
Rundunar ta umarci shugaban jam’iyyar ADC a jihar da ya gabatar da su a gaban sashen binciken manyan laifuka a ranar 8 ga Satumba, 2025.
Amma har har ranar ta wuce, ba a ga El-Rufa'i da sauran wadanda aka gayyata a ofishin 'yan sandan ba.

Source: Facebook
Sai dai kafin wannan rana ta yi, jami’an tsaro sun rufe ofishin ADC na jihar da ke titin Ali Akilu a Kaduna a lokacin da ake da ran manyan jam'iyya a Arewa maso Yamma za su ziyarci jihar.
Wannan ziyara ta biyo bayan harin da ƴan daba suka kai wa ƴa jam’iyyar makon da ya gabata, inda aka ji wa wasu rauni.

Kara karanta wannan
'Talauci ya yi muni a Najeriya,' El Rufa'i ya ce akwai mafita kan matsin tattalin arziki
El-Rufai ya zargi ƴan sanda da take dokar ƙasa
A taron manema labarai da ya gudanar a gidansa, El-Rufai ya caccaki ƴan sanda, inda ya ce rufe ofishin ADC da kuma hana taron jam’iyyar ya saɓa doka.
Ya ce jami’an ƴan sanda sun yi amfani da hujjar wani umarnin kotu da ba a gabatar masu ba a matsayin dalilin haramta taron.
El-Rufai ya yi nuni da cewa duk da hakan, shugabannin ADC sun yanke shawarar bin umarnin kwamishinan ƴan sanda domin gujewa rikici.
Ya ƙara da cewa za su bi matakan doka har zuwa kotun koli domin kalubalantar abin da ya kira cin zarafi.
El-Rufa'i ya kai karar Kwamishinan Yan sanda
A baya, mun wallafa cewa rikici tsakanin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da rundunar ‘yan sanda a jihar ya ɗauki sabon salo bayan harin taron ADC.
Tsohon gwamnan Kaduna ya ɗauki mataki a kan abin da ya kira cin zarafi da take hakkin ɗan Adam bayan yan sanda sun rufe ofishin ADC da ke jihar Kaduna.
Tsohon gwamnan ya kai karar Kwamishinan yan sanda, Rabiu Muhammad, da wasu jami’an rundunar tare da zarginsu da rashin ƙwarewa da cin zarafi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng