Shin Jonathan na da Hurumin Sake Zama Shugaban Najeriya? An Ji abin da Doka Ta Ce

Shin Jonathan na da Hurumin Sake Zama Shugaban Najeriya? An Ji abin da Doka Ta Ce

Abuja - A yayin da Najeriya ke tunkarar kakar zabe ta 2027, ana ta hasashen wadanda za su iya tsayawa takara a zaben, ciki har da Goodluck Ebele Jonathan.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sai dai babbar tambaya ita ce: Shin Jonathan na da hurumin sake zaman shugaban Najeriya bisa kundin tsarin mulki?

An fayyace abin da doka ta ce game da cancantar takarar Goodluck Jonathan a zaben 2027
Hoton tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan. Hoto:@GEJonathan
Source: Facebook

Akwai wasu jiga-jigai a jam'iyyar PDP da ADC da suke ganin Jonathan, wanda ya yi mulki daga 2010 zuwa 2015, zai iya kalubalantar shugaban kasa mai ci, Bola Tinubu, cewar rahoton Vanguard.

A wannan rahoto, za mu yi nazari kan tarihin mulkin Jonathan, tanadin kundin tsarin mulki kan wa’adin mulkinsa, hukuncin kotu da ra’ayin masana, don gano gaskiya kan matsayar takararsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Jonathan ya hau kujerar mulkin Najeriya

Goodluck Jonathan, wanda aka haifa a ranar 20 ga Nuwamba, 1957 a Otuoke, jihar Bayelsa, ya zama shugaban Najeriya bayan rike wasu manyan mukamai a baya.

Kara karanta wannan

Donald Trump ya sha alwashin hana Tinubu samun tazarce a 2027? Gaskiya ta fito

Jonathan ya fara siyasa a jihar Bayelsa, inda ya zama mataimakin gwamna daga 1999 zuwa 2005, daga baya ya zama gwamna daga 2005 zuwa 2007, inji rahoton Hope Global Forums.

A 2007, ya zama mataimakin shugaban kasa a karkashin Umaru Musa Yar’Adua, har zuwa lokacin da ya rike matsayin shugaban kasa na rikon kwarya saboda rashin lafiyar Yar'Adua.

Bayan mutuwar Yar’Adua a ranar 5 ga Mayu, 2010, aka rantsar da Jonathan a matsayin shugaban kasa a ranar 6 ga Mayu, 2010 don kammala wa’adin Yar’Adua har zuwa 29 ga Mayu, 2011.

A watan Afrilu 2011, Jonathan ya tsaya takara a zaben shugaban kasa kuma ya yi nasara da kashi 72.8% kan Muhammadu Buhari na jam’iyyar CPC.

Ya yi mulki har zuwa 2015, lokacin da ya sha kaye a hannun Buhari. Amincewarsa da sakamakon zabe ya sa ya kafa tarihi, domin shi ne shugaban Najeriya na farko da ya mika mulki cikin lumana.

A takaice, an taba rantsar da Jonathan sau biyu: a 2010 ta hanyar gadon mulki, da kuma a 2011 bayan ya lashe zabe.

Kara karanta wannan

Romon siyasa: Kansila ya naɗa sababbin hadimai 18, ya raba masu wurin aiki a Kaduna

Abin da doka ta ce kan wa'adin mulki

Kundin tsarin mulkin 1999 (wanda aka yi wa gyare-gyare) ya fayyace batun wa’adin mulki, amma lamarin Jonathan na bukatar nazari na musamman, inji kundin hukumar NNHRC.

Ga abin da kundin mulki ya ce kan wa'adin shugabancin kasa:

  • Sashe na 135: Ya fayyace cewa wa’adin shugaban ƙasa na shekaru hudu ne. Idan mutum ya karɓi mulki saboda wata kaddara, hakan ba zai hana shi tsayawa takara daga baya ba.
  • Sashe na 137(1)(b): Ya fayyace cewa mutum ba shi da hurumin sake tsayawa takara idan ya taba lashe zabe sau biyu a baya. Jonathan dai ya taba lashe zabe sau ɗaya ne kawai a 2011.
  • Sashe na 137(3): Gyaran kundin tsarin mulki na 2018 ya bayyana cewa duk wanda ya karɓi mulki bayan rasuwar shugaban kasa mai ci ko gaza aiwatar da aiki, ba zai tsaya takara fiye da zabe ɗaya ba. Sai dai wannan gyara ya fara aiki daga 2018, don haka bai shafi shekarun da suka gabace shi ba.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare, kotu ta yi hukunci kan halascin takarar Jonathan a zaben 2027

Yanzu da aka fahimci abin da kundin tsarin mulki ya ce, tambayar ita ce: Shin wannan kwaskwarimar da aka yi wa sashe na 137(3) ya shafi Jonathan tun da abin ya faru kafin 2018?

Nazarin doka: Cancantar takarar Jonathan

Yawancin lauyoyi da masana sun yarda Jonathan bai karya doka ba, kamar yadda rahoton jaridar Business Day ya nuna.

Yadda aka fassara doka kan cancantar takara da sake shugabancin Jonathan:

  • Zabe daya kacal: Jonathan bai hau mulkin Najeriya a 2010 don an zabe shi ba, sai dai don karasa wa'adin Yar'Adua. Amma an zabe shi ne sau daya kawai a 2011.
  • Gyaran 2018 bai shafi shekarun baya ba: Sashe na 137(3) bai shafi abubuwan da suka faru kafin 2018 ba, don haka ba za ta yi aiki a kan Jonathan ba.
  • Kalubale na hujja: Wasu lauyoyi da masana suna ganin cewa rantsar da Jonathan sau biyu, a 2010 da 2011 za su hana shi sake mulki, amma kotuna sun kore wannan fassara.

A takaice, Jonathan bai kai iyakar wa’adin mulki da kundin tsarin mulki ya kayyade ba. Har yanzu yana da damar tsayawa takara, kuma ya zama shugaba.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya kawo tsarin jawo hankalin yara shiga makaranta a Borno

Alkalai da dama sun yanke hukuncin cewa, Goodluck Jonathan yana da ikon sake shugabancin Najeriya.
Goodluck Jonathan yana jawabi a taron da aka shirya kan zabukan dimokuradiyya a Yammacin Afrika. Hoto: @GEJonathan
Source: Twitter

Hukuncin kotuna da ra’ayoyin masana

Kotunan Najeriya sun taba fassara wannan doka sau da dama.

  • Kotun daukaka kara (Cyriacus Njoku v. Jonathan), 2015: Kotu ta ce rantsuwar 2010 ba ta samo asali daga zabe ba, don haka ba zai hana Jonathan sake tsayawa takara a 2015 ba.
  • Babbar kotun tarayya, Yenagoa (Justice Isa Dashen), 2024: Mun ruwaito cewa, kotun ta ce gyaran da aka yi wa sashe na 137(3) ba zai yi aiki kan Jonathan ba, a karar da wasu mambobin APC suka shigar.

Ra’ayin masana kan takarar Jonathan

  • Monday Ubani, SAN: Arise News ta rahoto babban lauyan ya ce: “Zabe daya tilo da Jonathan ya taba lashewa shi ne na 2011. Yana da cikakkiyar damar sake yin takara.”
  • Robert Azibaola (dan uwansa, kuma lauyansa): Mista Azibaola ya ce, “GoodLuck Jonathan yana da damar sake tsaya wa takara bisa cancantar doka.”
  • Solomon Okedara (lauya): Lauyan ya ce Jonatha bai lashe zabuka biyu ba, don haka bai karya doka ba.
  • Festus Keyamo da Chidi Odinkalu: Sun taba cewa Jonathan bai cancanci tsaya wa takara ba, inda suka hujja da gyaran da aka yi wa sashe na 137(3).

Kara karanta wannan

Fetur: Yadda harajin Tinubu zai shafi ma'aikata, masu sana'a, 'yan kasuwa da sauransu

Kammalawa: E, Jonathan ya cancaci yin takara

Bisa kundin tsarin mulki, hukuncin kotu, da ra’ayoyin masana, Goodluck Jonathan na da cikakkiyar damar tsaya wa takara a zaben 2027.

Ya taba lashe zabe daya kacal (2011–2015), yayin da ba za a iya sanya rantsuwarsa ta 2010 a lissafi ba. Gyaran 2018 da aka yi wa sashe na 137(3) bai shafi Jonathan ba.

A karshe, jam’iyyun siyasa da 'yan Najeriya ne kawai za su iya yanke shawara kan sake zamansa shugaban kasa, amma doka ta ba shi damar yin takara.

2027: PDP na son Jonathan ya fito takara

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu kusoshin PDP sun fara shirin dawo da Goodluck Jonathan takarar shugaban kasa a 2027, inda ya fara amince da bukatar.

Mataimakin sakataren yada labaran PDP ya ce Jonathan ya cancanci a sake nemansa saboda irin yadda ya jagoranci kasar a baya, da nasarorin da ya samu.

Ibrahim Abdullahi ya bayyana cewa mutane da dama suna kira da a dawo da Jonathan saboda yadda ya mika mulki cikin sauki a 2015, ba tare da rikici ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com