Hadakarsu Atiku na Kara Karfi, Malami Ya Hango abin da Zai Faru da Tinubu a 2027
- Wani babban fasto a Legas, Apostle Victor Oku, ya bayyana cewa, Shugaba Bola Tinubu ne zai samu nasara a zaben 2027 mai zuwa
- Apostle Victor Oku ya ce Ubangiji ya bayyana masa cewa Tinubu zai mulki Najeriya ne har na tsawon shekaru takwas, ba hudu ba
- Malamin ya ce Ubangiji na tare da Tinubu, kuma shi ne ya zabar wa ‘yan Najeriya shi domin ya warware matsalolin kasar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Babban fasto na Cocin Divine Mercy International da ke Legas, Apostle Victor Oku, ya yi hasashen cewa ba za a samu sabuwar gwamnat a 2027 ba.
Ya ce, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai sake cin zabe duk da hakadar da wasu manyan 'yan siyasa a kasar ke yi a kansa gabanin 2027.

Source: Twitter
Apostle Oku ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da jaridar The Sun, inda ya tuno da yadda ya hasashensa kan nasarar Tinubu a zaben 2023 ya tabbata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsadar rayuwa a gwamnatin Bola Tinubu
Apostle Oku ya yarda cewa ana fama da matsaloli a yanzu, amma ya ce Ubangiji zai juya lamarin nan ba da jimawa ba.
A cewar Apostle Oku, Ubangiji ya bayyana masa cewa za a sha bakar wahala a farkon mulkin Tinubu, amma abubuwa za su inganta bayan wani lokaci.
"Kodayake yunwa da wahalar rayuwa suna kara ta'azzara, Ubangiji ya ce nan ba da jimawa ba za mu yi farin ciki.
"Bai kamata mu dogara ga Shugaba Tinubu ba, sai dai mu dogara ga Allah, mu ga yadda zai jagorance mu don samun nasara kan kalubalen tattalin arziki da sauran matsaloli a karkashin mulkin Shugaba Tinubu."
- Apostle Victor Oku.
Ya kuma ce ba kasafai ‘yan siyasa ke cika alkawuran da suka dauka ba, don haka ne ‘yan Najeriya da dama ba su gamsu da gwamnatin ba.
Ya kara da cewa:
“Amma idan Allah ya zaɓi shugaba, yana da hanyar juya lamarin don amfanin kowa."
Malami ya yi magana kan hadakar ADC
Dangane da kafuwar jam'iyyar hadaka ta ADC da nufin korar Tinubu da jam’iyyarsa a 2027, Oku ya ce Ubangiji yana tare da gwamnatin, kuma Tinubu zai sake cin zabe a 2027, duk da duk shirin da ake yi a kansa.
Ya ce mutum ba zai iya warware nufin Ubangiji ba, kuma Ubangiji yana amfani da mutane don taimakon al’umma.
Ya kara da cewa dalilin da ya sa ake yawan sukar gwamnatin Tinubu da kuma yunkurin wasu na kin sake zaben Tinubu shi ne saboda kin yin abubuwa yadda aka saba, wanda hakan ya bar Najeriya a cikin mawuyacin hali.

Kara karanta wannan
Shugaba Tinubu ya tafi hutun shekarar 2025, ya lula zuwa kasashe 2 a nahiyar Turai
Apostle Uku ya kuma ce Ubangiji ne ya tabbatar masa cewa Tinubu zai ci zabe, kuma zai mulki Najeriya na tsawon shekaru takwas, kuma ‘yan Najeriya za su yi farin ciki a karshe.

Source: Twitter
'Ubangiji ne zai ba Tinubu nasara a 2027' - Oku
Malamin ya ci gaba da cewa:
"Suna da miyagu wadanda ba sa son nufin Ubangiji ya tabbata a cikin al'amuran kasar. Amma gaskiyar ita ce, dole ne zabin Ubangiji ya tabbata a karkashin wannan gwamnati.
"A halin yanzu, 'yan Najeriya suna kukan matsananciyar yunwa da wahalar rayuwa tun lokacin da shugaba Tinubu ya karbi mulki, wanda dabi'ar mutum ce ta yin kuka idan abubuwa ba su tafi daidai ba."
Apostle Oku ya ba da shawarar cewa ya kamata Shugaba Tinubu da majalisarsa su koma ga Ubangiji, domin samun daidaituwar lamura a kasar.
Ya ce Ubangiji ya zabe shi ne a kan sauran 'yan takara a 2023 saboda zai nemo mafita ga matsalolin kasar.
Gwamna zai jagoranci yakin zaben Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan Legas, Akinwunmi Ambode, ya bayyana goyon bayansa ga tazarcen Shugaba Bola Tinubu a 2027.
Ambode ya ce Shugaba Tinubu ya cancanci ya koma mulki ya yi wa'adi na biyu, domin ya karasa ginin da ya riga ya dora harsashinsa.
Tsohon gwamnan ya ce zai jagoranci yakin neman zaben Tinubu a jihohi 6, kuma shi kansa zai sake tsayawa takarar gwamnan Legas.
Asali: Legit.ng


