Shirin 2027: Tsohon Mataimakin Gwamna da Attajiri Mai Taimakon Jama'a Sun Fice daga PDP

Shirin 2027: Tsohon Mataimakin Gwamna da Attajiri Mai Taimakon Jama'a Sun Fice daga PDP

  • Gwamna Inuwa Yahaya ya kara kassara yan adawa a jihar Gombe yayin da ake shirye-shiryen babban zaben 2027
  • Tsohon mataimakin gwamnan Gombe, Tha’anda Jason Rubainu da wani jigon PDP sun jagoranci magoya bayansu zuwa APC
  • Sun bayyana cewa ayyukan ci gaba da Gwamna Inuwa ke aiwatarwa na daga cikin abubuwan da suka ja hankalinsu zuwa APC

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Gombe - Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Gombe, Mista Tha’anda Jason Rubainu, tare da jigon PDP, Hon. Jerry Joseph Damara, sun sauya sheƙa zuwa APC mai mulki.

Rubainu da Damara, tare da wasu fitattun ‘yan PDP da dama musamman daga mazabar Gombe ta Kudu, sun koma APC a hukumance.

Gwamna Inuwa da masu sheka.
Hoton Gwamna Inuwa tare da wadanda suka sauya sheka a fadar gwamnatin Gombe Hoto: @governorinuwa
Source: Twitter

Rahoton Leadership ya nuna cewa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ne ya jagoranci taron tarbar masu sauya shekar a fadar gwamnatin Gombe.

Kara karanta wannan

'Ana kai wa 'yan APC hari a Kano,' Ado Doguwa ya fadi halin da suka shiga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rubainu, ya yi mataimakin gwamna a ƙarƙashin tsohon Gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo daga 2011 zuwa 2015.

Sai dai ana kallon hadewarsa da Mista Damara a matsayin wata babbar dabara ta karfafa siyasa a jihar Gombe.

Me yasa manyan kusoshin PDP suka koma APC?

Damara, fitaccen mai taimakon jama’a kuma attajiri, ya bayyana cewa jagorancin Gwamna Inuwa musamman wajen ayyukan raya kasa da tsaro shi ne ya sa ya koma APC.

Ya ce:

"Ko'ina ka duba ayyyukan raya kasa ne a Gombe. Babu mai iya canza jihar nan face ya zuba gine-ginen more rayuwa, shi yasa zan kira gwamna da sarkin gine-gine da tsaro.

Ya ƙara da cewa ba shi kadai ya yanke shawarar komawa APC ba, har da magoya bayansa, inda ya yi alkawarin ba da cikakken goyon baya ga jam’iyya mai mulki.

Gwamnan Gombe ya karbe su hannu biyu

A jawabinsa, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana sauya shekar jiga-jigan a matsayin abu na musamman ga yan APC a Gombe da ma Najeriya baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Ta fara tsami tsakanin gwamna da ministan tsaro, APC ta fusata kan lamarin

Ya jaddada muhimmancin samun cikakken goyon baya daga yankin Gombe ta Kudu, inda ya amince cewa jam’iyyar ba ta tabuka abin kirki a zabukan da suka gabata ba.

Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe.
Hoton Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya yana jawabi ga manema labarai a Gombe Hoto: @Governorinuwa
Source: Twitter

Gwamnan Gombe ya godewa Tinubu

Inuwa Yahaya ya gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa samar da yanayi mai kyau na siyasa da inganta tattalin arziki, tare da yabawa matakin cire tallafin man fetur.

Game da nasarorin gwamnatinsa, Gwamna Inuwa ya ce:

“Ayyukan da muke yi a Gombe su ne abubuwan da ya kamata a yi shekaru 30 da suka gabata.”

Ya bayyana cewa manyan titunan da ake ginawa a karkashin shugabancinsa za su saukaka zirga-zirga, tare da yin alkawarin ƙara hanzarta aikin ci gaban jihar, rahoton Tribune Nigeria.

Babban jigon PDP a Gombe ya koma ADC

A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban kwamitin sulhu na jam'iyyar PDP a jihar Gombe, AVM Shehu Adamu Fura ya koma ADC.

AVM Shehu ya sanar da ficewarsa daga babbar jam'iyyar adawa watau PDP tare da komawa jam'iyyar haɗaka domin kifar da gwamnatin APC a zaɓen 2027.

Tsohon sojan saman Najeriya ya bayyana cewa matakin da ya dauka ya biyo bayan tattaunawa da nazari mai zurfi da ya yi game da makomarsa a siyasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262