Jigon APC Ya Tona Asirin Kwankwasiyya, Ya Faɗi dalilin Watsewa Kwankwaso

Jigon APC Ya Tona Asirin Kwankwasiyya, Ya Faɗi dalilin Watsewa Kwankwaso

  • Musa Ilyasu Kwankwaso ya yaba wa Bola Tinubu inda ya tabbatar da cewa mutane da dama sun fara fahimtar gaskiya
  • Ya bayyana cewa Hon. Jibrin Abdulmumin Kofa ya tabbatar babu wanda zai iya kayar da Tinubu a zaben shugaban kasa
  • Alhaji Musa Kwankwaso ya ce ya kamata a hada kai don cigaban kasa, ya yi suka kan rikice-rikicen siyasa a Arewa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Babba a APC a jihar Kano, Musa Ilyasu Kwanwkaso ya yi magana kan ayyukan alheri da Bola Tinubu ke yi a Arewa.

Musa Ilyasu Kwankwaso ya bayyana cewa suna daga cikin wadanda ke kokarin bayyanawa mutane ayyukan alherin Tinubu.

Musa Kwankwaso ya soki tsarin Kwankwasiyya a Kano
Jigon APC, Musa Ilyasu Kwankwaso da Shugaba Bola Tinubu da Rabuu Musa Kwankwaso. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

Musa Kwankwaso ya dura kan Kwankwasiyya

Tsohon kwamishina a Kano ya bayyana haka ne yayin hira da jaridar DCL Hausa wanda ta wallafa a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Al'umma sun samu sauƙi, ƴan bindiga sun hallaka rikakken ɗan ta'adda da yaransa 4

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin bidiyon, Kwankwaso ya ce bai taba yin nadamar tallata Tinubu ba saboda abubuwan ci gaba da yake yi.

Ya ce da yawa daga cikin yan Kwanwkasiyya sun gane gaskiya sun fara watsewa Rabiu Musa Kwankwaso a Kano.

Ya ce:

"Ko babu komai dole ka yabawa Tinubu a kan tsaro, a baya mun yi Jonathan har ake ganin mu ba Musulmai ba ne, aka zo aka yi Buhari abubuwa ba su sauya ba.
"Tinubu da ya hau dan Arewa ya nada a matsayin mai ba shi shawara kan harkar tsaro, Nuhu Ribadu."
Musa Kwankwaso ya bayyana ayyukan alherin Tinubu a Arewa
Shugaba Bola Tinubu da jigon APC a Kano, Musa Ilyasu Kwankwaso: All Progressives Congress, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Kwankwaso ya tabo batun yaudarar Kwankwasiyya

Kwankwaso ya yi magana kan hirar da aka yi da Hon. Kofa inda ya tabbatar da cewa dan majalisar ya gano gaskiya kan tafiyar Kwankwasiyya.

Ya kara da cewa:

"Ko jiya naga an yi hira da Kofa, a NNPP yake ya ba jam'iyyar gudunmawa kuma yana daya daga cikin magoya bayan Tinubu.

Kara karanta wannan

"Ba laifin Tinubu ba ne," Dan Majalisa daga Kano ya yi magana kan matsalar tsaron Arewa

"Amma ga shi jiya da bakinsa yana fada babu wanda zai ci zabe sai Tinubu, ya nunawa duniya cewa Kwankwaso yaudarar al'umma yake yi.
"Ya nunawa mutane su mayaudare ne har mai gidansa Kwankwaso, ya ce ba mai kayar da Tinubu ya ce duk yaudara ake yi amma ace sai ya kira sunan Kwankwaso.
"Kofa ya ga gaskiya, ya ga yaudara, ya yi taimako ya ga duk karya ake, yana son ci gaban Arewa ya ga Tinubu da gaske yake yana son ci gaban Arewa da Najeriya."

Musa Kwankwaso ya ce Hon. Kofa ya fadi gaskiya ya kamata a hada kai inda ya ce Yarbawa ba su yin fada kamar na 'yan Arewa.

Kwankwaso ya ce amma a Arewa kullum fada ake yi ko gwamna ya ba ka tikiti kana cin zabe shikenan kun fara rigima saboda kana son ci gaba da juya gwamnati bayan ka gama mulki.

Musa Ilyasu Kwankwaso ya yabawa Tinubu

Kun ji cewa jigon APC a Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce ayyukan da Bola Tinubu ke yi a Arewa ne ya sa manyan yan siyasa ke komawa APC.

Kara karanta wannan

Jibrin Kofa: Na kusa da Kwankwaso ya fadi matsalar Arewa a shirin kifar da Tinubu a 2027

Tsohon kwamishinan na Kano ya jero wasu manyan ayyuka da Tinubu ya fara aiwatarwa a Kano da wasu jihohi a Arewa.

Ya bayyana cewa akwai manyan yan siyasa da za su baro jam'iyyun adawa, su koma APC daga nan zuwa karshen 2025.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.