'Sun Ci Amanata,' Jonathan Ya Fadi abin da ba a Sani ba kan Faduwarsa Zaben 2015
- Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya bayyana cewa ya fadi zaben 2015 ne saboda cin amanar wasu 'yan siyasar kasar nan
- Jonathan ya bayyana haka ne a bikin cika shekaru 70 da haihuwa na tsohon shugaban ma’aikatan fadarsa, Mike Oghiadomhe
- Tsohon shugaban kasar ya yi bayanin halayen 'yan siyasar Najeriya, musamman na rashin gaskiya da kuma saurin cin amanar mutum
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Edo - Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce babban dalilin da ya sa ya fadi zaben 2015 shi ne cin amana daga 'yan siyasar da ya yarda su.
Jonathan ya bayyana haka ne a wurin bikin cika shekaru 70 na tsohon shugaban ma'aikatansa kuma tsohon mataimakin gwamnan Edo, Chief Mike Aiyegbeni Oghiadomhe.

Source: Twitter
Jaridar Punch ta rahoto cewa an gudanar da wannan babban taron ne a Benin, babban birnin jihar Edo, a ranar Alhamis, 4 ga Satumba, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Na fuskanci cin amana a 2015” – Jonathan
Jonathan, wanda ya nemi wa’adi na biyu amma ya sha kaye hannun Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC, ya ce:
“Siyasa a tsarin Najeriya siyasa ce ta cin amana. Na fuskanci cin amana sosai a lokacin zaben 2015. Abin takaici shi ne, da yawan ’yan siyasa baki biyu gare su.”
Ya kara da cewa:
“Abin da za su fada da safe, zai bambanta da abin da za su fada da rana, da kuma abin da za su fada da yamma. A cikin awa guda, mutum zai iya fadin maganganu masu karo da juna.”
Sai dai ya bambance Oghiadomhe daga irin wannan hali, inda ya bayyana shi a matsayin amintacce da ya cancanci a yaba masa.
Jonathan ya mika mulki cikin sauki a 2015
A lokacin zaben 2015, kafin hukumar INEC ta kammala sanar da sakamakon, Jonathan ya kira Buhari don taya shi murna, bisa nasarar da ya samu.

Kara karanta wannan
Rasuwar tsohon shugaban 'yan sandan Najeriya ta bar baya da kura, an samu bayanai
Daga baya ya bayyana cewa ya amince da zaben ne don gujewa zubar da jini da tashin hankali a kasar, domin a cewarsa, burin siyasa bai kai darajar rayuwar ɗan ƙasa ba.
A lokacin, an ta yada jita-jitar cewa, Jonathan ya yanke shawarar mika mulki ne, saboda takaicin irin cin amanar da 'yan siyasa suka yi masa.

Source: Facebook
Manyan baki a taron na hannun daman Jonathan
Mataimakin Gwamnan Edo, Dennis Idahosa, wanda ya wakilci Gwamna Monday Okpebholo, ya bayyana Oghiadomhe a matsayin jagora da ya gina turbar siyasar jihar da har yanzu ake dogaro da ita, inji jaridar Daily Trust.
Bikin ya samu halartar fitattun ’yan siyasa da masu mukami da suka hada da:
- Tsoffin gwamnonin Edo – Lucky Igbinedion, Prof. Osarhiemen Osunbor, da Adams Oshiomhole
- Tsohon gwamnan Gombe, Ibrahim Dankwambo
- Tsofaffin mataimakan gwamnan Edo – Rev. Peter Obadan da Pius Odubu
- Marvellous Omobayo
- Babban alkalin Edo, Justice Daniel Okungbowa
- Kakakin majalisar Edo, Blessing Agbebaku, tare da sauran ’yan majalisa.
Ayodele ya hango makomar Jonathan a 2027
A wani labarin, mun ruwaito cewa, malamin addinin Kirista, Primate Elijah Ayodele ya ce Goodluck Jonathan ba ya cikin 'yan takarar da za su iya cin zabe a 2027.
A wani bidiyo da ya fitar, Ayodele ya nuna cewa tsayar da Jonathan takara a 2027 zai zama asarar kuri'a, don ba zai iya kayar da Shugaba Bola Tinubu ba.
A cewar Primate Ayodele, 'yan takara uku ne rak za su iya kayar da Tinubu idan suka tsaya takara a zaben 2027, kuma babu Goodluck Jonathan a cikinsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

