Dalilin da yasa Jonathan ya amince da sakamakon zaben 2015 – Cif Ben Obi
- Wani na kusa da Jonathan ya bayyana dalilin da yasa Jonathan ya amince da sakamakon zaben 2015
- Obi ya ce sakamakon taron na jam'iyyun siyasa na ranar 14 ga watan Janairun shekara ta 2015 yasa Jonathan ya amince da sakamakon zabe
- Tsohon mai ba da Jonathan shawara ya ce yana farin ciki ganin yadda shugaba Buhari ke ambata jaruntakan Jonathan
Tsohon mai ba da shawara na musamman ga tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan a kan hulda tsakanin jam'iyyu, Cif Ben Obi, ya bayyana dalilin da yasa Jonathan ya amince har ma kafin a sanar da sakamakon zaben 2015.
Ben Obi ya bayyana cewa, sakamakon taron na jam'iyyun siyasa na ranar 14 ga watan Janairun shekara ta 2015, wanda aka sani da sanarwar Abuja da kuma kwamitin zaman lafiya na kasa, wanda tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar ya jagoranta yasa Jonathan ya amince da sakamakon zaben.
Sauran dalilai sune matsayin da babban sakatare na Majalisar Dinkin Duniya na wancan lokacin, Ban Ki Moon ya yi, da tsohon magajinsa Kofi Annan da sauransu.
Kamar yadda Legit.ng ke da labari, Obi wanda yanzu shine sakatare na jam'iyyar mai adawa ta PDP, ya kuma yaba wa Jonatan ganin yadda ya mika mulki a cikin lumana da kuma kishin kasar.
KU KARANTA: Labarai cikin Hotuna: Shugabannin jam'iyyun APC da PDP sun kaiwa Shugaba Buhari ziyarar ban gajiya
Obi ya ce: "Ina farin ciki ƙwarai da gaske cewa shugaba Buhari ya ambaci jaruntaka na Jonathan. Don haka, har ya zuwa yanzu, na ga Jonathan a matsayin shugaba wanda za a iya koyi da shi a kasar Afrika baki daya”.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng