'Dan Kwankwasiyya Ya Yi Ta Maza, Ya Zaɓi Wanda Ya Fi So tsakanin Kwankwaso da Tinubu

'Dan Kwankwasiyya Ya Yi Ta Maza, Ya Zaɓi Wanda Ya Fi So tsakanin Kwankwaso da Tinubu

  • 'Dan majalisar tarayya, Abdulmumin Jibrin, ya yi magana kan zaben shekarar 2027 da ke tunkarowa
  • Hon. Jibrin ya bayyana cewa akwai yiwuwar Shugaba Bola Tinubu zai lashe zaben shugaban kasa na 2027
  • Jibrin ya ce duk da kasancewarsa a NNPP mai hamayya, yana son Tinubu ya samu nasara a zaben da za a yi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - 'Dan majalisar wakilai daga jihar Kano, Abdulmumin Jibrin ya yi hasashen abin da zai faru a zaben 2027.

Hon. Jibrin ya bayyana kwarin gwiwar cewa Shugaba Bola Tinubu zai lashe babban zaben shugaban kasa da za a gudanar a 2027.

Dan majalisa ya yi hasashen zaben 2027 da nasarar Tinubu
Dan Majalisa, Abdulmumin Jinrin yayin ziyara ga Tinubu a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Jibrin zai goyi bayan Tinubu a zaben 2027

Jibrin wanda ke wakiltar Bebeji/Kiru na Kano karkashin NNPP ya bayyana hakan a shirin Politics Today na Channels TV ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Kusa a APC ya 'tabbatar' da tazarcen Tinubu, ya ce a jira 2027

'Dan majalisar ya ce a ganinsa babu wani abin da zai hana Bola Tinubu lashe zaben 2027 da ke tafe.

Ya ce:

“Babu abin da nake gani da zai hana shi nasara a 2027, ni mutumin Tinubu ne, kuma ina son shi.”

Da aka tambaye shi ko hakan na nufin zai zabi Tinubu akan Kwankwaso a zabe mai zuwa, sai ya ce yana so su hada kai.

A cewarsa:

“A’a, zan zabi Kwankwaso da Bola Tinubu su yi aiki tare, amma Tinubu a matsayin shugaban kasa."

Musabbabin barin Hon. Jibrin APC

Tun da farko, Jibrin ya kasance babban mai goyon bayan Tinubu, har ya shugabanci 'Bola Tinubu Support Group' kafin ya fice daga APC a 2022.

Ya bayyana rikicin cikin gida a APC a matsayin dalilin barinsa, sannan daga baya ya shiga NNPP tare da biyayya ga Rabi'u Musa Kwankwaso.

Sai dai zuwansa fadar shugaban kasa biyu a watan Agusta 2025 ya haifar da rade-radin cewa yana shirin sake daidaita alaka da Shugaba Tinubu.

Kara karanta wannan

'Ba Jonathan ba ne,' Malami ya ce mutane 3 ne za su iya kayar da Tinubu a 2027

Yiwuwar komawar Kwankwaso APC

A gefe guda kuma, ya ce Kwankwaso a shirye yake ya shiga APC, inda ya bayyana yiwuwar tattaunawa da kulla yarjejeniya.

Ya kara da cewa:

“A kan shiga APC, ya dade yana cewa ƙofofinsa a bude suke. Ko da yaushe ana tattaunawa da yiwuwar wani abu ya iya faruwa.”
Jibrin Kofa ya nuna goyon baya ga Tinubu
Hon. Abdulmumin Jibrin tare da Bola Tinubu. Hoto: Abdulmumin Jibrin.
Source: Twitter

Wani yanki ne ya kamata su yi mulki?

Hon. Jibrin ya kuma yi imani cewa yankin Kudu ya kamata ya kammala shekaru takwas a mulki, don adalci tsakanin bangarorin kasar nan.

Ya musanta cewa an zalunci Arewa, yana mai cewa ta fi samun mulki tsawon lokaci, don haka lokaci ya yi da za a fadi gaskiya.

Maganganun nasa sun fito ne a daidai lokacin da ake ta muhawara kan tsarin mulki da yiwuwar kafa sababbin hadin gwiwar siyasa.

NNPP ta magantu kan ganawar Jibrin da Tinubu

Mun ba ku labarin cewa jam’iyyar NNPP ta ce ba ta da wani shiri na hukunta Abdulmumin Jibrin kan ganawarsa da Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Shugaban yakin zaben Tinubu ya juya baya, ya yi wa APC barazanar faduwa a 2027

Sakataren yaɗa labaran NNPP na ƙasa, Ladipo Johnson, ya ce Jibrin Kofa bai aikata wani abu da ya sabawa jam’iyya ba.

A wata hira da ya yi, Jibrin Kofa ya bayyana cewa komai zai iya yiwuwa a siyasance, amma bai bayyana ko zai koma APC ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.