Sirika: Tsohon Ministan Buhari Ya Fadi Matsayarsa kan Shiga Hadaka
- Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika, ya kai ziyara zuwa fadar shugaban kasa da ke Abuja
- Hadi Sirika ya sha tambayoyi daga wajen hadimin mai girma Bola Tinubu kan ko ya shiga hadakar 'yan adawa
- Tsohon ministan ya kuma bayyana cewa ziyararsa ba ta da nufin yin kamun kafa dangane da tuhume-tuhumen da hukumar EFCC ke yi masa.
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon ministan sufurin jiragen sama a gwamnatin Muhammadu Buhari, Hadi Sirika, ya yi magana kan shiga hadakar 'yan adawa.
Hadi Sirika ya nesanta kansa daga hadakar 'yan adawa da ake yi don hana Shugaba Bola Tinubu sake lashe zabe a shekarar 2027.

Source: Facebook
Hadi Sirika ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa a shirin 'Morning Brief' na tashar tashar Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hadi Sirika ya musanta batun shiga hadaka

Kara karanta wannan
Tinubu ya amsa kira kan kirkirar 'yan sandan jihohi, ya gano sirrin magance ta'addanci
Tsohon ministan ya musanta rahotannin da ke cewa ya shiga cikin hadakar 'yan adawa da suka sha alwashin ganin bayan APC a 2027.
Da aka tambaye shi game da batun shiga hadakar 'yan adawa, sai ya ka da baki ya ce:
“A’a, ba ni ba ne."
Tsohon ministan ya tabbatar da cewa ya ziyarci fadar shugaban kasa a Abuja ranar Talata, inda ya gana da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga.
"Jiya, ina tare da Cif Bayo Onanuga a fadar shugaban kasa, sai ya ce wai ni ina cikin hadaka."
“Na gaya masa ba ni ba ne, kuma ba zan taɓa kasancewa ba. Ya ce ya samu wannan labari daga rahotanni. Mutane na iya shiga hadaka, ai dimokuradiyya ake yi."
- Hadi Sirika
Me Sirika ya je yi fadar shugaban kasa?
Sai dai lokacin da aka tambaye shi ko ziyararsa zuwa fadar shugaban kasa domin neman sassauci ne kan tuhume-tuhume da EFCC ke yi masa, tsohon ministan ya ce har yanzu shari’arsa tana gaban kotu.
Ya bayyana cewa bai kamata ya yi sharhi a kan batun ba tun da yana gaban kotu

Kara karanta wannan
Malami: Ministan Buhari ya bayyana yadda 'yan daba suka farmake shi, ya nuna yatsa ga APC
"Manufar wannan ziyara ita ce gaisuwar ta’aziyya ga shugaban kasa wanda ya yi abin a yaba, bayan rasuwar shugabanmu, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari."
“Haka kuma mu nuna masa godiya bisa abin da ya yi, tare da tabbatar masa da goyon bayan jam’iyyarmu wanda shi ne jagoranta."
"Abin takaici, wannan batu yana gaban kotu, don haka ba batun da ya kamata a yi ta tattaunawa da manema labarai ba ne."
“Ni mutum ne tsarkakakke. Na yi aiki tare da mutane. Gwamnati na da dukkan kayan aiki a hannunta domin bincikar hali da gaskiyata."
- Hadi Sirika
Hukumar EFCC na tuhumar Hadi Sirika
Hukumar EFCC tana zargin Hadi Sirika da bayar da kwangiloli na biliyoyin Naira ga kamfanonin da iyalansa suka mallaka, ciki har da ‘yarsa, Fatima Sirika, da surukinsa, Jalal Hamma.

Source: Twitter
EFCC ta yi zargin cewa Sirika ya raba wata kwangilar sufurin jiragen sama ta tarayya mai darajar Naira biliyan 2.7 domin kaucewa amincewar hukumomi, sannan ya bai wa kamfanonin da iyalansa ke da iko da su.
EFCC ta ce kamfanin ‘yarsa da surukinsa, mai suna Al Buraq Global Investment Limited, ya karɓi Naira biliyan 1.3 kan wata kwangilar da ba a aiwatar da ita ba.
Hadi Sirika ya musanta zancen barin APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ya yi magana kan batun ficewa daga APC.
Sirika wanda ya taba wakiltar Arewacin Katsina a majalisar dattawa ya musanta cewa ya sauya sheka daga APC zuwa jam'iyyar adawa ta ADC.
Tsohon ministan ya bayyana cewa zai ci gaba da yin biyayya ga jam'iyyarsa ta APC wadda ya yi minista har sau biyu a gwamnatinta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
