Masoyan Buhari Sun Dauki Matsaya kan Wanda Za Su Marawa Baya a Zaben 2027
- Batun 'yan CPC na daya daga cikin matsalolin da ake ganin sun addabi jam'iyyar APC mai mulki yayin da ake tunkarar zaben 2027
- A jiya Talata, kungiyar masoyan Buhari (TBO) ta ziyarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar mulki da ke birnin tarayya Abuja
- 'Yan kungiyar, wadanda suna daga cikin asalin yan CPC sun tabbatar da goyon bayansu ga Tinubu, wanda suka bayyana da abokin siyasar Buhari
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Kungiyar masoyan marigayi Muhammadu Buhari, The Buhari Organisation (TBO), wacce ta shahara a siyasar Najeriya ta ziyarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Masoyan tsohon shugaban kasar sun bayyana cikakken goyon bayansu ga Bola Ahmed Tinubu, tare da yin alkawarin mara masa baya a babban zaben 2027.

Source: Facebook
TVC News ta ce a karkashin jagorancin tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Tanko Al-Makura, kungiyar ta kai ziyara fadar shugaban kasa a Abuja ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wace matsaya masoyan Buhari suka dauka?
Kungiyar TBO ta tabbatar wa Tinubu cewa bangaren CPC da ta narke a cikin jam'iyyar APC na tare da shi kuma za su goyi bayan tazarcensa a zabe na gaba.
Tanko Al-Makura ya ce:
“Muna tare da kai a zukata da kuma ayyukanmu, Allah Ya kara maka ƙarfin gwiwa wajen ci gaba da jagorantar ƙasarmu.”
Ya kuma tuna da wahalhalun da CPC ta sha kafin hadakar da aka kafa APC, inda ya bayyana Tinubu da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a matsayin masu hangen nesa.
"Shugabana, kai da Buhari ba abokan siyasa kadai ba ne, kun yi tarayya wajen hangen nesa, adalci, gina tattalin arziki da nagartaccen shugabanci.
"Tare kuka kirkiro kuma kuka gina dandalin siyasa wanda har yanzu shi ne abin alfahari da akidarmu."
- Tanko Al-Makura.
Tajudden Abbas ya jaddada mubaya'ar 'yan CPC
Shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, shi ma ya jaddada mubaya'arsu ga Shugaba Bola Tinubu, cewar rahoton This Day.
Ya fadawa Tinubu cewa:
"A karon farko, yau tsofaffin ‘yan CPC sun hadu wuri guda sun gana da mai girma shugabanmu. Ina tabbatar maka da cikakken goyon bayan dukkan tsofaffin mambobin CPC.
"Sama da kaso 90% na shugabannin farko na CPC har yanzu mutane ne masu biyayya kuma su na tare da kai."
Shugaba Tinubu ya ja hankalin 'yan CPC
Da yake jawabi ga tawagar, Shugaba Tinubu ya bukaci yan bangaren CPC watau masoyan Buhari da kar su bari wani abu ya karkatar da su daga manufar ci gaba.
“Kada ku bari wani ya maku barazana da abin da ba shi da tabbas, mun san hanyar da muka dauko kuma muna da yakinin akwai alamun nasara."

Source: Facebook
Ya kuma tuna da tsohon abokinsa Buhari da cewa:
"Da farko ina ba ku hakuri saboda na zo makare. Wannan shi ne bambanci tsakanin Muhammadu Buhari da Bola Tinubu. Idan da shi ne, da ya iso da wuri.”
Tinubu ya kuma yi alkawarin girmama tarihin Buhari, yana mai cewa daya daga cikin abubuwan da ya gada daga Buhari shi ne gaskiya, adalci da rikon amana.
Tinubu ya kwantar da hankulan masoyan Buhari
A wani labarin, kun ji cewa Bola Tinubu ya bukaci magoya bayan Muhammadu Buhari su kara hakuri domin akwai mukamai da dama da har yanzu bai jada ba.
Da yake ganawa da su a Aso Rock, shugaban kasa ya tabbatar wa yan kungiyar Buhari watau TBO cewa akwai guraben jakadun Najeriya a kasashen waje.
Shugaba Tinubu dai har yanzu bai fitar da sunayen jakadun da za su wakilci Najeriya a kasashen waje ba, kusan shekaru biyu bayan ya hau mulki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


