2027: 'Yan Siyasa 5 da Ake Hasashen Za Su Tsaya Takarar Shugaban Kasa a PDP
- Jam’iyyar PDP ta tura tikitin takarar shugaban kasa zuwa Kudu, inda ake hasashen fitattun yan siyasa biyar na iya yin takara
- Wannan mataki ya tabbatar da cewa dan takarar mataimakin shugaban kasa zai fito daga yankin Arewacin Najeriya
- Sai dai rikice-rikice a cikin jam’iyyar na iya ba ADC dama, yayin da wasu jiga-jigai suka soki tsarin tura takara Kudu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Siyasar Najeriya ta fara zafi tun ana saura kusan shekaru biyu kafin zaben shekarar 2027 da ke tafe.
Tun bayan tura tikitin takarar shugaban kasa zuwa Kudancin Najeriya da PDP ta yi aka afara hasashe kan lamarin.

Source: Facebook
Wadanda ake tunanin za su nemi tikitin PDP
Tribune ta ruwaito cewa ta sanar da cewa PDP ta zabi kai tikiti zuwa Kudu domin takarar shugaban kasa a 2027 bayan taron NEC karo na 102 a Abuja
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dangane da yanayin siyasa na yanzu da tarihin PDP, an ambaci ‘yan siyasa biyar daga Kudu wadanda za a iya fafatawa da su.
Legit Hausa ta duba wadanda ake ganin za su iya neman takara a zaben shugaban kasar a 2027 karkashin PDP.
1. Goodluck Jonathan
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan na daga cikin wadanda ake tsammanin za su tsaya takara a 2027.
Jonathan ya mulki Najeriya daga 2010 bayan rasuwar marigayi tsohon shugaban kasa, Umaru Musa Yar'Adua zuwa 2015.
Kafin zaben 2023, ana ta rade-radin APC na iya tsayar da Jonathan, amma jam’iyyar ta karyata wannan rahoton na daukarsa a matsayin dan takara.
Har ila yau, an ce PDP na tattaunawa da Jonathan domin sake tsayawa takara inda ta ce daman bai bar jam'iyyar ba tun farko.
Matsalar da Jonathan zai iya samu
Sai dai Jonathan ya ja baya da siyasa kuma ko da zai yi mulki, ba zai iya yin fiye da shekaru hudu ba wanda shi ma ake da ta-cewa a kai.
A 2017 Marigayi shugaba Muhammadu Buhari ya amince da dokar da ta haramta a rantsar da mutum fiye da sau biyu a kan kujera guda.

Source: Facebook
2. Peter Obi
Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi ya dade da barin jam'iyyar PDP zuwa LP wanda ya yi mata takara a zaben 2023.
Peter Obi yana da farin jini musamman tsakanin matasa da sauran jama’a duba da mamakin da ya bayar a zaben da aka gudanar a 2023.
Matsalar da ke gaban Peter Obi
Sai dai a yanzu haka, Obi na daga cikin jiga-jigan tafiyar jam'iyyar hadaka ta ADC wanda ake ganin zai yi wahala ya dawo takara PDP.
An tabbatar da cewa PDP na tattunawa da shi domin yi masa alkawarin tikiti saboda shawo kansa duk da ya bar jam'iyyar tun a 2022.
An bayyana cewa shugaban gwamnonin PDP, Bala Mohammed, ya ce jam’iyyar na tunanin shawo kan Obi da tsohon shugaban kasa, Jonathan saboda 2027.

Source: Twitter
3. Seyi Makinde
Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, yana da tasiri sosai a Kudu maso Yamma, yana iya zama karfin matasa, duk da bai bayyana kwadayinsa na takarar ba.

Kara karanta wannan
Ministan Tinubu ya hango hadarin da PDP za ta shiga idan ta tsayar da Jonathan takara a 2027
Rahotanni sun nuna yadda hotunan takarar shugaban kasa na Makinde suka bazu a Kano da Jigawa, inda matasa ke cewa shi ne zai ceto Najeriya, cewar BusinessDay.
Matsalar da Makinde zai samu
Sai dai a cikin wadannan manyan 'yan siyasa, kusan Seyi Makinde yana cikin wadanda ake ganin ba su farin jini idan aka fita daga yankin da suke.
Wata matsala da zai iya samu shi ne ya fito daga yanki guda da Bola Tinubu. Bayan kasancewarsa daga Kudu maso yamma, kuma Bayarabe ne.

Source: Facebook
5. Udom Emmanuel
Tsohon gwamnan Akwa Ibom, Udom Emmanuel na daga cikin yan siyasa da ake ganin za su gwada karfinsa a zaben 2027.
Emmanuel ya taba tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 inda ake ganin zai iya shiga takara bayan PDP ta maida kujerar zuwa Kudu.
Tsohon gwamnan na daga cikin jiga-jigan PDP wanda ya mulki jihar Akwa Ibom daga shekarar 2015 zuwa 2023.
Wace matsala Emmanuel zai samu?
A baya an rahoto cewa gwamnan jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulkin kasa daga PDP.
Ko shi bai bar PDP ba, watakila idan ya nemi takara tun daga gida za a fara durkusar da shi, sannan bai da karbuwa a wajen yankin Kudu.

Source: Facebook
An fara maganar takarar mataimakin shugaban kasa
Kun ji cewa jam'yyar PDP ta zabi ta baiwa Kudu tikitin shugabancin kasa a 2027, lamarin da ya mayar da hankali kan wasu jiga-jigai.
Wadansu da ake ganin da yiwuwar su zama mataimakan shugaban kasa daga Arewa sun fito, ciki har da Gwamna Bala Mohammed.
PDP na fuskantar kalubale saboda matsalar hadin kai, karɓuwa ga jama’a, da biyayya ga jam’iyya, wanda zai tantance nasararta a 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


