"Ana Yiwa Arewa Aiki," Musa Kwankwaso Ya Hango Manyan 'Yan Adawa Za Su Koma APC
- Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce ayyukan da Gwamnatin Tinubu ke yi a Arewa ne ya sa manyan yan siyasa ke tururuwar komawa APC
- Tsohon kwamishinan na Kano ya jero wasu manyan ayyuka da Tinubu ya fara aiwatarwa a Kano da wasu jihohi a Arewacin Najeriya
- Musa Kwankwaso ya bayyana cewa akwai manyan yan siyasa da za su baro jam'iyyun adawa, su koma APC daga nan zuwa karshen 2025
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon.shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Jjigo a jam’iyyar APC kuma tsohon kwamishina a jihar Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso ya cika baki kan tazarcen shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a 2027.
Kwankwaso, Daraktan Kuɗi a hukumar Raya Kogunan Hadejia da Jama’are, ya yi ikirarin cewa kafin ƙarshen shekarar 2025, galibin jiga-jigan adawa za su bar jam’iyyunsu su koma APC.

Source: Facebook
'Dan siyasar wanda ya yi kaurin suna a Kano ya fadi haka ne a wata hira da aka yi da shi kan zaben 2027 mai zuwa, kamar yadda Tribune Nigeria ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Abin da yasa APC ke kara karbuwa'
A cewarsa, ‘yan Najeriya sun fahimci cewa APC ce kaɗai jam’iyyar da ke da karfin aiwatar da manufofin da za su amfanar da talakawa.
Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce a shekaru biyu da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya shafe yana mulki, ya zuba ayyuka a Kano da Arewa gaba daya, wanda zai kawo ci gaba.
Ya ce:
“Shugaban ƙasa Tinubu ya tabbatar da kansa a matsayin jagora mai hangen nesa, ya zuba ayyuka da dama da za su kawo ci gaba a fannin tsaro, tattalin arziki, da habaka jarin ɗan adam.”
Ya jaddada cewa wannan ne ya sa masu adawa da Tinubu suka rikice, har ta kai ga manyan jiga-jigai daga jam’iyyu daban-daban ke cigaba da sauya sheka zuwa APC.
Kwankwaso ya jero ayyuka da aka yi a Kano
Tsohon kwamishinan ya kawo misali da sauya shekar wasu jiga-jigan jam’iyyar NNPP a Kano, ciki har da Sanata Kawu Sumaila.
Musa Kwankwaso ya kuma yi nuni da ayyukan da gwamnatin Tinubu ta amince a yi su a Kano a matsayin abin da zai ƙara wa APC karfi a 2027.
Ya ce aikin titin Kano Northern Bypass, gyaran titin Kano–Kaduna–Abuja da aanya bututun mai daga Ajaokuta zuwa Kaduna da Kano da za a kammala a 2025, na nuna muhimmancin Arewa a wurin Tinubu.

Source: Facebook
Wadanne 'yan siyasa ne za su koma APC?
Dangane da yadda za ta kaya a 2027, Kwankwaso ya bayyana tabbacin cewa APC za ta samu galaba, ganin yadda ‘yan siyasa da jam’iyyu ke fuskantar rikice-rikice.
“Kafin wannan shekarar ta kare, manyan ‘yan siyasa za su koma APC tare da magoya bayansu, ba zan ambaci sunaye ba, amma dole su bi ƙa’idojin jam’iyya domin a ci gaba da tafiya cikin tsari da hadin kai,”
- in ji Musa Iliyasu Kwankwaso
Musa Kwankwaso ya tare wa Tinubu fada
A wani labarin, kun ji cewa Musa Illiyasu Kwankwaso, ya caccaki Hakeem Baba-Ahmed da Buba Galadima kan sukar da suke yiwa Bola Tinubu.
Jagoran na APC a Kano ya bayyana cewa yan siyasar biyu ba su karfi ko ikon hana Tinubu zarcewa zuwa zango na biyu a zabe mai zuwa.
Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi ikirarin cewa yankin Arewa ba zai juyawa Tinubu baya ba, domin ya kawo masa ayyukan ci gaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


