Rikicin Siyasa Ya Barke a Abuja, An Tsige Shugaban Majalisa saboda Alaka da PDP
- Kansilolin APC a karamar hukumar kwaryar Abuja (AMAC) sun tsige shugaban majalisarsu, Mathew Yare, tare da zabar sabon shugaba
- Sabon shugaban majalisar, Jankaro Ibrahim ya bayyana cewa matakin tsige Mathew da suka dauka ya yi daidai dokokin majalisa
- To sai dai kuma, Mathew Yare, ya fitar da sanarwa jim kadan bayan tsige shi, inda ya bayyana kuskuren da 'yan majalisar suka yi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Rikicin siyasa ya barke a majalisar karamar hukumar kwaryar Abuja (AMAC) yayin da wasu kansiloli da suka koma APC suka yi zaman tsige shugaban majalisar.
Wannan rikici ya samo asali ne bayan shugaban karamar hukumar AMAC, Christopher Maikalangu, ya sauya sheka daga PDP zuwa APC tare da magoya bayansa.

Source: Facebook
Sauyin shekar da Maikalangu ya yi ta karfafa jam’iyyar APC a cikin majalisa, inda yanzu suka mallaki kansiloli takwas daga cikin 12, cewar rahoton AIT.
Dalilin tsige shugaban majalisa a Abuja
Kansilolin APC sun gudanar da zaman tsige tsohon shugaban a karkashin jagorancin mataimakin shugaban majalisa, Tony Onoja, inda suka ce hakan ya zama dole.
Rahotanni sun nuna cewa an tsige Mathew Yare ne saboda, shi da wasu kansiloli uku sun ki sauya sheka zuwa APC, tare da jaddada biyayyarsu ga PDP.
An ce, saboda samun rinjaye, kansilolin APC takwas suka samu ikon zartar da hukunci a majalisar, lamarin da ya ba su damar sauya shugabanci cikin sauki.
Sabon shugaban majalisa ya kawo hujja
Bayan zaman tsige Yare, kansilolin APC sun gudanar da zabe, inda suka nada Jankaro Ibrahim daga mazabar Kabusa a matsayin sabon shugaban majalisar AMAC.
Da yake magana da manema labarai, Jankaro ya ce matakin ya dace da tsarin dimokuradiyya, domin ba zai yiwu marasa rinjaye su ci gaba da shugabanci ba.
Ya jaddada cewa jam’iyyar APC tana da kansiloli takwas yayin da PDP ke da hudu kawai, don haka jam’iyyar da ke da rinjaye ce ke da iko kan shugabancin majalisar.

Source: Facebook
Martanin tsohon shugaban majalisa
Sai dai, shugaban majalisar da aka tsige, ya bayyana cewa tsigewar da aka yi masa ba ta da inganci kuma ta saba da ka’idoji da dokokin dimokuradiyya.
A cewar Mathew Yare, abin da aka gudanar a majalisar ya zama babban cin zarafi ga tsarin dimokuradiyya da kuma dokokin da suka kafa majalisar AMAC.
Ya bukaci magoya bayansa da jama’ar AMAC su kwantar da hankalinsu, tare da tabbatar da zaman lafiya duk da rikicin da ake fuskanta a yanzu.
Tsohon shugaban AMAC ya koma APC
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon shugaban karamar hukumar kwaryar Abuja (AMAC), ya amince zai tsaya takarar gwamnan Anambra.
Wannan na zuwa ne yayin da tsohon shugaban, Prince Nicholas Ukachukwu ya sanar da sauya shekarsa zuwa jam'iyya mai mulki ta APC.
Prince Ukachukwu ya ce idan mutane suka zaɓe shi ya hau kan karagar mulki, zai magance matsalar tsaro, talauci da sauransu cikin watanni uku kaɗai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

