'Ba Jonathan ba ne,' Malami Ya Ce Mutane 3 ne Za Su Iya Kayar da Tinubu a 2027

'Ba Jonathan ba ne,' Malami Ya Ce Mutane 3 ne Za Su Iya Kayar da Tinubu a 2027

  • Fitaccen malamin addinin Kirista, Primate Elijah Ayodele ya yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kashedi gabanin zaben 2027
  • Primate Ayodele ya bayyana cewa Ubangiji ya nuna masa wasu ’yan siyasa uku da za su iya kayar da Tinubu idan suka tsaya takara
  • Sai dai malamin ya ce, Goodluck Jonathan, wanda ake ta yada jita-jitar tsayawarsa takara, ba ya cikin wadannan 'yan siyasa uku

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Primate Elijah Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, ya gargadi shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu game da zaben 2027.

Babban malamin addinin Kiristan, ya bayyana cewa akwai ’yan siyasa uku da za su iya kayar da Shugaba Tinubu a zaben 2027 mai zuwa.

Malamin addinin Kirista ya gargadi Tinubu kan mutanen da za su iya kayar da shi a 2027
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zaune a dakin taron TICAD 9 da aka gudanar a Japan. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Ayodele ya fadi makomar Jonathan a 2027

Primate Ayodele ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafin cocinsa na Facebook, inda yake bayani kan zaben mai zuwa.

Kara karanta wannan

Shugaban yakin zaben Tinubu ya juya baya, ya yi wa APC barazanar faduwa a 2027

A jawabinsa da ya yi a cikin bidiyon, Ayodele ya ce hankula sun karkata ne kan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, matsayin wanda zai kayar da Tinubu.

Sai dai malamin ya bayyana cewa Jonathan bai cikin cikin wadanda aka nuna masa a wahayin da ya samu, duk kuwa da maganganun da ake yi a siyasar kasar.

Mutanen da za su kada Tinubu a 2027

Primate Ayodele ya dage cewa Ubangiji ya nuna masa mutane uku da za su iya kayar da Tinubu, amma bai ambaci sunayensu a fili ba.

Wannan ya bar tambayoyi masu yawa a zukatan ’yan Najeriya kan su wanene wadannan mutane uku da ke iya yin tasiri a zaben 2027.

Kuma ko kafin wannan sabon bidiyon, a kwanakin baya, Primate Ayodele ya yi hasashen cewa 'yan takara biyu ne za su kayar da Tinubu a zaben mai zuwa.

Sai ga shi yanzu kuma ya ce mutane uku ne, kenan an samu karin mutum daya daga cikin mutane biyu na farko da aka fara bayyana masa.

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa bai kamata Jonathan ya fafata da Tinubu ba a 2027'

Kalli bidiyon a nan kasa:

Jam'iyyar PDP na son Jonathan ya dawo

A cikin jam’iyyar PDP kuwa, wasu jiga-jigai daga Arewa sun bayyana ra’ayinsu cewa Jonathan shi ne zabin da ya fi dacewa a 2027.

Malamin addini, Primate Ayodele ya ce Tinubu zai iya fuskantar barazana daga mutane 3 a 2027.
Primate Elijah Ayodele a yana wa'azi a cikin cocinsa, da Shugaba Bola Tinubu a wajen wani taro a Abuja. Hoto: @primate_ayodele, @DOlusegun
Source: Facebook

Sule Lamido, tsohon gwamnan Jigawa, ya shaida cewa Jonathan shi ne mutumin da zai iya fitar da PDP daga matsalar da take ciki, kuma ya iya kayar da APC.

Ya ce babu wani dan Kudu na PDP da ya kai kimar Jonathan, musamman ganin cewa ya samu karbuwa a sassa daban daban na kasar.

Jam’iyyar PDP ta fitar da sanarwa ta bakin kakakinta, Debo Ologunagba, inda ta tabbatar da cewa har yanzu Jonathan mamba ne na jam’iyyar.

Ologunagba ya ce jam’iyyar ta riga ta kammala tsarin da zai baiwa Kudu damar tsayar da dan takara, kuma nan gaba za a bayyana sunan mutumin.

"PDP na bukatar Kirista daga Kudu a 2027"

A wani labarin, mun ruwaito, gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed Abdulkadir, ya bayyana cewa, Kirista daga Kudu ne ya fi cancantar samun tikitin PDP a 2027.

Kara karanta wannan

Tsohon dan takarar shugaban kasa ya fadi kuskuren Tinubu kan zuwa Brazil

A cewar shugaban kungiyar PDP na kasa, mikawa Kirista daga Kudu takarar shugaban kasa, tare da abokin takara Musulmi daga Arewa, zai ba jam'iyyar nasara a zaben mai zuwa.

Gwamna Bala Mohammed ya ce PDP ba za ta maimaita irin kuskuren da APC ta yi a zaben 2023, inda ta yi amfani da Musulmi da Musulmi, lamarin da ya jawo rudani sosai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com