"Ku Daina": El Rufai Ya Shawarci Amaechi da Peter Obi kan Takarar Shugaban Kasa

"Ku Daina": El Rufai Ya Shawarci Amaechi da Peter Obi kan Takarar Shugaban Kasa

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya fito ya ba abokansa na tafiyar hadaka shawara kan takarar shugaban kasa
  • El-Rufai ya bayyana cewa alkawarin yin wa'adin mulki daya da Peter Obi da Rotimi Amaechi suke yi, ba abu ba ne mai yiwuwa
  • Ya nuna cewa babu wanda yake yarda wannan alkawarin na su, don haka ha kamata su daina yin sa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ba da shawara ga Rotimi Amaechi da Peter Obi kan takarar shugaban kasa.

Nasir El-Rufai ya bukaci su daina yin alkawarin yin mulki na wa’adin shekara huɗu kawai, domin babu wanda yake yarda da hakan.

El-Rufai ya ba da shawara ga Peter Obi da Amaechi
Hotunan Nasir El-Rufai, Peter Obi da Rotimi Amaechi Hoto: @elrufai, @GEJonathan, @MSLamido
Source: Twitter

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne a shirin 'Sunday Politics' na tashar Channels Tv a ranar Lahadi, 31 ga watan Agustan 2025.

Kara karanta wannan

'Ban taba abokantaka da Uba ba,' El Rufa'i ya fadi alakarsa da gwamnan Kaduna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amaechi da Peter Obi sun yi alkawari

Peter Obi ya sha nanata cewa idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban kasa a 2027, zai yi wa’adi ɗaya kawai, yana mai jaddada cewa shekaru huɗu sun isa a daidaita kasar nan.

Shi kuma Rotimi Amaechi ya bayyana cewa zai amince ya zama shugaban kasa na wa’adi ɗaya kawai a 2027, idan ya samu tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC.

Tsohon ministan sufurin ya kuma ce a shirye yake ya sauka daga mulki bayan shekara huɗu domin mutuntsa tsarin karba-karba da samun daidaito.

Wace shawara El-Rufai ya ba su?

Da aka tambaye shi kan irin waɗannan alkawuran, El-Rufai ya ce ya kamata Peter Obi da Amaechi, su fahimci cewa hakan ba mai yiwuwa ba ne.

Ya ce ya kamata daga kwarewarsu su fahimci cewa shekara huɗu ba su isa a yi gyare-gyare masu ma’ana a gwamnati ba.

"Game da batun mutane da ke fitowa suna cewa, ‘Zan yi wa’adi ɗaya’, bana ganin akwai wanda ya yarda da hakan. Ba daidai ba ne. Bai kamata ka yi watsi da abin da kundin tsarin mulki ya ba ka damar yi ba."

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: El Rufai ya fallasa abin da gwamnatin Tinubu ke yi wa 'yan bindiga

"Maganar gaskiya na yi shekara takwas a matsayin gwamna, kuma Amaechi da Peter Obi dukkansu sun taɓa zama gwamnoni, sun san lokacin da ake bukata don yin canji mai amfani a gwamnati. Shekara huɗu sun yi kadan."

- Nasir El-Rufai

El-Rufai ya ba Amaechi da Peter Obi shawara
Hoton tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai yana jawabi a wajen wani taro Hoto: @elrufai
Source: Twitter

Malam El-Rufai ya fadi halin 'yan siyasa

El-Rufai ya ce yawancin ’yan siyasa da ke yin irin wannan alkawari na yin wa’adi ɗaya kawai, daga bisani suna sauya ra’ayi bayan sun hau mulki.

"Don haka, ina roƙon kowa ya daina yin waɗannan alkawura na cewa ‘Zan yi shekara huɗu’ ko ‘Zan yi shekara takwas’, domin babu wanda ya yarda da ku."

- Nasir El-Rufai

El-Rufai ya zargi gwamnatin Uba Sani

A wani labarin kuma, kun ji cewa Nasir El-Rufai ya zargi gwamnatin jihar Kaduna ta dauko 'yan daba don tarwatsa taron jam'iyyar ADC.

Tsohon gwamnan ya yi zargin cewa gwamnatin Uba Sani ceta dauko 'yan daban da suka raunata mutane a wurin taron.

El-Rufai ya bayyana cewa yana da hujjojin da zai gabatar domin tabbatar da zargin da ya yi a kan gwamnatin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng