'Ban Taba Abokantaka da Uba ba,' El Rufa'i Ya Fadi Alakarsa da Gwamnan Kaduna
- Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i ya ce bai taɓa yin abota da gwamnan Kaduna mai ci, Uba Sani ba
- Ya bayyana haka ne bayan ya zargi gwamnan Kaduna da shirya harin da aka kai wa jam’iyyar ADC da sauran 'yan adawa
- Tsohon gwamnan ya ce zai gabatar da hujjoji ga Sufeton ƴan sanda a kan zargin da ya yi matukar akwai niyyar binciken lamarin
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya bayyana cewa magajinsa, Sanata Uba Sani, ba abokinsa ba ne.
Nasir El-Rufa’i ya bayyana haka ne bayan ya zargi gwamnatin Kaduna da hannu a harin da aka kai wa taron ƴan adawa a ranar Asabar a Kaduna.

Kara karanta wannan
Ba boye boye: El Rufa'i ya magantu kan zargin muzgunawa Kiristocin Kudancin Kaduna

Source: Facebook
El-Rufa'i ya yi wannan bayani ne a cikin shirin Sunday Politics na Channels TV a ranar Lahadi, 31 ga watan Agusta, 2025.
Nasir El-Rufa'i ya faɗi alakarsa da Uba Sani
Duk da yake shi ne ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar Uba Sani a zaben 2023, tsohon gwamnan ya ce bai taɓa yin abota da shi ba.
El-Rufa’i ya ce:
“Ban yi faɗa da gwamna ba. A’a, ba abokina ba ne. Yaro na ne, wanda na ba horo. Ba mu yi faɗa ba. Har yanzu ba na magana da shi.”
Ya ƙara da cewa babban abin alfahari a rayuwarsa shi ne ya taimaka wa mutane da dama su kai matsayi mai girma, wasu ma sun fi shi girman matsayi a yanzu.
Dalilin El-Rufa'i na sukar Uba Sani
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya ce ba zai iya yin shiru ba idan wanda ya ɗaukaka ta hanyarsa ya karkace daga abin da ya dace ba.
A yayin hirar, El-Rufa’i ya zargi Gwamna Uba Sani da shirya harin da aka kai a taron ƙaddamar da kwamitin jam’iyyar ADC a Kaduna a makon da ya gabata.

Source: Facebook
Ya ce:
"Ina da hujjoji; Gwamnan Jihar Kaduna ne ya shirya harin da aka kai ranar Asabar. Zan miƙa hujjojin ga IGP da sauran hukumomi idan suna son bincike.”
Tsohon gwamnan ya yi Allah-wadai da yadda ‘yan sanda suka tsaya suna kallo lokacin da aka kai wa ‘yan adawa hari, yana mai cewa tsarin tsaro ya durƙushe a Najeriya.
El-Rufa’i ya magantu kan tikitin Muslim Muslim
A baya, mun wallafa cewa Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana dalilin da ya sa ya mara baya ga tikitin Muslim-Muslim na jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa na 2023 da ya gabata.
Tsohon gwamnan Kaduna ya bayyana cewa an dauki matakin amfani da tsarin domin a ci zaben Shugaban Kasa a lokacin, amma ba shi da alaka da addini ko kabila.
El-Rufai ya bada misali da irin abin da ya aikata lokacin yana gwamna a Kaduna, inda ya zaɓi mataimakiya Musulma, inda ya ce hakan bai tauye hakkin kiristocin kasar nan ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
