'Yan Daba Sun Tarwatsa Taron Ƴan Adawa da El Rufa'i Ya Halarta a Kaduna, An Ji Raunuka

'Yan Daba Sun Tarwatsa Taron Ƴan Adawa da El Rufa'i Ya Halarta a Kaduna, An Ji Raunuka

  • Jam'iyyun adawa a Kaduna sun shiga tsaka mai wuya a lokacin da su ke kaddamar da kwamitin mika mulki na ƙungiyarsu a jihar
  • A ranar Asabar, 30 ga watan Agusta 2025 ne aka samu bayanin yadda ƴan daba su ka farmaki taron da Nasir El-Rufa'i ya halarta
  • Shaidu sun zargi ’yan sanda da sakaci, inda aka ce jami’an da aka tura wajen ba su tsawatar wa ƴan bangar ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Rikici ya barke a wajen kaddamar da kwamitin mika mulki da ƙungiyoyin adawa suka kafa a jihar Kaduna, a ranar Asabar, 30 ga watan Agusta, 2025.

Shaidu sun shaida cewa wasu da ake zargin ’yan daba ne sun shigo wajen taron da makamai irinsu adduna, sanduna da duwatsu.

Kara karanta wannan

Mazauna Katsina sun nema wa kansu mafita, sun kulla yarjejeniya da 'yan ta'adda

'Yan daba sun kai hari Kaduna
Hotunan wasu daga cikin mahalarta taron Kaduna da aka raunana Hoto: Abubakar Kanjest
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa matasan sun raunata mutane da dama tare da lalata motocin da mahalarta taron su ka ajiye.

Kwamitin dai ya haɗa ƴan jam’iyyun adawa da dama daga ciki har da PDP, SDP, NNPP, LP da ADC, tare da wani ɓangare na APC da ke adawa da shugabancin jam’iyyar a jihar.

Yadda aka gudanar da taron siyasa a Kaduna

Rahotanni sun bayyana cewa duk da tashin hankali da aka shiga, an ci gaba da gudanar da taron cikin yanayi na tsoro da rudani

Shaidu sun bayyana ɓacin ransu kan yadda jami’an ’yan sanda da aka tura wajen suka tsaya kawai suna kallo ba tare da sun shiga tsakani ba

Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, wanda ya halarci wajen taron, ya yi Allah-wadai da abin da ya faru, yana mai kiran shi a matsayin taɓarɓarewar doka da oda.

El-Rufa'i ya zargi ƴan sandan Kaduna

Kara karanta wannan

Yadda gini ya rikito kan maƙwabta a Zariya, an kwashi gawarwaki 4 nan take

Nasir El-Rufa'i ya zargi manyan jami’an ’yan sandan Kaduna, daga ciki har da wani Mataimakin Kwamishina da cewa sun tsaya suna kallo yayin da ake fasa dukiyoyin jama'a.

El-Rufai ya gargadi cewa idan ba a kawo ƙarshen dabi’ar ’yan daba cikin harkokin siyasa ba, abin zai zama barazana ga zaman lafiya.

El-Rufa'i ya magantu kan harin Kaduna
Hoton tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i Hoto: Nasir El-Rufa'i
Source: Facebook

Ya ce:

"Babu wanda ya fi kowa kwarewa a kan jawo tashin hankali, idan ba a ɗauki mataki ba, mu za mu ɗauki matakin tabbatar da cewa haka ba ta sake faruwa ba."

Ƴan adawa a Kaduna sun shiga damuwa

Shugaban jam’iyyar ADC a yankin Arewa maso Yamma, Jafaru Sani, shi ma ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.

Ya ce:

“Ba za mu bari a tsoratar da mu ba ko kuma a tilasta mana janyewa. Za mu ci gaba da gudanar da ayyukan siyasa da jajircewa.”

Sai dai Sakataren APC na jihar Kaduna, Alhaji Yahaya Baba-Pate, ya nesanta jam’iyyarsa daga lamarin, yana mai cewa APC ba ta da hannu a ɗaukar ’yan daba.

Ya ce:

“ADC da sauran jam’iyyu suna da ’yancin gudanar da harkokinsu ba tare da wani tsangwama ba."

Kara karanta wannan

Katsina: Yadda ƴan ta'adda su ka sace ɗiyar fitaccen ɗan kasuwar fetur da iyalinta

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Mansir Hassan, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce za a fitar da cikakken jawabi daga rundunar nan gaba.

Omokrii ya yabawa tsaron titin Kaduna-Abuja

A baya, mun wallafa cewa tsohon mai taimakawa shugaban ƙasa, Reno Omokri, ya bayyana cewa hanyar da ke a tsakanin Abuja da Kaduna ta samu lafiya.

A ranar Alhamis, 28 ga watan Agusta, 2025, Omokri tare da jarumin Nollywood Wale Ojo da wasu ‘yan jarida sun shiga hanyar ba tare da jami’an tsaro ba.

Omokri ya ce manufar ziyarar ita ce nuna wa duniya cewa tafiya ta hanyar Abuja–Kaduna yanzu babu barazan, saboda Bola Tinubu ya yi aiki sosai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng