PDP Ta Yi Wa APC Lahani a Jigawa yayin da Daruruwa Mambobi Suka Koma Adawa
- Shirye-shiryen babban zaben shekarar 2027 ya sanya wasu 'yan siyasa na sauya sheka daga wannan jam'iyya zuwa wancan
- Hakan ya kasance ga wasu mambobin jam'iyyar APC a jihar Jigawa, wadanda suka raba gari da jam'iyya mai mulki
- Mambobin sun koma jam'iyyar PDP mai adawa inda suka nuna cewa sun yi nadamar kasancewarsu a cikin APC
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
jam’iyyar APC mai mulki sun sauya sheka zuwa PDP a jihar Jigawa.
Mambobin na APC sun sauya sheka zuwa PDP ne a gundumar Sakwaya cikin karamar hukumar Dutse, a Jigawa.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce an gudanar da bikin sauya shekar ne a ranar Jumma’a a ofishin jam’iyyar PDP na gundumar Sakwaya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tarbi 'yan APC da suka koma PDP
Mataimakin shugaban PDP na jihar, Umar Danjani, ya wakilci shugaban jam’iyyar na jihar domin tarbar sababbin mambobin.
Umar Danjani ya yaba da taron jama’a mai yawa na fitattun ’yan adawa daga sassan jihar da suka halarci wurin, yana mai bayyana sauya shekar a matsayin babban karin karfi da haɗin kai ga jam’iyyar a shirye-shiryenta kafin zaɓe.
Ya nanata cewa kofar jam’iyyar PDP a bude take kuma a shirye take ta tallafa wa sababbin mambobin.
Mataimakin shugaban na PDP ya kuma yi kira ga dukkan ’yan siyasa a jihar da su gudanar da harkokinsu cikin lumana tare da kiyaye ka’idojin dimokuraɗiyya yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen zaɓen 2027.
"Mun tarbe ku hannu bibbiyu, kuma mun yi alkawarin aiki tukuru domin magance matsalolinku yayin da muke gina Jigawa tare."
"Kofofinmu a bude suke ga duk wanda ke da niyyar kawo ci gaba ga Jigawa. Tare da karfinku, mun kara kusantar samun haɗin kai da zai kawo dawwamammen ci gaba a jihar.”
- Umar Danjani

Source: Original
Meyasa mambobin APC suka koma PDP?
Tun da farko, Hajiya Harira Sakwaya, jagorar sababbin mambobin da suka sauya sheka, wadda kuma ita ce matar shugaban APC na gundumar, ta bayyana nadamar shiga APC a baya.
"Shiga APC babban takaici ne a gare mu. Muna godiya ga Sule Lamido wanda ya yi wa Sakwaya da mata a nan ayyuka masu yawa, abubuwan da ba za mu iya rama masa ba.”
- Harira Sakwaya
Harira Sakwaya ta kuma koka da gazawar APC wajen cika burin mambobinta, inda ta bayyana cewa shugabancin jam’iyyar ya gaza, lamarin da ya tilasta wa da dama daga cikinsu neman kyakkyawar makomar siyasa a cikin PDP.
APC ta lallasa jam'iyyar PDP a jigawa
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta yi rashin nasara a zaben cike gurbi da aka gudanar a mazabar majalisar wakilai ta Babura/Garki.
Dan takarar jam'iyyar APC, Alhaji Rabiu Mukhtar ya yi nasarar lashe zaben bayan ya samu mafi yawan kuri'un da aka kada.
Abokin hamayyarsa na PDP, Auwal Isah Manzo ya zo na biyu a zaben inda ya samu kuri'u 13,519.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

