'Sun Yanke Matsaya,' Kwankwaso Ya Hararo Abin da Talakawa za Su Yi a 2027
- Rabiu Musa Kwankwaso ya ce yunwa da tsananin talauci sun hana miliyoyin ‘yan Najeriya walwala, abin da zai tasiri zaben 2027
- Tsohon gwamnan Kano ya ce jama’a sun gama yanke shawarar abin da za su yi a zaben gaba saboda rashin tsaro da tabarbarewar tattali
- Madugun Kwankwasiyya ya gargadi mambobin NNPP da su guji ruɗani daga sauya sheƙa ko tattaunawar haɗin gwiwa da wasu jam’iyyu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa yawancin ‘yan Najeriya sun riga sun san abin da za su yi a babban zaben 2027.
Sanata Kwankwaso ya fadi haka ne sakamakon halin da ake ciki na talauci, yunwa da rashin tsaro.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa Kwankwaso ya yi wannan bayani ne a wajen taron majalisar zartarwa ta ƙasa (NEC) na jam’iyyar NNPP da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis.

Kara karanta wannan
Kwankwaso ya rufe bakin masu yada jita jitar zai koma jam'iyyar APC kafin zaben 2027
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce matsalolin da al’umma ke fuskanta sun nuna cewa jama’a sun gama yanke shawara, inda ya tabbatar da cewa jam’iyyarsu ce ke tare da talakawa.
Kwankwaso ya ce ana yunwa da talauci
Kwankwaso ya nuna damuwarsa kan yadda miliyoyin mutane ke neman abinci amma sun kasa samu saboda tsananin yunwa a ƙasar.
Ya ce wasu al’ummomi ba za su iya zuwa gona ba, wasu kuma ba sa iya zuwa kasuwa saboda tsaro ya tabarbare.
A cewarsa, akwai waɗanda ba su iya zuwa asibiti saboda talauci ya hana su samun kudin magani.
Tsohon Sanatan ya yi nuni da cewa matsalar talauci ta fi muni a Arewacin ƙasar, inda yawancin ƙauyuka ke cikin halin kunci.
'Talakawa sun yi matsaya game da 2027'
Kwankwaso ya bayyana cewa halin da ake ciki ya sa jama’a sun yanke shawarar yadda za su yi a babban zabe mai zuwa.
Ya ce NNPP tana alfahari da kasancewarta tare da talakawa, domin mutane sun gane jam’iyyar ce take tare da su ba tare da rabuwa ba.
“Mutane a ƙasar nan sun gama sanin abin da za su yi a 2027, kuma wannan ne ke ba mu kwarin gwiwa cewa mu ne zaɓin talakawa,”
Inji Kwankwaso.

Source: Twitter
Gargadin Kwankwaso ga 'ya NNPP a Najeriya
Kwankwaso ya yi gargadi ga mambobin jam’iyyarsa da su guji fadawa cikin rikice-rikicen siyasa da maganganun sauya sheƙa ko tattaunawa da wasu jam’iyyun.
Ya ce akwai siyasa ta masu sauya sheƙa marasa tsari waɗanda suke ɗaukar kansu a matsayin masu ilimi, alhali basu da zurfin fahimta.
A cewarsa:
“Wasu suna yawan sauya jam’iyya suna ɗaukan kansu sun fi kowa sani, amma a gaskiya babu ilimi mai zurfi da suke da shi. Idan suna son fahimta, su zo su koya daga gare mu,”
Hadimin Kwankwaso, Saifullahi Hassan ya wallafa a X cewa taron ya samu halartar manyan jam’iyyar NNPP a Najeriya.
Kwankwaso ya gana da Hausawan Legas
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da da Hausawan da aka rusawa kasuwa a jihar Legas.
Rahotanni sun bayyana cewa Kwankwaso ya gana da 'yan kasuwar ne domin duba yadda za su samu mafita.
Shugabannin kasuwar sun bayyana cewa sun tafka asara mai girma ta biliyoyin Naira sakamakon rusau din da aka musu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
