Gwamna Abba Ya Kara Kinkimo Babbar Badakala, Ganduje na Tsaka Mai Wuya a Kano
- Gwamna Abba Kabir ya sake kinkimo aikin bincike kan yadda aka sayar da katafariyar mahautar da Kwankwaso ya gina a Kano
- Abba ya kaddamar da kwamitin mutum 11 domin su bi diddigin yadda tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya cefatar da mahautar
- Tsohon shugaban hukumar yaki da rashawa ta Kano, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ne zai jagoranci kwamitin
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa kwamitin mutane 11 domin binciken yadda aka sayar da katafaren wurin yankar dabbobi watau Abatuwa ta Kano.
Gwamna Abba ya lashi takobin binciko yadda tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya sayar da mahautar, 'Nigerian Meat and Allied Products (NIMAP)'.

Source: Facebook
Daily Trust ta ce katafaren ginin mai darajar miliyoyi Naira da ke yankin Chalawa, an gina shi ne a lokacin mulkin tsohon gwamna, Rabiu Musa Kwankwaso.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tsara wurin ne domin gudanar da ayyuka daban-daban da za su samar da kudaden shiga da kuma damar ayyukan yi ga jama’a.
Gwamna Abba zai kara binciken Ganduje
Yayin kaddamar da kwamitin a ranar Laraba, Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG), Umar Faruq Ibrahim, ya ce wannan bincike ya zama dole domin gano hakikanin abin da ya faru.
SSG, wanda ya wakilci gwamna, ya jaddada cewa gwamnatin Abba ta dauki nauyin kwato duka kadarorin Kano da aka sayar ba bisa ka’ida ba.
Ya bayyana cewa kwamitin binciken zai gudanar da aikinsa ne karkashin jagorancin tsohon shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci ta Jihar, Barista Muhuyi Magaji Rimin-Gado.
Ayyukan da kwamitin binciken zai yi
Gwamnatin Abba ta bukaci kwamitin da ya gudanar da wannan aiki cikin adalci da gaskiya, ba tare da tsoro ko son zuciya ba.
“An umarci kwamitin ya binciki dukkan abubuwan da suka shafi sayar da filin da kayan aiki na mahautar Nigerian Meat and Allied Products (NIMAP) Abattoir.
“Ku duba dukkan takardu, yarjejeniyoyi da amincewa, wadanda suka shafi wannan mu’amala, sannan ku tantance ko an bi dokoki da ka’idoji yadda ya kamata.
“Ana sa ran kwamitin zai gano rawar da mutane, kungiyoyi ko ma’aikatan gwamnati suka taka a cinikin, sannan ya dawo da duk kudaden gwamnati, kadarori ko kayan aiki da aka rasa a wannan tsari."
- Umar Faruq Ibrahim.

Source: Facebook
Muhuyi ya sha alwashin binciko gaskiya
A nasa jawabin, shugaban kwamitin, Rimin-Gado, ya yaba wa gwamnati kan zaben mambobin kwamitin tare da tabbatar da cewa za su gudanar da binciken cikin gaskiya da rikon amana.
Ya kara da cewa za su gudanar da bincike a tsanake ba tare da tsoro ko son zuciya ba, inda ya bayyana cewa za su yi wannan hidima da kulawa sosai, rahoton Daily Post.
Da gaske hadimin gwamna ya karkatar da N6.5bn?
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnatin Kano ta musanta zargin cewa wani hadimin Gwamna Abba ya wawashe ko cire kudi har Naira biliyan 6.5.
Ta bayyana cewa duk wasu kudi da aka fitar a kowace ma'aikata ko ofishin gwamnati, suna kan tsarin dokar kasafin kudin Kano.
Gwamnatin Kano ta kuma sake tunatar da mutane irin barnar da ake zargin tsohuwar gwamnati da ta gabata ta yi kafin ta bar mulki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

