Wadanda Suka Taso Tinubu a Gaba, yayin da Ake Shirin Kifar da Shi a 2027

Wadanda Suka Taso Tinubu a Gaba, yayin da Ake Shirin Kifar da Shi a 2027

FCT, Abuja - An fara tunanin ya za ta kaya tsakanin mai girma Bola Tinubu da 'yan adawa, yayin da ’yan Najeriya ke jiran zuwan babban zaɓen shugaban kasa na 2027,

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

'Yan adawa na ci gaba da shirye-shiryen kifar da shugaban kasa Bola Tinubu ta hanyar dimokuraɗiyya a 2027.

Wasu 'yan siyasa na son kifar da Bola Tinubu a 2027
Hotunan Shugaba Bola Tinubu, Atiku Abubakar da Peter Obi Hoto: @atiku, @PeterObi, @DOlusegun
Source: Facebook

Shirin kifar da Tinubu a 2027

Ƙawancen 'yan adawa na cewa kasar nan na bukatar sauyin jagoranci, inda suke suka mai zafi ga jam'iyyar APC wadda take mulki tun daga 2015.

Mun duba manyan ’yan siyasar Najeriya da ke sa ido kan Tinubu kafin babban zaɓen 2027.

1. Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, wanda ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar PDP a 2023, bai nuna alamar ja da baya daga siyasa ba.

Atiku na da burin zama shugaban kasa
Hoton Atiku Abubakar yana jawabi a wajen wani taro Hoto: Mustapha Sule Lamido
Source: Facebook

Atiku ya nuna goyon bayansa ga hadakar 'yan adawa da ke shirin kifar da Tinubu a 2027.

Kara karanta wannan

2027: APC ta cika baki kan yiwuwar takara tsakanin Jonathan da Shugaba Tinubu

Kwanan nan ya fito ya nuna aniyarsa ta yin takara a 2027, inda ya nuna cewa duk mai kishin kasa zai so ya ceto kasar nan daga hannun Shugaba Tinubu.

2. Seyi Makinde

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, na daga mutanen da ake ganin za su nemi takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar PDP.

Rahotanni masu karo da juna sun rika fitowa game da burin Makinde. Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya ce Makinde ya tabbatar masa ba zai tsaya takara da Bola Tinubu ba.

Jaridar The Punch ta ce Makinde da kansa ya bayyana cewa:

"Ban da wata shakka cewa ina da kwarewar zama shugaban kasa."

3. Peter Obi

Tsohon gwamnan Anambra ya yi takara tare da Atiku a matsayin mataimaki a 2019 lokacin da aka sake zaɓar APC da Shugaba Muhammadu Buhari (Allah ya ji kansa).

A 2023, Peter Obi ya koma jam’iyyar LP inda ya fafata da Atiku na PDP, da kuma wanda ya yi nasara da shugaba Tinubu na APC.

Peter Obi ya kasance daga cikin 'yan siyasar adawa da ke sukar gwamnatin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

2027: Amaechi ya sha sabon alwashi kan takarar shugaban kasa karkashin ADC

4. Rotimi Amaechi

Tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi, ya fito fili ya ce zai iya kayar da APC idan aka ba shi tikitin takarar shugaban kasa na ADC a 2027.

Ya sha alwashin fallasa dabarun APC idan aka ba shi dama, yana mai cewa zai yi amfani da iliminsa game da jam’iyyar don yin nasara 2027.

5. Babachir David Lawal

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Babachir Lawal, ya kasance cikin manyan masu adawa da Tinubu.

Yana taka muhimmiyar rawa a tattaunawar hadakar adawa, tare da tsara dabarun 2027.

6. Bala Mohammed

A watan Agustan 2024, gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana yiwuwar tsayawa takarar shugaban kasa, amma zai janye idan Goodluck Jonathan ya yanke shawarar tsayawa, cewar rahoton The Punch.

Ya ce sukarsa ga gwamnatin Tinubu wani ɓangare ne na rawar da yake takawa domin dawo da Najeriya kan turbar da ta dace.

7. Aminu Tambuwal

Sanata mai wakiltar Sokoto ta Kudu a majalisar dattawa, kuma tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, na cikin hadakar 'yan adawan da ke son kifar da Tinubu.

Kara karanta wannan

"Ya godewa Allah": Tsohon dan takarar shugaban kasa ya ba Tinibu shawara kan 2027

Tambuwal ya soki gwamnatin Tinubu
Hoton Aminu Waziri Tambuwal a zauren majalisar dattawa Hoto: Aminu Waziri Tambuwal
Source: Facebook

Tambuwal kwanan nan ya tara magoya bayansa a jihar Sokoto, inda ya sha alwashin cewa za a kifar da APC a 2027, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Tambuwal ya zargi Shugaba Tinubu da gwamnatin APC da jefa Najeriya cikin matsanancin kuncin tattalin arziki, rashin tsaro da durkushewar siyasa.

“A 2023, mun zagaya faɗin kasar nan muna gargadin ‘yan Najeriya kada su zaɓi Bola Ahmed Tinubu, mutumin da jagorancinsa zai jefa kasar nan cikin abin da na kira (Sharar Bola)."
"Kuma yau, wahala, yunwa da rashin fata da kuke gani a ko ina shaida ce ta abin da muka faɗa."

- Aminu Waziri Tambuwal

An gargadi Tinubu kan sauya Shettima

A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar APC North Central Forum ta ja kunnen Shugaba Bola Tinubu kan sauya Kashim Shettima.

Kungiyar ta bayyana cewa sauya Shettima zai jawo Tinubu ya rasa mafi yawa daga cikin kuri'un 'yan Arewa musulmai a zaben 2027.

Shugaban kungiyar, Saleh Zazzaga, ya ba da tabbacin cewa sauya Kashim Shettima, ba zai sanya wadanda ba su goyawa Tinubu baya ba 2023, su dawo bayansa a zaben 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng