APC Ta Dakatar da Babban Jami'in Gwamnati saboda Aikata Zunubai Masu Girma

APC Ta Dakatar da Babban Jami'in Gwamnati saboda Aikata Zunubai Masu Girma

  • Jam’iyyar APC ta dakatar da tsohon dan takarar majalisar dattawa a Edo, Hon. Valentine Asuen saboda ya aikata zunubai masu girma
  • APC ta ce Valentine Asuen ya aikata ayyukan da suka haddasa rarrabuwar kawuna da gurgunta biyayya a cikin jam’iyyarta
  • APC ta bayyana cewa ta yi amfani da Sashe na 21 na kundin tsarin gudanarwarta wajen dakatar da tsohon dan takarar majalisar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Edo - Jam'iyyar APC reshen Edo ta sanar da dakatar da shugaban hukumar gandun daji ta jihar, Hon. Valentine Asuen, daga jam’iyyar.

APC ta yanke shawarar dakatar da Hon. Valentine Asuen ne bisa zargin rashin ladabi da aikata abubuwan da ke barazana ga haɗin kan jam’iyya.

Jam'iyyar APC ta dakatar da tsohon dan takarar kujerar sanata a Edo
Magoya bayan APC suna daga tutoci a wajen wani gangamin jam'iyyar da aka gudanar a Edo a 2024. Hoto: @OfficialAPCNg
Source: Twitter

APC ta dakatar da jami'in gwamnati daga jam'iyya

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Asuen shi ne ɗan takarar majalisar dattawan Edo ta Kudu a zaben 2024 da ya gabata, kuma tsohon shugaban matasan APC a jihar.

Kara karanta wannan

PDP ta samu koma baya, tsohon sanatan Kebbi ya fice daga jam'iyyar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dakatar da tsohon dan takarar majalisar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar a jihar, Barr. Peter Uwadiae-Igbinigie, ya sanya wa hannu.

A cikin sanarwar, APC ta ce ta ɗauki wannan mataki ne bayan la’akari da halayen Asuen da jam’iyyar ta ce sun saɓa wa kundin tsarin mulkinta.

APC ta zargi Asuen da shiga cikin ayyukan da ke haddasa rarrabuwar kai da kuma gurgunta tsarin biyayya da ake tsammani daga 'ya'yan jam’iyyar.

Zunuban da jami'in gwamnatin ya aika a APC

Sanarwar ta bayyana cewa dakatarwar ta yi daidai da sashe na 21 na kundin tsarin mulkin APC (2022 da aka yi wa gyara), wanda ya tanadi matakan ladabtarwa kan laifuffukan mambobi.

APC ta ƙara da cewa irin waɗannan halaye da aka danganta da Asuen suna jawo rarrabuwar kawuna, wanda ya cancanci dakatarwa, bisa tanadin doka.

Jaridar Leadership ta rahoto sanarwar da Uwadiae-Igbinigie ya fitar ta ce:

Kara karanta wannan

"Rashin tausayi" ADC ta caccaki gwamnonin PDP, ta fadi kuskuren da suka yi

“An ɗauki wannan matakin ladabtarwa ne bisa ga halayensa da suka saba wa haɗin kai, biyayya da cigaban jam'iyya, kuma sun saba da kundin tsarin mulki.
"Ayyukansa sun zama masu haddasa rarrabuwar kai a cikin jam’iyya, wanda hakan ke raunana haɗin kai da ladabi da ake tsammani daga kowane mamba."
APC ta ce Hon. Valentine Asuen ya aikata laifuffukan da suka cancanci a dakatar da shi
Tsohon dan takarar kujerar sanata a Edo, Hon. Valentine Asuen (a tsakiya) yana magana da shugabannin matasa. Hoto: @Gen_Buhar
Source: Twitter

Dokokin ladabtar da mambobin APC

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

“Bisa ga tanadin Sashe na 21:2 (ii) da (v) na kundin tsarin mulki na 2022 da aka yi wa gyara, irin wannan hali ya yi dai dai da take hakkokin da suka rataya kan mamba.
"Haka kuma, kamar yadda aka fayyace a cikin Sashe na 21:5 (a), (c), (d), (e), (f) da (h), waɗannan laifuffuka na iya jawo hukunci, ciki har da dakatarwa.”

APC ta jihar Edo ta kuma jaddada aniyar ta na tabbatar da ladabi da dimokuraɗiyya a cikin gida, tana mai gargadin cewa ba za ta lamunci duk wani abu da zai iya haifar da rikici ko rashin jituwa tsakanin mambobi ba.

An dakatar da Sanata mai-ci daga APC

A wani labarin, mun ruwaito cewa, APC ta dakatar da tsohon gwamnan jihar Ogun, Sanata Gbenga Daniel da wani dan siyasa, Hon. Kunle Folarin.

Kara karanta wannan

'Ka dawo gida da gaggawa: An buƙaci Tinubu ya sanya dokar ta ɓaci a jihohin Arewa 2

An dakatar da 'yan siyasar biyu ne bayan kin amsa gayyatar kwamitocin ladabtarwa da ke bincikarsu kan zargin cin amanar jam'iyya.

APC ta ce Sanata Daniel da Hon. Folarin sun nuna rashin da'a kuma sun yi yunkurin tursasa wa 'yan kwamitin janye bincike a kansu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com