'APC Ƙungiyar Asiri ce,' Ƙusa a PDP Ya Jero Manyan Matsalolin Jam'iyya Mai Mulki

'APC Ƙungiyar Asiri ce,' Ƙusa a PDP Ya Jero Manyan Matsalolin Jam'iyya Mai Mulki

  • Dakta Gbenga Olawepo-Hashim ya zargi jam’iyyar APC da rashin akida, inda ya ce tsarin ta ya fi kama da na mulkin kama-karya
  • Ya bayyana cewa APC ta jawo durkushewar tattalin arzikin Najeriya daga $570bn zuwa $300bn tare da karuwar matsalar tsaro
  • Hashim ya dage cewa PDP ce sahihiyar jam’iyyar dimokuraɗiyya, ya na mai neman ‘yan Najeriya su kawo sauyi a zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Dakta Gbenga Olawepo-Hashim, ya yi magana kan halin da Najeriya take ciki.

Dakta Olawepo-Hashim ya bayyana cewa jam’iyyar APC mai mulki ba ta da akida, riko da dimokuraɗiyya, ko kuma hangen nesa mai ma’ana.

Tsohon dan takarar shugaban kasa, Dakta Gbenga Hashim ya ce APC na mulki a tsarin kama karya
Hoton magoya bayan APC a taron yakin neman zaben jam'iyyar a Imo, da Dakta Gbenga Olawepo-Hashim. Hoto: @GoziconC, @GbengaOH
Source: Twitter

"Mutum 1 ko 2 ke juya APC" - Jigon PDP

Kara karanta wannan

'Ka dawo gida da gaggawa: An buƙaci Tinubu ya sanya dokar ta ɓaci a jihohin Arewa 2

Ya bayyana haka ne a cikin shirin gidan talabijin na AIT mai taken 'Ranar Dimokuradiyya,' sannan ya fadi hakan a taron manema labari a Abuja a ƙarshen mako.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hashim ya yi zargin cewa tsarin shugabanci na APC ya fi kama da mulkin kama-karya fiye da jam'iyya mai riko da dimokuraɗiyya.

“Mutum ɗaya ko biyu ne kawai ke juya akalar APC, sauran sun zama 'yan amshin shata ne kawai. Wannan ba jam’iyya ba ce; kungiyar asiri ce."

- Dakta Olawepo-Hashim.

Kusa a PDP ya caccaki gwamnatin APC

Ya kuma zargi jam’iyyar APC da jagorantar Najeriya cikin matsanancin halin durƙushewar tattalin arziki da ƙaruwar matsalar tsaro a ƙasar.

A cewarsa:

“Sun yi alƙawarin samar da canji, kuma sun kawo canjin – ta hanyar durkusar da GDP na Najeriya daga $570bn a 2014 zuwa ƙasa da $300bn a 2025.
“Suka rushe GDP-p.c daga sama da $3,000 zuwa ƙasa da $1,000. Haka kuma suka faɗaɗa rashin tsaro daga Arewa maso Gabas zuwa Arewa maso Yamma, Arewa ta Tsakiya da Kudu maso Gabas."
Gbenga Olawepo-Hashim ya ce jam'iyyar PDP ce kawai ke riko da dimokuradiyya a Najeriya.
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Gbenga Olawepo-Hashim tare da shugaban PDP, Umar Damagum a ofishin jam'iyyar a Abuja. Hoto: @GbengaOH
Source: Twitter

"PDP ce jam’iyyar dimokuraɗiyya" - Hashim

Kara karanta wannan

'Karshen APC ya zo,' Gwamnonin PDP sun faɗi abin zai hana jam'iyya mai mulki sake cin zaɓe

Dakta Hashim ya dage cewa PDP ce “gaskiyar jam’iyyar dimokuraɗiyya” a Najeriya, wadda ke tafiya bisa ra’ayoyi mutane daban-daban ba wai tsiraru ba, inji rahoton The Guardian.

Ya kawo misali, cewa kwanan nan a Zamfara, gwamnonin PDP suka nuna goyon baya ga shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Umar Damagum, wanda ya nuna hadin kai da tsarin dimokuradiyya na PDP.

Hashim ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su riƙa neman mafi ingancin tsarin jam’iyya yayin da zaɓen 2027 ke ƙaratowa, yana mai gargadi cewa mulki ba tare da akida ko tsarin lissafi ba ba zai iya kawo ci gaba ba.

Ya jaddada cewa ya kamata jam’iyyun siyasa su zarce dandalin neman nasara a lokacin zaɓe, su zama dandalin samar da shugabanci na-gari don cigaban ƙasa.

Gbenga Olawepo-Hashim ya koma PDP

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Dakta Gbenga Olawepo-Hashim, wanda ya yi takarar shugaban ƙasa a 2019, ya koma jam'iyyar PDP.

Hashim ya gana da ƴan kwamitin gudanarwa na PDP ta ƙasa (NWC) a hedkwatar jam'iyyar da ke Abuja ranar Laraba, 23 ga watan Yuli, 2025.

Ya ce duk da ƙalubalen da PDP ke fuskanta da yadda manyan jiga-jigai ke ficewa daga cikinta, har yanzu jam'iyyar ce kaɗai za ta iya ceto Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com