2023: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya koma APC a hukumance, ya gana da shugaban jam'iyyar a Abuja

2023: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya koma APC a hukumance, ya gana da shugaban jam'iyyar a Abuja

  • Tsohon dan takarar shugaban kasa, Olawepo-Hashim ya gana da shugaban riko na jam'iyyar APC, Gwamna Buni, bayan sauya sheka zuwa jam'iyyar mai mulki
  • A taron da aka yi a Abuja, Olawepo-Hashim ya yaba da salon shugabancin Buni tare da rokon 'yan siyasar Najeriya da su guji amfani da tunanin kabilanci don ingiza ajandar su
  • Gwamna Buni ya jinjina wa sabon jigon na APC tare da ba shi tabbacin za a yi masa duk abun da aka yi wa mambobin jam'iyyar

FCT, Abuja - Gbenga Olawepo-Hashim, tsohon dan takarar shugaban kasa, ya koma jam'iyyar All Progressive Congress (APC) mai mulki gabanin zaben 2023.

Olawepo-Hashim a ranar Alhamis, 7 ga watan Oktoba, ya gana da Mai Mala Buni, shugaban kwamitin riko na APC kuma gwamnan jihar Yobe a gidan sa dake Abuja.

Read also

Ya kamata 'yan Najeriya su fahimci ilimin Buhari don gane tasirinsa, Minista

2023: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya koma APC a hukumance, ya gana da shugaban jam'iyyar a Abuja
2023: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya koma APC a hukumance, ya gana da shugaban jam'iyyar a Abuja Hoto: Gbenga Olawepo-Hashim's media office
Source: UGC

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, 8 ga watan Oktoba, ta ofishin yada labaransa, jigon na APC ya bukaci shugabannin da aka zaba a dandamalin jam’iyyar da su guji amfani da dandamali na kabilanci don isar da damuwarsu kan lamuran siyasa.

Ya kuma shawarci shugabannin siyasa da su yi amfani da na’urorin cikin gida na jam’iyya don hura ra’ayoyinsu da warware sabanin da ke tsakaninsu maimakon komawa ga taron kabilanci da na addini don rura wutar sha’awa da rarrabuwa.

Olawepo-Hashim ya tuna cewa bai taba zama al'ada a siyasar kasar ba cewa shugabanni su tattara kansu a matsayin shugabannin kudu ko na arewa.

A cewarsa, shugabannin Jamhuriya ta biyu sun yi magana a matsayin UPN ko NPN, PRP ko NPP, GNPP ko NAP.

Read also

Da duminsa: 'Yan daba sun yi wa babban jami'in APC duka har ya gigice, sun kona gidansa a jihar Nasarawa

Olawepo-Hashim ya kuma yabawa Gwamna Buni kan kokarin da yake yi na fadada tushen membobin jam'iyyar.

A martaninsa, Gwamna Buni ya gode wa Olawepo-Hashim da tawagar yana mai cewa jam'iyyar na farin cikin jawo hankalin babban shugaba kamarsa.

Ya ce:

"Kai ba sabon fuska bane a gare mu, muna girmama ka ƙwarai. Kada ka ɗauki kanka a matsayin sabon shiga cikin APC, daidai kake da duk wanda ya shigo APC tun daga ranar farko."

2023: Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Moghalu ya fice daga jam'iyyar YPP ya koma sabuwar jam'iyya

A gefe guda, mun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Young Progressive Party (YPP), Kingsley Moghalu ya koma jam'iyyar Action Democratic Congress (ADC) gabanin babban zaben 2023.

Kingsley Moghalu ya bayyana hakan ne a shafinsa na dandalin sada zumunta ta Facebook a ranar Juma'a inda ya rubuta cewa, "An kammala komai a hukumance."

Read also

Bincike: Jerin gwamnonin Najeriya 5 da suka fi yin kokari

Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Nigeria, CBN, ya kuma wallafa wata sabuwar fosta dauke da hotonsa da tambarin sabuwar jam'iyyarsa.

Source: Legit

Online view pixel