'Karshen APC Ya Zo,' Gwamnonin PDP Sun Faɗi Abin zai Hana Jam'iyya Mai Mulki Sake Cin Zaɓe
- Gwamnonin PDP sun ce APC ta gaza, wannan ya sa na dole a fitar da ita daga fadar shugaban kasa
- Gwamnonin sun kara da zargin gwamnati da tumurmushe dimokuraɗiyyar da jefa ƙasa cikin tsadar rayuwa
- Sun ce PDP ce kawai za ta dawo da kyakkyawan mulki da tsaro da ƴan kasa su ka fada a karkarshin APC
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Zamfara – Gwamnonin jam’iyyar PDP sun bayyana cewa ‘yan Najeriya za su yi watsi da jam’iyyar APC a zaɓen 2027.
Sun bayyana cewa da a dauki matakin ne saboda manufofin gwamnatin Bola Tinubu da suka jefa ƙasa cikin wahala.

Source: Twitter
The Cable ta wallafa cewa gwamnonin sun faɗi haka ne ta cikin sanarwar Bayan taro da suka gudanar a Gusau, babban birnin Zamfara, a ranar Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'PDP ce mafitar Najeriya,' inji gwamnoninta
Jaridar Vanguard ta ruwaito gwamnonin, PDP sun ce jam'iyyarsu ta jajirce wajen ceto Najeriya daga tsarin mulkin da suka kira na rarrabuwar kawuna da kuncin rayuwa da APC ke haifarwa.
Duk da sauye-sauyen da aka samu daga PDP zuwa wasu jam’iyyu, gwamnonin sun ce jam’iyyar tana ci gaba da jawo hankalin jama’a.
A zaman, sun tattauna halin da ƙasa ke ciki, matsalolin tsaro, da kuma lalacewar dimokiraɗiyya tare da shirin ƙarfafa jam’iyya kafin babban taron ƙasa na PDP da ke tafe a watan Nuwamba.
Dangane da tsaro, sun yi Allah wadai da kisan gilla a jihohin Katsina, Filato, Neja, Binuwai da sauran sassan ƙasa, inda suka nemi gwamnatin tarayya ta fi mayar da hankali kan kare rayukan jama’a.
Gwamnonin PDP sun zargi APC da lalata dimokuraɗiyya
Gwamnonin sun yaba wa magoya bayan jam’iyyar bisa jajircewarsu duk da barazana da danniya da suke ce suna fuskanta daga gwamnatin APC.
Sun zargi gwamnatin tarayya da jawo sojoji a cikin zaɓen cike gurbi a jihohi, lamarin da ya haifar da tafka maguɗi, sayen ƙuri’u da tashin hankali.
A cikin sanarwar, sun jaddada cewa PDP ba za ta raunana ba saboda ficewar wasu, domin tana da karɓuwa a ƙasa baki ɗaya.

Source: Original
Sun kuma yi kira ga ƴaƴanta da magoya baya su tsaya tsayin daka kan akidar PDP duk da tsangwamar gwamnati.
Sun tabbatar wa masu goyon bayansu da babban taron jam’iyyar na Nuwamba tare da gargadin kada a bari wasu su kawo tangarda.
Gwamnonin sun ce PDP ita ce:
"Jam’iyyar dimokiraɗiyya kuma zabin da zai dawo da Najeriya kan hanyar ci gaba da kyakkyawan mulki.”
A cikin waɗanda suka halarci taron akwai Bala Mohammed (Bauchi), Dauda Lawal (Zamfara), Agbu Kefas (Taraba), Ahmadu Fintiri (Adamawa), Seyi Makinde (Oyo), Douye Diri (Bayelsa), da Ademola Adeleke (Osun).
PDP ta koka da zaɓen Zamfara
A baya, mun wallafa cewa jam'iyyar adawa ta PDP ta zargi APC da sojoji da ‘yan bindiga da kawo magudi a zaben cike gurbi a Kaura Namoda, Zamfara.
Shugaban PDP na jihar, Jibo Magayaki Jamilu, ya bayyana wa manema labarai a Gusau cewa an yi ƙoƙarin hana wakilan PDP shiga rumfunan zaɓe.
Haka kuma, ya ce a wasu mazabu, ba a gudanar da zaɓe ba kwata-kwata saboda barazana da ɗaukar ƴan ta'adda da sojoji domin su kankane komai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


