Kada Mage ba Yanka ba, Gwamna Makinde Ya Fadi Shirin PDP na Karbar Mulki a 2027
- Gwamna Seyi Makinde, ya tabbatar da cewa jam’iyyar PDP tana nan da ƙarfinta, kuma za ta share hawayen ‘yan Najeriya a 2027
- Makinde ya bayyana haka ne bayan taron rabon mukaman PDP na yankin Kudu a Legas, inda aka haɗa manyan jiga-jigan jam’iyyar
- Gwamnan jihar na Oyo ya ce mahalarta taron sun yanke muhimmiyar matsaya ta haɗa kai domin karɓar mulki daga APC a 2027
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ba ta mutu ba, tana nan daram, kuma ja da baya ba tsoro ba ne.
Seyi Makinde ya ce jam'iyyar PDP ce za ta zamo zabin 'yan Najeriya a 2027, kuma za ta dawo da martabar kasar da aka rasa a mulkin APC.

Source: Twitter
PDP ta yi taron rabon mukamai a Legas
Gwamnan ya bugi kirjin ne a lokacin zantawarsa da manema labarai a Legas bayan kammala taron rabon mukaman PDP a yankin Kudu a ranar Alhamis, inji rahoton Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Makinde ya ce an gudanar da taron ne domin haɗa kan dukkanin masu ruwa da tsaki da sauran ɓangarori na jam’iyyar gabanin manyan zaɓuka masu zuwa.
Tare da sauran shugabannin jam’iyyar, Makinde ya jaddada cewa ba a shirya taron don bata ran wani ba, illa ma ƙarfafa dimokuraɗiyyar cikin gida da kuma shirya PDP don karbar mulki a 2027.
Taron ya haɗa fitattun jiga-jigan jam’iyyar da suka haɗa da gwamnan Bayelsa Douye Diri, tsohon gwamnan Akwa Ibom Emmanuel Udom, tsohon gwamnan Osun Olagunsoye Oyinlola, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Ben Obi, Chief Olabode George, da mambobin kwamitin BoT.
"PDP za ta zama zabin Najeriya" - Makinde
Da yake magana bayan kammala taron, Gwamna Seyi Makinde ya cewa PDP ba za ta kara bata lokacinta kan masu kokarin kawo rarrabuwar kawuna a cikin jam'iyyar ba.

Kara karanta wannan
Yana shirin kawo wa hadakar adawa tarnaki, ADC ta fatattaki jam'iyyar 'shugabanta'
Makinde ya ce an shirya taron don yin shawara, kuma mahalarta taron sun yanke muhimmiyar matsaya ta mayar da PDP kan turbar da ta dace a Najeriya.
“Mun kammala taron shawarwari na kwamitin rabon mukamai na PDP a Kudu, lallai dimokuraɗiyya ita ce ke ba kowa damar ya faɗi albarkacin bakinsa, kuma an dauki shawarar wadanda suka fi rinjaye. Wannan shi ne dimokuraɗiyya.
“Me muke ƙoƙarin yi? Muna ƙoƙarin haɗa kan dukkanin masu ruwa da tsaki da ɓangarori daban-daban na PDP wuri guda, don mu zama zabin ‘yan Najeriya a 2027."
- Gwamna Seyi Makinde.

Source: Facebook
"PDP ba ta mutu ba" inji Gwamna Makinde
Jaridar ThisDay ta rahoto Gwamna Makinde ya kara da cewa:
"Masu yada cewa PDP ta mutu sun yi karya, PDP ta ba ta mutu ba, tana nan da ranta kuma da karfinta, don kada mage ba yanka ba ne.
"Ko a wannan taron da aka yi za ku san PDP na nan da karfinta, kun dai ga irin manyan mutanen da suka halarta, akwai gwamnoni masu ci, tsoffin gwamnoni, shugabanni da dattawa, tsohon shugaban majalisar dattawa, shugaban BoT."

Kara karanta wannan
"Kan mage ya waye": Jam'iyyar PDP ta kada hantar APC, ta fadi abin da zai faru a 2027
Makinde ya ce dukkanin dukkanin jiga-jigan sun cimma matsaya ta yin aiki tare don dawo da martabar PDP da kuma sake karbar shugabanci a Najeriya.
Shugaban PDP na farko ya mutu a Edo
A wani labarin, mun ruwaito cewa, jam'iyyar PDP a jihar Edo ta rasa daya daga cikin mutanen da suka taba jagorantarta, bayan ya koma ga Mahaliccinsa.
Mukaddashin PDP na Edo, Anthony Aziegbemi, ya sanar da rasuwar wanda ya fara shugabantar jama'iyyar a jihar, Solomon Aguele.
Ya bayyana marigayi Solomon Aguele a matsayin wanda za a rika tunawa da shi saboda irn gudunmawar da ya ba da wajen ci gaban PDP da jihar Edo.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
