Sanata Wadada Ya Fice daga Jam'iyyar SDP, Ya Hango Makomar Tinubu a Zaben 2027
- Sanata Ahmed Wadada ya sanar da ficewarsa daga SDP, inda ya danganta hakan da rikicin cikin gida da ya yi katutu a jam'iyyar
- Wadada ya nuna godiya kan gogewa da zumuncin da ya samu a SDP, amma ya ce lokaci ya yi da zai gwada sababbin dabarun siyasa
- Wannan na zuwa ne yayin da ya yi watsi da ikirarin ADC kan tazarcen Shugaba Bola Tinubu, inda ya nuna yiwuwar ya koma APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Sanata mai wakiltar mazabar Nasarawa ta Yamma, Ahmed Wadada, ya sanar da murabus dinsa daga mamban jam’iyyar SDP.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa da aka aikawa shugaban jam’iyyar SDP na gundumar Tudun a ƙaramar hukumar Keffi, jihar Nasarawa.

Source: Facebook
Sanata Wadada ya fice daga SDP
Wasiƙar da hukumar dillacin labarai na kasa (NAN) ta gani a ranar Alhamis na dauke da taken:: “Sanarwar murabus daga jam’iyyar SDP.”
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wasiƙar, Sanata Wadada ya rubuta cewa:
“Na rubuta wannan wasikar domin sanar da ku shawarar da na yanke ta yin murabus daga zama ɗan jam’iyyar SDP, daga yau.
“Na yanke wannan shawarar ne bayan da na fahimci cewa rikicin cikin gida da ya daɗe yana addabar jam’iyyar ba zai kare ba.
“Kamar yadda kuka sani, waɗannan rikice-rikice sun jawo rarrabuwar kai sosai da kuma shari’o’i a cikin jam’iyyar.
Sanata Wadada zai nemi wata jam'iyyar
Sanata Wadada ya mika godiyarsa ga jam'iyyar SDP, yana mai cewa:
“Na gode da damar da aka bani a lokacin da nake ɗan jam’iyyar SDP, kuma ina matuƙar godiya da irin zumuncin da aka kulla.
“Amma yanzu lokaci ya yi da zan matsa gaba domin gwada wasu sababbin hanyoyi da za su taimaki siyasa ta."
Wannan lamari ya faru ne a daidai lokacin da Wadada ya fito da bayanai na goyon baya ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Source: Facebook
Sanata Wadada ya kalubalanci ADC
Bayan wata ziyarar da ya kai fadar shugaban ƙasa, sanatan ya yi watsi da ikirarin cewa jam'iyyar ADC za ta iya samar da shugaba da zai zarce nasarorin da Tinubu ya samu.
“ADC ta ƙunshi ‘yan Najeriya da muke girmamawa, amma ku dubi kowanne daga cikinsu — wa zai iya yin abin da ya fi abin da gwamnatin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ke yi? Ku gaya mini, ban ga kowa ba.”
- Sanata Ahmed Wadada.
Wadada ya kuma yi nuni da yiwuwar dawowa jam’iyyar APC, inda ya tuna cewa ya taɓa zama babban jami’in PDP a ƙasa kafin daga bisani ya shiga APC sannan daga baya ya shiga SDP.
Ya jaddada cewa bai bar jam’iyyar SDP saboda wata ƙiyayya ba, illa kawai “yanayin rayuwa da ke sanya dole a canja salo na tafiyar da wakilcin jama'a.”
'Tinubu zai koma Aso Rock Villa' - Wadada
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sanata Ahmed Wadada ya yi ikirarin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne zai lashe zaben 2027.
Sanata Wadada ya ce Tinubu zai yi nasara ne saboda ayyukan da ya shimfida a kasa, musamman aikin titin Sokoto–Badagry, hanyar Abuja–Kano.
'Dan majalisar dattawan da ke wakiltar Nasarawa ta Yamma ya jaddada ce tuni aka mamaye fadar shugaban kasa a 2027, kuma Tinubu ne ya zauna daram a ofis
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


