Jerin Sunayen 'Ya'yan Manya da Bola Tinubu Ya Bai Wa Mukamai Masu Gwabi a Najeriya
Abuja - Tun bayan rantsar da shi a ranar 29 ga Mayu, 2023, shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nada 'ya'yan manyan mutane a Najeriya a mukamai daban-daban.
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ana ganin Tinubu ya yi haka ne da nufin kafa gwamnatin hadin kan kasa, sai dai duk da haka wasu 'yan siyasa na ganin ya yi watsi da su ta bangaren nadin mukamai.

Source: Facebook
A kokarinsa na girmama tsofaffin abokan gwagwarmaya, Shugaba Bola Tinubu ya bai wa ’ya’yan tsoffin manyan mutane mukamai a gwamnatinsa, rahoton Bussiness Day.
Rikicin Marigayi MKO Abiola da Janar IBB
Daga cikin manyan da 'ya'yansu suka shiga gwamnatin Tinubu akwai marigayi Chief MKO Abiola da kuma tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB).
MKO Abiola shi ne wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 12 ga Yuni, 1993, wanda har yanzu ake ɗauka a matsayin mafi sahihanci a tarihin Najeriya.
Amma Janar Babangida mai ritaya ya soke zaɓen, lamarin da ya jawo suka daga ciki da wajen ƙasa.
IBB ya amince ya yi kuskure a zaben Abiola
A baya-bayan nan, a wajen ƙaddamar da wani littafinsa, Babangida ya amince da cewa Abiola ne ya lashe zaɓen amma ya soke shi ne saboda maslaha.
Hakan ya biyo bayan matakin tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari, wanda ya ayyana Abiola a matsayin wanda ya ci zaben 1993 tare da ba shi lambar girmamawa ta GCFR.
Tinubu, wanda ya kasance cikin masu fafutukar tabbatar da sakamakon zaɓen 1993, ya halarci ƙaddamar da littafin Babangida, daga bisani kuma ya bai wa ɗansa mukami.
Haka nan kuma, Shugaba Tinubu ya bai wa ’ya’yan Abiola biyu mukamai a gwamnatinsa.
'Ya'yan tsofaffin shugabanni da Tinubu ya ba mukami
A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro muku duka 'ya'yan manya da aka bai wa mukamai daban-daban a gwamnatin Bola Tinubu.
1. Rinsola Abiola
Kwanan nan, Shugaba Tinubu, ya daga matsayin Rinsola Abiola, ’yar marigayi MKO Abiola, daga mataimakiya ta musamman zuwa shugabar cibiyar CLTC.
Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Rinsola Abiola a matsayin Darakta Janar (DG) ta Cibiyar Horar da yan Ƙasa (CLTC).

Source: Twitter
Bayo Onanuga, mai ba wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, ne ya bayyana wannan naɗi a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X.
Sanarwar ta ce:
“Mis Abiola ƙwararriya ce a fannin sadarwa da dabarun mulki, kuma ta taɓa yin aiki a matsayin mai taimaka wa shugaban kasa ta musamman.”
2. Jamiu Abiola
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Jamiu Abiola a matsayin babban mai taimaka masa na musamman kan harsuna da harkokin ƙasashen waje.
Jamiu, ɗan marigayi Moshood Abiola, wanda ya lashe zaɓen 1993 da aka soke, ya taɓa yin aiki a matsayin mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan manyan ayyuka a ofishin mataimakin shugaban ƙasa.

Source: Twitter
Sanarwar ta fito ne daga bakin Segun Imohiosen, daraktan yada labarai da hulɗar jama’a a ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya.
A cewar sanarwar, nadin dan Abiola ya fara aiki ne daga ranar 14 ga Nuwamba, 2024, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa ta ragargaji Atiku, El Rufa'i kan wata nasarar da Tinubu ya samu
“Shugaba Tinubu ya amince da nadin Jamiu Abiola a matsayin bbban mai taimaka masa na musamman kan harsuna da harkokin kasashen waje. Wannan nadin ya fara aiki daga ranar 14 ga Nuwamba, 2024.”
3. Mohammed Babangida
A watan Yuli da ya gabata, shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nada Mohammed Babangida, ɗan tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida.
Shugaba Tinubu ya sanar da nadin wannan matashi a matsayin shugaban Bankin Harkokin Noma (BoA) da aka yi wa garambawul.
Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru, Babyo Onanuga, shi ne ya bayyana hakan sanarwa da ya wallafa a X a ranar Juma’a, 18 ga Yuli, 2025.
Mohammed Babangida ya nuna godiyarsa ga shugaban kasa bisa wannan dama da aka ba shi.

Source: Twitter
Nadin Mohammed IBB ya zo da rudani lokacin da aka fara yada jita-jitar cewa ba zai karbi mukamin ba, amma daga bisani ya fito ya karyata labarin, cewar rahoton NTA.
Dan tsohon shugaban kasar ya tabbatar da cewa ya karbi mukamin hannu bibbiyu, kuma zai ba da gudummuwarsa daidai gwargwado wajen ci gaban Najeriya.
4. Muhammad Abu Ibrahim
Shugaban Bola Tinubu ya amince da nadin Muhammad Abu Ibrahim, ɗan sanata Abu Ibrahim, a matsayin shugaban asusun bunkasa harkokin noma (NADF).
Hakan na kunshe a wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar, ta ce nadin ya fara aiki nan take daga ranar Alhamis, 19 ga Oktoba, 2023, The Nation ta rahoto.
Tinubu yana sa ran sabon jagoran zai kawar da duk wani cikas da ke hana manoma samun tallafin kudi, musamman ma waɗanda za su taimaka wajen samar da abinci.
5. Umar Abdullahi Ganduje
A wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis, 8 ga Maris, 2024, fadar ahugaban kasa ta ce Shugaba ya nada Umar Abdullahi Ganduje, dan tsohon shugaban APC a matsayin ahugaban hukumar kula da wutar lantarki (REA).
Wannan naɗin ya biyo bayan dakatar da Ahmad Salihijo Ahmad, tsohon MD/CEO na REA, da wasu daraktoci guda uku saboda zargin almundahana na sama da N1.2 biliyan, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan
IBB: Bayan cika shekara 84, Janar Babangida ya aika muhimmin sako ha 'yan Najeriya
An bayyana cewa Tinubu ya naɗa ɗan Ganduje, tsohon gwamnan Kano ne a matsayin wani nau'in lada ko sakayya ta siyasa ga mahaifinsa.
6. Asiya Abdullahi Umar Ganduje
Diyar Ganduje, Asiya Abdullahi Ganduje na daya daga cikin wadanda Shugaba Tinubu ya nada a sabuwar hukumar raya yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
Hakan na kunshe ne a wata wasika da Shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Senator Barau I. Jibrin, suka sanya rattaba wa hannu.
Waikar mai dauke da sunayen mutane 11 da aka nada a hukumar, an tura ta zuwa ofishin shugaban kasa domin amincewa.
A cikin sunayen, an nada Asiya Abdullahi Umar Ganduje, 'yar Ganduje, a matsayin Daraktar Harkokin Jama'a da Raya Karkara, In ji Sahara Reporters.
7. Ummasalma Isiyaka Rabiu
Shugaba Bola Tinubu ya nada Ummasalma Isiyaku Rabiu, yar gidan Sheikh Isiyaka Rabiu a matsayin kwamishina a hukumar FCCPC ta kasa.
Hakan na cikin wata sanarwa da hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba 13 ga watan Agustan, 2025.
Ummusalma, mai shekaru 35 daga jihar Kano, ita ce ta kafa Gidauniyar Usir, ƙungiyar taimako da ke tallafa wa talakawa da al’ummomi.
8. Muhammad Mahdi Aliyu Wamakko
Dan tsohon gwamnan Sakkwato, Sanata Aliyu Wamakko na daya daga cikin wadanda aka nada a hukumar raya Arewa maso Yamma tare da diyar Ganduje.
An nada Muhammad Mahdi Aliyu Wamakko a matsayin Daraktan Sashen Tsare-tsare, Bincike, Kididdiga da Tattara Bayanai a sabuwar hukumar.
Rahoton Premium Times ya nuna cewa nadin na cikin takardar da Majalisar Tarayya ta mikawa Shugaba Tinubu dauke da sa hannun Tajudeen Abbas da Barau Jibrin.
Shugaba Tinubu ya ba kanwar Abdussamad BUA mukami
A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya nada Louis Odion da Ummusalma Isiyaka Rabiu a matsayin kwamishinonin hukumar FCCPC.
Ya nada Louis Odion a matsayin kwamishina mai kula da harkokin gudanarwa, da Ummusalma Isiyaku Rabiu a matsayin kwamishinar ayyuka.
Ummusalma, mai shekaru 35 daga jihar Kano , ita ce ta kafa Gidauniyar Usir, ƙungiyar taimako da ke tallafa wa talakawa da al’ummomi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



