Kashim: Wike Ya Fallasa Dalilin da Ya Sa Babachir Lawan ke Sukar Bola Tinubu
- Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, Nyesom Wike ya bayyana dalilin da ya sa tsohon Sakataren Gwamnati, Babachir Lawal ke adawa da Bola Tinubu
- Ya ce suka da Babachir ke yi a kan gwamnatin APC da shi kan shi Shugaban Kasa na da nasaba da rashin nasarar zama mataimakin Tinubu a 2023
- Da ya waiwaya kan gamayyar 'yan adawa ta ADC, Wike ya ce zaben cike gurbin da aka yi a ranar Asabar ya tabbatar da cewa ba su da katabus
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Babachir Lawal, na cike da haushin Shugaban Kasa tun a 2023.
Wike ya bayyana cewa lamarin ya samo asali ne bayan Kashim Shettima ya yi nasarar zamam abokin takarar Tinubu a maimakon a Babachir da ya sa rai.

Source: Twitter
A wata hira da aka yi da shi a Channels TV a ranar Talata, Wike ya ce Babachir ya ziyarce shi a gidansa da ke Fatakwal jim kaɗan bayan Tinubu ya sanar da Kashim a matsayin abokin takararsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wike: 'Babachir na cike da haushi'
Tribune Online ta wallafa cewa Wike ya yi bayanin cewa fushin da Babachir ke nunawa ga shugaba Tinubu bai da alaƙa da ci gaban ƙasa, sai dai rashin cimma burin siyasa da ya yi masa ciwo.
Ya ce:
“Babachir ba wanda za a ɗauka da muhimmanci ba ne. Mutumin da ya fito a talabijin ba domin ya yi suka bisa gaskiya kan abin da shugaban ya yi ba, sai dai don ya taɓa samun kusanci da shugaban ƙasa, yanzu kuma yana cewa Tinubu ya fiya girman kai."
Mista Wike ya ce har yanzu, Babachir ya gaza manta wa da rashin nasarar takara tare da Tinubu, wanda zai ba shi damar zama mataimakin Shugaban Kasa,
Wike ya yi watsi da gamayyar adawa ta ADC
Wike ya kuma yi tsokaci kan sabuwar gamayyar adawa da ta ɗauki jam’iyyar ADC a matsayin dandamalin fatattakar gwamnatin Tinubu daga mulki.
Ya bayyana gamayyar a matsayin “ba komai ba,” yana mai cewa ƙuri’un zabubbukan cike da aka kammala kwanan nan sun nuna yadda al’umma suka riga suka yi watsi da su.

Source: Twitter
A kalaman Wike:
“Babu wata gamayya. ‘Yan Najeriya sun riga sun ƙi su; sakamakon zaɓen cike gurbi hujja ce. Ba su da tasiri.”
Ministan Abuja ya ƙara da cewa bai kamata a zargi gwamnatin Tinubu da gazawa ba saboda sabuwa ce mai shekaru biyu kacal.
Ya ce ba za a iya warware matsalolin da suka daɗe a cikin ƙasar nan a cikin dare ɗaya ba, yana mai roƙon al’umma da su ba wa gwamnati lokaci.
Jam'iyyar PDP ta ja layi da Wike layi
A baya, mun ruwaito cewa jam’iyyar PDP ta bayyana cewa babu wani ɗan siyasa, kama daga ciki ko wajen jam’iyyar da zai iya saka mata sharadi kafin a samu kanta a Najeriya.

Kara karanta wannan
"Ka ajiye Shettima": An gayawa Tinubu wanda ya fi dacewa ya zama mataimakinsa a 2027
Wannan martani ya biyo bayan wasu sharudda da Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya gabatar cikin wata muhawara, wacce ke nuna kamar shi ne mau fada a ji da ya rage a PDP.
Mai magana da yawun babbar jam'iyya ta ƙasa, Debo Ologunagba, a yayin ganawa da manema labarai a Abuja ranar Laraba, 13 ga Agusta, 2025, ya ce babu wanda ya isa ya kafa masu sharadi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

