Rigima Ta Barke a APC, An Dakatar da Tsohon Gwamna kuma Sanata Mai Ci
- Jam’iyyar APC ta dakatar da tsohon gwamnan jihar Ogun, Sanata Gbenga Daniel da wani babban dan siyasa, Hon. Kunle Folarin
- An dakatar da 'yan siyasar biyu ne bayan kin amsa gayyatar kwamitocin ladabtarwa da ke bincikarsu kan zargin cin amanar jam'iyya
- APC ta ce Sanata Daniel da Hon. Folarin sun nuna rashin da'a kuma sun yi yunkurin tursasa wa 'yan kwamitin janye bincike a kansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ogun – Jam’iyyar APC ta dakatar da Sanata Gbenga Daniel da Hon. Kunle Folarin saboda zargin aikata ayyukan da suke cin dunduniyar jam’iyya.
An yanke wannan hukunci ne a wani taro da shugaban jam’iyyar na jihar, Cif Yemi Sanusi, ya jagoranta a ranar Talata, inda mambobi 16 suka halarta.

Source: Twitter
Ana tuhumar sanata da cin dunduniyar APC
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran APC a Ogun, Nuberu Olufemi, ya fitar a Abeokuta, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta bayyana cewa taron ya kuma yi la’akari da rahotannin kwamitocin ladabtarwa da suka gudanar da bincike kan manyan 'yan siyasar biyu.
Jam'iyyar APC a Ward 4, Sagamu, ta kafa kwamitin ladabtarwa domin bincikar zargin da aka yi wa Sanata Gbenga Daniel na aikata ayyukan adawa da jam’iyya.
Hakanan, APC a Ward 6, Sagamu ta kafa kwamiti domin bincikar ayyukan rashin da’a da ayyukan adawa da jam’iyya da ake zargin Hon. Kunle Folarin ya aikata.
Sanata ya ki amsa gayyatar kwamitin APC
Kwamitocin sun rubuta takardun gayyata ga wadanda ake zargi domin halartar zaman ladabtarwar, inda za su sami damar kare kansu ko neman afuwa daga jam’iyyar.
The Guardian ta rahoto cewa duka 'yan siyasar biyu sun ki amsa gayyatar, sun gaza rubuta takardar kare kai, ko kuma su halarci zaman ladabtarwar don kare kansu.
Nuberu Olufemi ya bayyana cewa la’akari da rashin amsa gayyatar ba tare da wani dalili ba, kwamitocin sun ci gaba da zamansu, inda suka saurari shaidu, sannan suka duba hujjojin da aka gabatar.

Source: Twitter
APC ta dakatar da sanata daga jam'iyya
Sanarwar ta kuma ce tsohon gwamna, Gbenga Daniel da Hon. Folarin sun yi amfani da matsayinsu wajen cin zarafi da yin barazana ga mambobin kwamitin ladabartarwar don janye korafe-korafen da aka shigar kansu.
Nuberu Olufemi ya kara da cewa:
“Duba da abin da ya faru, kwamitocin suka yanke hukuncin dakatar da Sanata Gbenga da Hon. Folarin har sai an kammala bincike."
Ya ce dakatarwar ta biyo bayan rashin hadin kan da manyan 'yan siyasar suka nuna a lokacin binciken da kuma yunkurinsu na tursasa kwamitocin su janye ƙorafe-ƙorafen da aka shigar.
Gwamna zai rusa gidan Sanata Gbenga Daniel
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan jihar Ogun ya shiga damuwa yayin da yake zargin ana yi masa bita da kulli domin ruguza shi.
Gbenga Daniel, ya zargi Gwamna Dapo Abiodun da amfani da sabuwar doka wajen yi masa barazanar rushe gidaje da gine-ginen da ya mallaka a jihar.
Tsohon gwamnan wanda yanzu sanata ne ya ce gwamnatin Ogun ta ba shi kwana uku kacal ya kwashe kadarorinsa da suka hada da Asoludero da otal.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

