'Ya Cancanci Tazarce,' An ba Ƴan Najeriya Dalilai 20 na Sake Zabar Tinubu a 2027

'Ya Cancanci Tazarce,' An ba Ƴan Najeriya Dalilai 20 na Sake Zabar Tinubu a 2027

  • Reno Omokri ya bayyana cewa zabukan cike gurbi sun nuna amincewar ’yan Najeriya da shugabancin Bola Tinubu da APC
  • Tsohon hadimin shugaban kasar ya gabatar da wasu dalilai 20 da ya ce za su sanya 'yan Najeriya su sake zabar Tinubu a 2027
  • Dalilan sun haɗa da daidaita tattalin arziki, sabon mafi ƙarancin albashi, kari a GDP, ingantaccen tsaro, da dai sauransu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Reno Omokri, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya cancanci tazarce a 2027.

Fitaccen marubucin ya bayyana cewa 'yan Najeriya sun zabi jam'iyyar APC a zabukan cike gurbi da aka gudanar ranar Asabar saboda wasu dalilai 20.

Reno Omokri ya ce Shugaba Bola Tinubu ya cancanci tazare a 2027 saboda wasu dalilai 20.
Tsohon hadimin Jonathan, Reno Omokri yana gaisawa da Shugaba Bola Tinubu a Legas. Hoto: @renoomokri
Source: Twitter

Dalilai 20 na zabar Tinubu a 2027

A shafinsa na Facebook, Reno Omokri ya ce wadannan dalilai 20 ne kuma za su sanya 'yan kasar su sake zabar Tinubu a zaben 2027.

Kara karanta wannan

'Kwankwaso ba zai goyi bayan Tinubu a zaben 2027 ba,' Buba Galadima ya kawo dalilai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Daidaita tattalin arzikin Najeriya

Shugabar Hukumar Cinikayya ta Duniya, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana cewa Shugaba Tinubu ya “daidaita” tattalin arzikin Najeriya.

2. Ƙaruwa a GDP na ƙasa

Najeriya ta samu ci gaban GDP na 3.84% a zango na hudu, 2024, mafi girma a cikin shekaru uku, sama da wanda Buhari ya bari.

3. Sabon mafi ƙarancin albashi

A ranar 29 ga Yuli, 2024, Shugaba Tinubu ya rattaba hannu dokar sabon mafi ƙarancin albashi na ₦70,000, fiye da ninki biyu na tsohon albashin.

4. Cika ƙa’idar OPEC

Najeriya ta cika, ta kuma zarce, ƙa’idar fitar da mai ta OPEC tsawon watanni uku a jere, abin da ba a samu ba tsawon shekaru.

5. Sauya tsarin haraji

A ranar 26 ga Yuni, 2025, Shugaba Tinubu ya sanya hannu kan dokar Haraji ta Najeriya, abin da ya kawo sabon tsarin adalci wajen raba kudaden haraji.

Kara karanta wannan

Jihohi 3 da 'yan adawa suka lallasa APC a zaben cike gurbi a Najeriya

6. Tarihi a bangaren wutar lantarki

A ranar 4 ga Maris, 2025, Najeriya ta karya tarihin samar da wuta da 5,801.84MW, mafi girma da aka taɓa samu a tarihin masana’antar wutar lantarki.

7. Ƙara GDP da dala biliyan 67

Najeriya ta ƙara dala biliyan 67 cikin GDP dinta, daga ₦269.29tr a watan Mayun 2023 zuwa ₦372.8tr a halin yanzu.

8. Rarar ciniki ta tarihi

An samu rarar ciniki ta ₦16.89tr ($14bn), saboda ƙarancin dogaro da shigo da kaya daga ƙasashen waje.

9. Ƙarin kuɗin ajiyar kuɗin kwaje

Saboda wadatar Naira, ajiyar kuɗin waje ya kai dala biliyan $40.877, sama da dala biliyan $3.7 da aka gada daga gwamnatin Buhari.

10. Rage bashi na ƙasa

Bashin ƙasa ya ragu daga dala biliyan $108.2 a 2023 zuwa $94.2bn. Obasanjo da Tinubu ne kaɗai suka taɓa rage bashin ƙasa a mulkin farar hula.

11. ’Yancin kananan hukumomi

'Yancin cin gashin kai na kananan hukumomi ya zama gaskiya karkashin Tinubu, inda yanzu kananan hukumomi suka samu ’yanci daga gwamnonin jihohi.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya ga ta kansa, ana zargin shi ya jawo APC ta fadi zabe a Ibadan

12. Lamunin ɗalibai

Fiye da ɗalibai 600,000 sun amfana da tsarin lamunin karatu na Tinubu karkashin NELFUND, kuma rabinsu sun fito ne daga Arewacin Najeriya.

13. Babu yajin aikin ASUU

Malaman jami'o'i karkashin ASUU ba su shiga yajin aiki ba tsawon shekaru biyu na mulkin Tinubu, abin da bai taɓa faruwa cikin shekaru 30 ba.

14. Ƙarancin man fetur ya kare

Najeriya ta daina shigo da mai, yanzu tana wadatar da kanta kuma ita ce babbar mai fitar da man da aka tace a Yammacin Afirka.

15. Tsaro a titin Abuja–Kano

Titin Abuja–Kano da ya sha fuskantar sace-sacen mutane yanzu ya zamo hanya mai tsaro saboda matakan da NSA Nuhu Ribadu ya dauka.

Reno Omokri ya ba 'yan Najeriya dalilai 20 da za su sanya su zabi Shugaba Tinubu a 2027
Shugaa Bola Tinubu a zauren majalisar zartarwar yayin da za a fara taron FEC a Abuja. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

16. Fasfo cikin makonni biyu

’Yan Najeriya na samun fasfo dinsu cikin makonni biyu ko ƙasa da haka, matsalar karancin fasfo ta kare a kasar.

17. Filin jirgin Abuja na zamani

Filin jirgin Nnamdi Azikiwe ya zama na zamani a ƙasa da ma yankin Sahara, komai ya zama mai amfani da lantarki daga saukar jirgi har zuwa mutum ya fita daga filin jirgi.

Kara karanta wannan

"Ƴan takara 2 ne za su iya hana Tinubu cin zaɓen 2027," Ayodele ya gargaɗi Atiku

18. Zaman lumana a Niger Delta

Satar mai ta ragu zuwa ƙasa da 2%. A Ogoni, gwamnati na gina sabuwar makarantar kimiyya da fasaha tare da tsaftace muhalli duk don ci gaban Neja Delta.

19. Ingantuwar hasashen IMF

Asusun IMF ya sauya hasashensa kan ci gaban Najeriya, inda ya ce ci gaban ya karu daga 3.0% zuwa 3.4% a ranar 29 ga Yuli, 2025.

20. Matsayi daga Fitch da Moody’s

A watan Afrilu da Mayu, 2025, hukumomin Fitch da Moody’s sun ɗaga matsayin tattalin arzikin Najeriya zuwa B da B3, alamar ci gaba mai ƙarfi a kasar.

Sai dai Legit Hausa ta fahimci cewa akwai gyara a wasu batutuwan da Omokri ya kawo.

Alal misali, a watan Agustan nan binciken Punch ya nuna fiye da 71% na man fetur da aka sha daga waje yake, 'yan kasuwa sun yi watsi da matatar Dangote.

Nasarar APC a zabukan cike gurbi

Tun da fari, mun ruwaito cewa, APC ta samu nasara a mafi yawan mazabun da aka gudanar da zaben cike gurbi a jihohi 13 a Najeriya a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

'Mun gama zabi,' APC a yankin Tinubu ta yanke hukunci kan zaben shugaban kasa

APC reshen jihar Legas ta ce jama'a sun fito sun zabi jam'iyyar ne saboda su kara nuna gamsuwa da goyon bayan gwamnatin Bola Tinubu.

Mai magana da yawun APC a Legas ya ce nasarorin da APC ta samu ranar Asabar karkashin shugabancin Nentawe Yilwatda sun shiga tarihi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com