Matasa Sun Fara Kokarin Jawo Ra'ayin Gwamna, Sun Nemi Ya Sauya Sheka zuwa APC
- Matasa sun fara kiran Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu ya sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC kafin babban zaben 2027
- Matasan sun sha alwashin tara masa kuri'u masu yawa tare da tabbatar da ya koma zango na biyu a zabe mai zuwa
- Shugaban matasan APC na Enugu, Peter Chime ya ce dawowar Peter Mbah cikin jam'iyyar zai cika burinsu na karbe mulkin jihar daga PDP
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Enugu - Matasan APC a jihar Enugu da ke Kudu maso Gabashin Najeriya sun fara kokarin kwadaitar da Gwamna Peter Mbah ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.
Matasan sun bukaci mai girma gwamnan da ya duba yiwuwar baro PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya kafin babban zaben 2027.

Source: Twitter
Shugaban matasan na Enugu, Mista Peter Chime, ne ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki na tawagar matasa da aka shirya a jihar, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan
ADC ta cimma matsaya da Atiku, Peter Obi da Amaechi kan batun takara a zaben 2027
Matasa sun bukaci gwamna ya dawo APC
Da yake jawabi a wurin taron, Mista Chime ya ce suna gayyatar Gwamna Mbah ya dawo APC ne domin su mara masa baya ya yi tazarce a zaben 2027.
Ya kara da cewa hakan na daya daga cikin shirye-shiryen da suke yi na karfafa APC, domin karbe mulkin jihar Enugu.
“Muna roƙon gwamnanmu, Dr. Peter Ndubuisi Mbah, da ya shigo APC domin Jihar Enugu ta more cikakkun alfanu da fa'idoji daga gwamnatin tarayya,” in ji Chime.
Chime ya bayyana cewa wannan taron da suka yi ya kuma mayar da hankali kan sasantawa da masu ƙin jinin jam’iyya da kuma jawo waɗanda suka ja gefe su dawo su tallafa wajen gina APC.
Matasan Enugu sun marawa Tinubu baya
Matasan sun kuma bayyana cikakken goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ya yi tazarce zuwa wa'adi na biyu a zaben 2027.

Kara karanta wannan
'Abin da ya sa APC ta lashe mafi yawan zabukan cike gurbi da aka yi a Kano da jihohi 12'
A cewarsu, sun shirya tsaf domin fadada goyon bayan APC da tara wa duk wani dan takarar jam'iyyar kuri'u masu yawa a shiyyar Kudu maso Gabas a zabe mai zuwa.

Source: UGC
Tsohon shugaban APC na jihar, Dr. Ben Nwoye, wanda ya halarci taron, ya ce jam’iyyar na kan aiki ba dare ba rana domin tara magoya baya da jama’a a matakin ƙananan hukumomi.
Ya ce za su ci gaba da roƙon Gwamna Mbah da ya canza tunani, ya taho ya hada kai da tsare-tsaren APC ta hanyar shigowa jam'iyyar.
Gwamna Mbah ya nada sababbin kwamishinoni
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Peter Mbah ya yi garambawul a majalisar zartarwa ta jihar Enugu bayan rantsar da sababbin kwamishinoni.
Gwamna Mbah ya raba wa sababbin kwamishinonin ma'aikatin da za su yi aiki bayan da Chizoba Ogbodo, wakiliyar ma'aikatar shari'a, ta rantsar da su.
Ya shaidawa wadanda aka rantsar cewa babu lokaci batawa a gwamnatinsa, don haka su zage dantse wajen ci gaba da ayyukan da aka faro tun shekaru biyu da suka gabata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng