Ministan Tinubu Ya ga Ta Kansa, Ana Zargin Shi Ya Jawo APC Ta Fadi Zabe a Ibadan

Ministan Tinubu Ya ga Ta Kansa, Ana Zargin Shi Ya Jawo APC Ta Fadi Zabe a Ibadan

  • Wata ƙungiyar APC, Unity Frontiers ta danganta faduwar jam’iyyar a zaben cike gurbi na mazabar Ibadan ta Arewa ga rabuwar kai
  • A hannu daya, kungiyar Concerned Leaders ta yi ikirarin cewa ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu ne ya jawo faduwar APC
  • Kungiyoyin biyu, sun ce idan har ba a taka wa Adelabu birki ba, to abubuwan da yake yi za su jawo APC ta fadi zabe a jihar Oyo a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Oyo - Wata kungiyar magoya bayan APC a jihar Oyo mai suna APC Unity Frontiers, ta bayyana dalilin da ya sa jam'iyyar ta fadi zaben cike gurbi a mazabar Ibadan ta Arewa.

Kungiyar ta ce APC ta fadi zaben kujerar majalisar ne saboda rabuwar kawuna a cikin jam’iyyar da kuma tasirin ministan wutar lantarki, Cif Adebayo Adelabu.

Kara karanta wannan

PDP ta yi kuka da zaɓe a Zamfara, ta yi zargin sojoji da ƴan ta'adda sun jawo matsala

Kungiya ta bayyana dalilin da ya sa jam'iyyar APC ta sha kasa a zaben cike gurbi na mazabar Ibadan ta Arewa
Gungun magoya bayan APC a wani gangamin jam'iyyar da aka gudanar a jihar Imo a Fabrairun 2023. Hoto: @GoziconC
Source: Twitter

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaba da sakataren ƙungiyar, Alhaji Akindele Olatubosun, da Mr. Taiwo Adeniyi suka fitar a ranar Lahadi, inji rahoton The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Dalilin rashin nasarar APC a Ibadan' - Kungiya

Kungiyar ta yi gargadin cewa irin wannan matsalar na iya sake maimaituwa a zaben gwamna na shekarar 2027 idan aka tsayar da Adelabu a matsayin ɗan takarar jam’iyyar.

Ta yi zargin cewa ministan ne ya kakaba dan takarar APC a zaben cike gurbin ta karfin tsiya, wanda ya jawo faduwar jam'iyyar.

Sanarwar ta ce:

“Mutanen jihar Oyo ba sa son komai daga wurin Adelabu halinsa na rashin kyautata wa mutane, ji-ji-da-kai da kuma uwa-uba taurin kai.
“Da ace Mr Murphy ɗan takara ne mai zaman kansa, ba wanda ministan wutar lantarki ya ɗora shi ba, da sakamakon zaben zai iya bambanta.”

Ƙungiyar ta roƙi Shugaba Bola Tinubu da shugabannin APC na ƙasa su hana daidaikun mutane juya akalar jam’iyyar, tana mai jaddada cewa kin magance wannan matsala ka iya janyo faduwarta a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Nasarar APC, PDP, NNPP: INEC ta bayyana sakamakon zabukan cike gurbi a jihohi 8

An danganta ministan da faduwar APC

Hakazalika, wata ƙungiya mai suna Concerned Leaders ita ma ta bayyana cewa ɗora ɗan takara da yanke shawara mara kyau sune dalilan da yasa APC ta sha kaye a zaben cike gurbin Ibadan ta Arewa.

Ana zargin ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu ne ya jawo APC ta fadi zaben cike gurbi a Ibadan ta Arewa.
Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu yana jawabi a wani taron makamashi da aka gudanar a Abuja. Hoto:@EUinNigeria
Source: UGC

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban ƙungiyar, Tejumola Adisa, ya rattaba hannu a kai, kuma aka rabawa jaridar New Telegraph.

Kungiyar ta zargi ministan wuta, Adebayo Adelabu, da cewa ya kakaba Mr Murphy Olatunji a matsayin dan takara a zaben, kuma mafi yawan ‘yan APC ba su ji daɗin hakan ba.

Adisa, wanda ya yi magana a madadin ƙungiyar, ya kuma zargi Adelabu da bayar da manyan mukamai uku da aka bai wa jihar ga mambobin jam’iyyar AP, jam’iyyar da ya tsaya takarar gwamna a shekarar 2023.

'Dan takarar PDP ya lashe zabe a Ibadan

Tun da fari, Legit Hausa ta rahoto cewa ɗan takarar jam’iyyar PDP, Folajinmi Oyekunle, ya lashe zaben cike gurbi na mazabar Ibadan ta Arewa a jihar Oyo.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta lallasa PDP a zaben cike gurbi na dan majalisar Jigawa da ya rasu

INEC ta bayyana cewa Oyekunle ya samu kuri’u 18,404 inda ya doke abokin hamayyarsa mafi kusa, Adewale Olatunji na APC wanda ya samu kuri’u 8,312.

Hukumar ta ce Femi Akin-Alamu na jam'iyyar ADC ya samu kuri’u 88, yayin da Olabisi Olajumoke na jam'iyyar APGA ya samu kuri’u 40.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com