Kano: INEC Ta Sanar da Sakamakon Zaben Cike Gurbi na Ghari, Tsanyawa
- A ranar Asabar, 16 ga watan Agustan 2025 aka gudanar da zabe a mazabar Ghari/Tsanyawa na majalisar dokokin jihar Kano
- Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanar da sakamakon zaben da safiyar ranar Lahadi, 17 ga watan Agustan 2025
- Jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano ta yi rashin nasara bayan dan takararta ya sha kashi a hannun abokin hamayyarsa na APC
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) reshen jihar Kano, ta sanar da sakamakon zaben mazabar Ghari/Tsanyawa a majalisar dokokin jihar Kano.
Jam’iyyar APC mai adawa a jihar Kano ta lashe zaben na mazabar Ghari/Tsanyawa a jihar Kano, bayan ta lallasa abokiyar hamayyarta wato NNPP.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an bayyana sakamakon zaben ne da misalin karfe 6:10 na safiyar ranar Lahadi, 17 ga watan Agustan 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami’in tattara sakamakon zabe, Farfesa Muhammad Waziri na Jami’ar Bayero, ya bayyana sakamakon zaben.
Farfesa Muhammad Waziri ya bayyana cewa Garba Ya’u Gwarmai na jam’iyyar APC ya yi nasara da ƙuri’u 31,472.
Ya doke ɗan takarar jam’iyyar NNPP, Yusuf Ali Maigado, wanda ya samu ƙuri’u 27,931.
An gudanar da wannan zaɓen cike gurbin ne bayan an ayyana zaɓen farko a mazabar a matsayin wanda bai kammalu ba.
An yi musayar kalamai tsakanin APC da NNPP
Tun da farko jam'iyyar APC ta bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta soke zaɓen cike gurbi a Kano.
APC ta bayyana cewa a akwai matsaloli, saboda haka ta roƙi INEC ta soke zaɓen majalisar dokokin da aka gudanar a ranar Asabar.
Ta bayyana cewa ba a gudanar da zaɓen a cikin lumana ba, inda ta ce an samu tashin hankali, rikici, da kuma fitinar ’yan daba a rumfunan zabe daban-daban a mazabun da abin ya shafa.

Source: Original
Jam’iyyar NNPP ta yi Allah-wadai da kiran soke zaɓen cike hurbi da aka gudanar a mazabar Shanono/Bagwai da kuma sake zaɓe a mazabar Ghari a jihar Kano.
Jaridar The Cable ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na NNPP, Ladipo Johnson, ya fitar a ranar Asabar.
Ladipo Johnson ya bayyana cewa buƙatar da jam’iyyar APC ta gabatar ba ta da tushe kuma ba ta da wata hujja ko dangantaka da gaskiya.
Ya dage cewa zaɓen ya kasance cikin gaskiya, sahihnaci da lumana.
APC ta yaba da sakamakon zabe
Kakakin jam'iyyar APC a jihar Kano, Ahmed Aruwan, ya shaidawa Legit Hausa cewa sun yi farin ciki sosai da wannan nasarar da suka samu a zaben.
Ya kuma yi watsi da sukar da jam'iyyar NNPP ta yi kan zaben na Ghari/Tsanyawa.
"Muna farin ciki da wannan nasarar da muka samu a zaben. Muna fatan ma na Bagwai/Shanono ya dawo hannunmu idan INEC ta yi bincike."
- Ahmed Aruwan
NNPP ta lashe zabe a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar NNPP ta samu nasara a zaben cike gurbi na Shanono/Bagwai da hukumar zabe ta INEC ta gudanar.
Dan takarae NNPP, Ali Lawan Alhassan Kiyawa, ya lallasa abokin hamayyarsa na jam'iyyar APC.
Hukumar INEC ce dai ta sanar da sakamakon zaben bayan ta kammala tattara kuri'un da aka kada.
Asali: Legit.ng


