Matasa Sun Lakadawa Wakilin PDP Duka kan Zarginsa da Rike Musu Katunan Zabe
- Rikici ya barke a zaben Edo inda aka lakada wa jami’in PDP duka saboda kin raba katin zabe ga masu kada kuri’a
- Jami’an ‘yan sanda sun shiga tsakani inda suka ceci wakilin PDP daga fushin jama’a a makaratar firamare
- Duk da rikicin, kayan zabe sun iso tun 7:00 na safe, mutane da dama sun fito domin kada kuri’a a wuraren zabe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Benin City, Edo - Ana ci gaba da gudanar da zaben cike gurbi na wasu kujeru a fadin Najeriya a yau Asabar 16 ga watan Agustan 2025.
Hukumar INEC ce ta sanya yau Asabar domin cike gurbin wasu kujeru da babu kowa na majalisun jiha da na tarayya a Najeriya.

Asali: Facebook
An yi wa wakilin PDP duka a Edo
Rahoton The Nation ya ce an samu tashin hankali a zaben Edo lokacin da aka lakada wa wani wakilin jam’iyyar PDP duka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin ya faru ne a mazabar Ozolua da ke makarantar firamare ta Model a garin Iguobazuwa da ke jihar a Kudancin Najeriya.
Shaidu sun bayyana cewa wakilin jam’iyyar ya ki raba katin zabe ga masu kada kuri’a, lamarin da ya fusata jama’ar da ke layin zabe.
Sun yi zargin cewa jami’in PDP ya yi nufin hana su damar kada kuri’unsu, abin da suka ce ya saba wa hakkinsu na dimokiradiyya.
Bayan jama’ar sun fara kai masa hari, jami’an ‘yan sanda suka shigo cikin lamarin domin ceton rayuwarsa daga hannun masu zabe.
An ce babu wanda ya ji rauni mai tsanani, sai dai wakilin jam’iyyar PDP ya sha da kyar da dukan da aka yi masa a wurin.

Asali: Original
Yan sanda sun shiga lamarin a Edo
Sai dai rundunar yan sanda ta tabbatar da cewa za a gudanar da bincike kan lamarin domin gano dalilan rashin raba katin zaben.

Kara karanta wannan
Zabe ya dauki zafi, ana zargin an sace yar takarar majalisar tarayya da wasu 25 a Kaduna
Bayan haka, rahotanni sun nuna cewa kayan zabe sun iso a wuraren zabe na Iguobazuwa tun ƙarfe 7:00 na safe.
Masu kada kuri’a da dama sun bayyana cewa sun fito domin kada kuri’a duk da dan rikicin da ya faru a yankin, Daily Post ta ruwaito.
A cewar wani mazaunin yankin:
“Jama’a suna son yin zabe cikin kwanciyar hankali, amma abin da ya faru ya jawo ɗan tsoro ga wasu.”
Sai dai hukumar zabe ta bayyana cewa za a ci gaba da gudanar da zabe a wuraren da aka tashi hankali ba tare da matsala ba.
Wannan lamari ya nuna yadda zaben ke kasancewa da kalubale a wasu wurare, duk da cewa an shirya tsaf domin gudanarwa lafiya.
Kaduna: An kama wakilin PDP da miliyoyon kudi
Mun ba ku labarin cewa yan sanda da jami'an DSS sun cafke wani mutumi da ake zargin wakilin PDP ne dauke da makudan kudi.

Kara karanta wannan
Asiri ya tonu: An kama wakilin PDP a otal dauke da kusan Naira miliyan 26 a Kaduna
An kama dan PDP, Shehu Fantagi a wani fitaccen otal a cikin garin Kaduna da kudi kimanin N25,963,000.
Rundunar yan sanda ta gargadi mazauna Kaduna cewa babu wanda za ta daga wa kafa idan aka kama shi da hannu a yunkurin lalata zabe.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng