2027: Manyan APC 4 da Suka Ƙaryata Rade Radin Komawa Jam’iyyar Hadaka Ta ADC
A Najeriya, jam'iyyar haɗaka ta ADC na ci gaba da dauke jiga-jigan jam'iyyun siyasa da dama yayin da ake tunkarar zaben shekarar 2027.
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Hadakar ADC ta samu ne bayan manyan yan adawa a kasar da wasu fusatattun yan APC sun yanke shawarar amfani da ita a matsayin dandalin siyasa.

Asali: Facebook
Jiga-jigan da suka koma ADC kan zaben 2027
Rahoton Punch ya ce ADC na dauke da manyan yan adawa kamar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da Peter Obi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran sun hada da tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark da wasu da suka bar APC mai mulkin Najeriya zuwa jam'iyyar haɗaka ta ADC
Daga cikin wadanda suka bar APC akwai Malam Nasir El-Rufai wanda ya koma SDP kafin goya wa ADC baya a matsayin jam'iyyar haɗaka.

Kara karanta wannan
Al Makura: Ƴan bindiga sun bi dare, sun sace hadimin tsohon gwamna, an bazama daji
Sai kuma tsofaffin ministoci a APC, Abubakar Malami da Rotimi Amaechi da suka rike mukaman a mulkin marigayi Muhammadu Buhari.
Rade-radin cewa manyan APC sun koma ADC
An yi yawa jita-jitar cewa wasu yan APC sun bar jam'iyyarsu zuwa ADC wanda suka musanta hakan.
Legit Hausa ta yi duba kan manyan APC har ma da gwamnoni da suka musanta sauya sheka zuwa ADC.
1. Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni
Gwamna jihar Yobe, Mai Mala Buni ya fito karara ya ƙaryata labarin cewa ya koma ADC mai adawa a Najeriya.
Gwamnan ya ce babu abin da zai yi a jam'iyyar haɗaka duba da irin matsalolin da suke fama da ita kuma yana nan daram a APC.
Gwamnatin jihar Yobe ta ce rade-radin cewa gwamnan zai koma jam’iyyar ADC karya ce marar tushe kuma bai kamata a rika yarda da labarai marasa tushe ba.
Hadimin gwamnan, Mamman Mohammed ya bayyana cewa wannan zance jita-jita ce da aka riga aka karyata a baya.

Kara karanta wannan
PDP ta sacewa magoya bayan Jonathan da Obi guiwa da aka kafa kwamitin karba karba
Wannan na zuwa ne yayin da APC ke shirin zaben sabon shugaban jam’iyya bayan murabus din Abdullahi Umar Ganduje.

Asali: Twitter
2. Tsohon sakataren gwamnati, Boss Mustapha
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya a mulkin Muhammadu Buhari ya yi magana kan jita-jitar komawa ADC.
Ya ce duk rahoton da ake haɗawa karya ne babu abin zai fitar da shi daga jam'iyyar APC wanda suka sha mata wahala.
Boss Mustapha ya musanta rahotannin da ke danganta shi da kawancen ‘yan adawa da kuma rungumar jam’iyyar ADC.
Ya kara da cewa kamar kowace jam'iyya, APC na fama da ƙalubale, amma ficewa daga cikinta ba shi ne maslaha a halin da ake ciki ba.

Asali: Facebook
3. Tsohon gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi
Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya musanta zargin cewa da shi aka kafa sabuwar kawancen ADC da ke adawa da Bola Tinubu.
Dr. Kayode Fayemi ya bayyana cewa har yanzu yana tare da APC, kuma babu kamshin gaskiya a ikirarin cewa su ne suka farfado da ADC.
Wannan na zuwa a matsayin martani ga wasu kalamai da aka alakanta da tsohon gwamnan jihar Rivers watau Rotimi Amaechi, cewar Premium Times.

Asali: Facebook
4. Sanata Abdul'aziz Yar'Adua
A bangarensa, Sanata Abdulaziz Musa Yar'adua ya yi magana kan jita-jitar da ke cewa ya fice daga jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Sanatan ya bayyana cewa ko kadan babu kamshin gaskiya a ciki domin har yanzu shi cikakken mamba ne a jam'iyyar APC.
Yar'Adua da ke wakiltar Katsina ta Tsakiya ya bayyana cewa ba kowane mai suna Yar'adua ba ne yake da alakar siyasa da shi.
Hakan ya biyo bayan ficewar tsohon sanata a jihar Katsina, Abubakar Sadik Yar'Adua wanda ya yi murabus daga cikin jam'iyyar APC.

Asali: Twitter
Ana zargin ADC na tattaunawa da Jonathan
A wani labarin, wasu rahotanni sun tabbatar da cewa jam'iyyar haɗaka ta ADC na tattaunawa da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.
Majiyoyi suka ce hakan na cikin wani shiri da jam'iyyar ke yi domin kifar da gwamnatin Bola Tinubu a zaben shekarar 2027 da ake tunkara a Najeriya.
Hakan kamar yadda aka ruwaito na daga cikin dalilin da ya sa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar bai karbi katin jam'iyyar ba kamar yadda ya shirya a Yola.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng