Rikici Ya Kacame da Shugaban Karamar Hukuma a Neja Ya Maka Gwamna Bago a Kotu

Rikici Ya Kacame da Shugaban Karamar Hukuma a Neja Ya Maka Gwamna Bago a Kotu

  • Rikicin siyasa ya kunno kai tsakanin Gwamna Umaru Bago na Neja da shugaban karamar hukumar Chanchaga, Aminu Yakubu Ladan
  • Shugaban karamar hukumar ya kai ƙara kotu kan yunkurin kawo ƙarshen wa’adinsa ba bisa ka'ida ba bayan Bago ya shirya sabon zabe
  • APC ta zaɓi tsohon abokin hamayyarsa a matsayin ɗan takarar da zai tsaya a zaɓen kananan hukumomi mai zuwa a jihar Neja

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Neja – Rikicin siyasa tsakanin Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago, da shugaban karamar hukumar Chanchaga, Aminu Yakubu Ladan, ya ƙara tsananta.

Aminu, wanda ya sha gwagwarmayar shari’a kafin ya shiga ofis ya fara aiki bayan kotu ta mayar da shi a matsayin shugaban ƙaramar hukuma.

Gwamnan jihar Nej, Umaru Bago
Gwamna Umaru Bago a yayin wani taro a Neja Hoto: Mohammed Umaru Bago
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an alakanta dawowarsa kujerar saboda tasirin manyan APC masu biyayya ga Alhaji Baba Yakubu, ɗan siyasa mai ƙarfin fada a ji a jihar.

Kara karanta wannan

Jerin manyan kujerun gwamnatin tarayya da Tinubu ya ba mutanen Kano a shekaru 2

Shugaban karamar hukumar Neja ya kai ƙara kotu

Daily Post ta wallafa cewa yayin da wa’adin mulkin shugabannin ƙananan hukumomi ke gab da ƙarewa, Ladan ya kai ƙara kotu yana kalubalantar abin da ya kira yunkurin kawo ƙarshen wa’adinsa da wuri.

Ya ce:

“Kamar yadda shugaban ƙasa da gwamnoni suke, shugabannin ƙananan hukumomi ma suna da ikon kammala cikakken wa’adin shekaru huɗu.”

Akwai rikici a APC reshen jihar Neja

Gwamnan ya sanar a wani taron shugabannin jam’iyyar cewa APC za ta yi amfani da tsarin yarjejeniya wajen zaɓar ‘yan takara a zaɓen kananan hukumomi da aka shirya gudanarwa a ranar 1 ga Nuwamba, 2025.

Sai dai tsarin bai amfanar da Aminu ba, domin an zaɓi tsohon abokin hamayyarsa, Dr Mustapha Alheri—wanda kotu ta taba cirewa daga kujerar—don tsayawa takara.

Wasu shugabannin APC na jihar sun bayyana cewa, ko da an fito da ɗan takarar yarjejeniya daga wani yanki, gwamna na da ikon sauya shi kuma cire Aminu na da alaka da siyasa.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi ruwan mukamai a hukumomin tarayya ana jita jitar ciwo

Hoton gwamnan jihar Neja
Gwamna Umaru Bago a gidan gwamnatin Neja Hoto: @HonBago
Source: Twitter

Wata majiya ta ce:

“Gwamna na ƙoƙarin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a watan Nuwamba, kuma ƙarar da Aminu ya kai kotu tana adawa kai tsaye da wannan shiri. Rikicin ya ƙara tsananta ne lokacin da majalisar ƙaramar hukumar Chanchaga ta dakatar da shi daga aiki.”

Majiyar ta bayyana cewa akwai wasu faifan sauti da suka fito daga baya, inda ake zargin kansilolin sun yarda cewa sun karɓi kuɗi daga wasu mutane domin su cire shi.

Gwamnatin Neja ta shigar da Tinubu a kotu

A baya, mun wallafa cewa gwamnatin Neja ta shigar da ƙara a gaban Kotun Koli tana kalubalantar cire ta daga cikin jihohin da ke amfana da 13% na haƙƙin albarkatun ƙasa a Najeriya.

Masu shigar da ƙarar sun roƙi Kotun Koli da ta tantance ko jihar Neja ba ta cancanci a saka ta cikin jerin jihohin da ke samar da albarkatun ƙasa ba, don haka ba ta da haƙƙin samun kasonta.

Haka kuma, ta zargi gwamnatin tarayya da gazawa wajen haɗa kuɗin da ake samu daga albarkatun da ake samarwa daga madatsun ruwan wutar lantarki da ke cikin yankinta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng