'Ya Riga Ya Ci Zabe,' Sanatan Nasarawa Ya Fadi Wanda Zai Shiga Aso Rock a 2027

'Ya Riga Ya Ci Zabe,' Sanatan Nasarawa Ya Fadi Wanda Zai Shiga Aso Rock a 2027

  • Sanatan Nasarawa ta Yamma, Aliyu Wadada, ya ce tuni kujerar shugaban ƙasa ta 2027 ta koma hannun Shugaba Bola Tinubu
  • Wadada ya ce babu wata jam'iyyar adawa ko 'yan takararsu da za su iya shimfida ayyukan alherin da Tinubu ya yi wa Najeriya
  • Dan majalisar dattawan ya bayyana yiwuwar komawa APC yayin da ya jaddada cewa Najeriya ta samu ci gaba karkashin Tinubu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Sanatan Nasarawa ta Yamma, Aliyu Wadada, ya bayyana cewa tuni kujerar shugaban ƙasa ta zama ta Shugaba Bola Tinubu a 2027.

Sanata Wadada ya bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban ƙasa a ranar Talata, jim kaɗan bayan ganawarsa da Tinubu.

Sanata Wadada ya ce Shugaba Bola Tinubu ya lashe zaben shugaban kasar 2027 ya gama
Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zauren majalisar zartarwa ta kasa ana shirin fara taron FEC. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Dan majalisar dattawan ya ce ya kai wa shugaban kasar ziyara don nuna godiya bisa taya shi murna da Tinubu ya yi kan nadin da aka yi masa matsayin Maga Jindengi na Lafia inji rahoton The Guardian.

Kara karanta wannan

Wadada: Sanatan SDP ya koma APC bayan ganawa da Shugaba Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Wadada na shirin komawa APC

Da aka tambaye shi kan yadda yake ziyartar fadar shugaban ƙasa a kai a kai duk da kasancewarsa ɗan jam’iyyar SDP, Wadada ya ce Aso Rock “gida ne ga kowanne dan Najeriya.”

Sanata Wadada ya ce dole ya tariyo yadda ya taɓa zama sakataren kudi na kasa na PDP kafin daga bisani ya koma APC tun kafin a kafa ta, sannan daga baya ya bar APC ya koma SDP.

“Ban fita daga APC zuwa SDP APC ta yi min wani laifi ba, yanayi ne kawai ya kawo hakan. Komai mukaddari ne, tun da ga shi yanzu ina majalisar dattawa karkashin SDP."

- Sanata Aliyu Wadada.

Mun ruwaito cewa Sanata Wadada ya nuna yiwuwar dawowa APC, inda ya ce:

“SDP a matsayinta na jam’iyya ba ta yi min laifi ba, kuma har yanzu ina alfahari da ita. Amma abubuwan da ke faruwa a cikinta yanzu na iya sanya wa in sauya matsaya. Zan iya cewa ni ɗan APC ne, kodayake ban koma a hukumance ba.”

Kara karanta wannan

'Za mu more': An faɗi dalilai da ke nuna Jonathan ne mafi dacewa da bukatun Arewa

Sanata Wadada ya kalubalanci 'yan adawa

Sanata Wadada ya kuma ce jam’iyyun adawa kamar ADC ba za su iya kwace mulki daga hannun Shugaba Tinubu a 2027 ba.

“Ku duba su ɗaya bayan ɗaya, wacce jam'iyyar ce ko dan takararta da zai iya yin wani abin a zo a gani fiye da abin da gwamnatin Bola Tinubu ke yi? Ban ga wanda zai iya ba,” in ji shi.

Ya kalubalanci masu neman takarar shugaban kasa daga jam’iyyun adawa da su fito da tsare-tsare na gaskiya maimakon “suƙa maras amfani.”

Ya kuma jefa masu tambayar ko za su dauki wani mataki na daban kan cire tallafin mai, gyara tsarin musayar kuɗi da haraji da samar da ababen more rayuwa da suka sabawa na Tinubu?

“Muna magana kan Najeriya gaba ɗaya, ba siyasar yanki ba. Shugaba Tinubu shugaban Najeriya ne, ba na Legas ko kudu maso yamma kawai ba,” inji Wadada.
Sanata Wadada ya ce babu 'yan adawa da za su iya karawa da Tinubu a 2027
Sanata Aliyu Ahmed Wadada ya bayyana yiwuwar komawa jam'iyyar APC. Hoto: Sen. Ahmed Aliyu Wadada
Source: Facebook

Tinubu ya mallake Aso Rock a 2027

Kara karanta wannan

Ana jita jitar rashin lafiyar Tinubu, Sanata ya fadi halin da Shugaban kasa ke ciki

Haka kuma, Sanata Wadada ya yaba wa Shugaba Tinubu kan yadda yake shimfida ayyukan ababen more rayuwa musamman aikin titin Sokoto–Badagry, hanyar Abuja–Kano.

Jaridar Leadership ta rahoto Wadada ya kuma yaba wa Nyesom Wike, kan irin ci gaban da ya kawo a babban birnin tarayya a matsayinsa na ministan birnin.

Kan ko wannan kalamai nasa na nufin yana goyon bayan tazarcen Tinubu a 2027, Sanata Wadada ya ce:

“Idan kana ganin ka cancanci a mara maka baya, to ka fito ka tsaya takarar. Duk wanda ya damu da Najeriya ya san mutane na jin tsoron sauyi, amma Asiwaju ya kawo sauye-sauye da ba a taɓa gani ba.
“Tuni aka mamaye fadar shugaban kasa a 2027, kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya riga ya mallake kujerar shugaban kasar."

Sanata ya magantu kan 'rashin lafiyar' Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sanata Orji Uzor Kalu ya yi karin haske kan rashin lafiyar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da ake ta yadawa a Najeriya.

Sanatan da ya fito daga jihar Abia ya karyata jita-jitar cewa Shugaba Tinubu yana cikin wani yanayi na rashin lafiya mai tsanani da har ta kwantar da shi.

Sanata Orji Uzor Kalu ya bayyana cewa ya yi magana da Tinubu ta waya kuma yana shirin tafiya Japan da Brazil domin wani taro mai muhimmanci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com