Wadada: Sanatan SDP Ya Koma APC bayan Ganawa da Shugaba Tinubu

Wadada: Sanatan SDP Ya Koma APC bayan Ganawa da Shugaba Tinubu

  • Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta samu karuwa bayan Sanata Aliyu Wadada na SDP ya dawo cikinta
  • Sanata Aliyu Wadada ya bayyana cewa yana alfahari da jam'iyyar SDP amma lokaci ya yi da zai bar ta
  • Ya bayyana cewa yana daukar kansa a matsayin dan APC duk da har yanzu bai kammala komawa cikinta a hukumance ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Yamma a majalisar dattawa, a karkashin SDP, Ahmed Aliyu Wadada, ya fice daga jam'iyyar.

Sanata Ahmed Aliyu Wadada ya bayyana cewa yana daga cikin mambobin jam’iyya mai mulki APC duk da cewa bai kammala sauya shekarsa a hukumance ba.

Sanata Ahmed Aliyu Wadada ya koma jam'iyyar APC
Sanata Ahmed Aliyu Wadada ya fice daga jam'iyyar SDP Hoto: Sen. Ahmed Aliyu Wadada
Source: Facebook

Sanata Ahmed Aliyu Wadada ya yi wannan bayanin ne yayin da yake magana da manema labarai a fadar shugaban kasa, bayan ganawar sirri da Shugaba Bola Tinubu, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Ana jita jitar rashin lafiyar Tinubu, Sanata ya fadi halin da Shugaban kasa ke ciki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Wadada ya koma APC daga SDP

Wadada wanda ya bayyana PDP a matsayin ɗaya daga cikin “sinadaran da aka haɗa don dafa jam’iyyar APC”, ya ce bai ga wani ɗan ADC wanda zai fi Tinubu nagarta idan aka zaɓe shi shugaban kasa a 2027 ba.

Ya mika godiyarsa ga Shugaba Tinubu bisa girmamawa da ya yi masa ta hanyar aika sakon taya murna a lokacin naɗa shi sarautar Maga Jindengi na Lafia a watan Agusta, rahoton jaridar independent ya tabbatar.

Yayin da yake tunawa da tafiyar siyasar sa, Wadada ya bayyana yadda ya riƙa sauya jam’iyya, inda kafin ya shiga SDP, ya kasance tare da APC tun kafin a kafa ta, kuma ya taba zama sakataren kuɗi na ƙasa a PDP.

Ya ce sauya shekarsa daga APC zuwa SDP a lokacin baya, ba saboda wata matsala da APC ta ba ce, sai dai saboda wasu dalilai, kuma yana alfahari da SDP har yanzu.

Kara karanta wannan

Lema ta yage: Tsohon mataimakin gwamna ya yi murabus daga PDP, ya ba da haƙuri

Meyasa sanatan SDP zai koma APC?

Sai dai ya nuna alamun cewa abubuwan da ke faruwa yanzu na iya sa ya bar SDP, yana nuni da yiwuwar komawarsa APC duk da cewa bai tsallaka a hukumance ba.

Sanata Wadada ya yi magana bayan ficewa SDP
Sanata Wadada ya sauya sheka daga SDP zuwa APC Hoto: @ahmedwadadaa
Source: Twitter
"Na kasance a APC kafin SDP, kuma a APC nake tun kafin a kafa APC, na taba zama jami’in PDP na ƙasa. Na kasance sakataren kuɗi na ƙasa na PDP. Kuma babu wanda zai musanta cewa PDP ta kasance ɗaya daga cikin sinadaran da aka haɗa aka kafa APC."
"Kuma saboda haka, har yanzu ina da dangantaka da APC tun kafin na shige ta. Ficewa ta daga APC zuwa SDP a wancan lokacin, ba wai saboda APC ta yi min wani laifi ba, sai dai yanayi ne ya tilasta hakan."
"Babu shakka, kamar yadda na faɗa a baya, SDP ba ta yi mani wani laifi ba. Ina alfahari da ita, amma abubuwan da ke faruwa yanzu na iya sa na daina zama a SDP. Zan iya cewa ina APC, ko da ban koma ba a hukumance, kuma ba saboda SDP ta yi min laifi ba."

Kara karanta wannan

Shugaban majalisar malaman Kano zai nemi gwamna, zai kara da Abba a 2027

- Sanata Ahmed Aliyu Wadada

Jam'iyyar APC na zawarcin gwamnan Enugu

A wani labarin kuma, jam'iyyar APC a jihar Enugu ta fara zawarcin Gwamna Peter Ndubuisi Mbah na PDP.

Jam'iyyar APC ta bayyana cewa a shirye take ta yi maraba da shi gwamnan idan ya amince ya yi watsi da jam'iyyarsa ta PDP.

APC ta nuna cewa za ga karbi gwamnan tare da dukkanin mukarrabansa a duk lokacin da ya shirya shigowa cikinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel